← Book details Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 87

Sashe 20

Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Karfe uku yau suka tashi ko alamar jiran feea batai ba don tana cike da jin haushinta,tama rasa wanda zatace tana so sai wannan gantalellen mahaukacin,mts aka taringa jera tsaki ta fito daga makarantar,kirane yashigo mata mama ta gani saurin dauka tayi tace"Assalamu alaikum mama lafiya ko."
Cikin farin ciki taji mamar tayi magana cewa"daman ince maki babanku ya dawo babu jimawa."
Itama cikin farinciki tace"dagaske mama?wayyo mungode Allah mungode ma Alha ganinan zandawo insha Allah."
Kashewa tayi sai lokacin taga sakon malik na biyu ayau din nan.
_fatan lectures sunyi dadi,inba damuwa kisaman gida yanzu pls._
Tarar taxi tayi ta gaya mai unguwar dazaikaita suka tai.
KOfar gidan ya sauketa tayi addua sannan tashiga......compound din gidan banu kowa inda suka saba zama bata ganshiba tayi shahadar nufar main falonsu kirjinta yana amsa wa,amman ta saka dakiya da natsuwa kadan aranta ta shiga.
Yana tsaye wajen taga yana shan win din sa ga wayarsa yana danna wa,malik kuma yana cikin daki baikai ga fitowa bah.tunda tayi sallama ta shiga ta hangoshi can tsaye kirjinta ya tsanan ta bugawa,zama tayi tana karanta duk adduar da tazo bakinta.
Juyowa yayi bai sauke idonsa ko ina ba sai inda take zaune kamar kazar da aka tsamo daga ruwan zafi haka tayi.
Shan mur tayi ta kauda kai kamar bata ganshi ba,nan kuwa kamar ta saki zawo taji,ganin dagaske wajenta yayo tsoro yasa takasa cigaba da zaman ta mik'e cike da dakiya tana ja baya fuskarta aya mutse idonta a kan cup d'in hannun sa.tai saurin toshe bakinta da hancinta har saida ta dangane da bango sannan ta tsaya,babu sassauci kokadan ga fuskarsa daf da ita yatsaya idonsa tar akan fuskarta,farare tas said shining suke kamar anzuba mangyada aciki.banda daddad'en k'amshinsa da yake nusar hancinta bata jin komi amman saboda ta k'ular dashi yasa ta ringa kauda kai tana yamutsa fuska.hannu tasa tana dakatar dashi da had'e duk kusancinsu cikin yar muryarta tace"dallah malam miye haka,matsa kaban waje nace kamatsa,kar namaka amai ga jiki nibada shan giya ba nida warinta."
Duk cikin kalamanta babu abunda yake b'ata masa rai irin tace yana warin giya.shak'o wuyanta yayi yana huci iyakar karfinsa bayan ya hade hannayenta baya yasake matseta ga bangon.
cup dinner giyar yake k'okarin kaiwa bakinta ta guntseshi ga shida ker take nishi idonta duk sun yo wake sun fara canza kala,cikin dakakkar murya yace.
"Naga alamar kwa'ayinta kike ko,to sha inbaki shata ba saina fiddo mak'ogwaronki shegiya yar iska maibiyo maza gidajensu,ke akaruwancin nakin ma marar aji kikeyi banza gantalalla.ai tsirara zakiyi yawo asan cewar kedin yar tasha ce."
Duk yadda ya shak'eta da yadda ya murd'e mata
Hannu duk bataji zafinsu kamar yadda kalamansa suka tsaya mata garai suke sukarta ga rai.jitai wasu kwallah zasu zubo mata tai saurin maidasu.....afusace yayi watsi da ita bakin k'ofa kadan yarage batabfad'a bisa hannunta ba fitowar malik kenan aguje ya iso wajenta yana sallallami
"Wai Alfah baka da hankaline?wajen ka tazo ne?banson rashin tausayi."
Hannu ya mikabmata ta kama amman ta k'iya ta dafa bango tana mik'ewa daker,cikin zuciya Alfah yace "muddin bata bar zuwa gidan nan ba wlh watarana ferfesun ta zanyi incinye,wawuya kawai ya watso mata sauran win din dake cikin cup din hannunsa,ga fuska......runtse ido tayi tana jin wani k'ullutun bak'in ciki yana d'awainiya da ita........kadan yarage bata fashe da kuka ba amman saboda gudun karyaga wallanta tasake maxewa.....ciki muryarta dake rawa tace"macucu azzalumi mak'etaci baka san komi ba sai zallar cuta da shaye shaye,taya zakaji feeeling din tausayi cikin ranka ai bana tantama inkace zakai kisa don kuwa y'an shaye shaye kamar ka abu abunda ba sayi,wannan la,anannanr giyar babu abunda bata sawa. wani saboda ita har uwarsa yake yiwa fyad'e."
Innalillahi zo kaga tashin hankali wajen Alfah gabaki d'aya fuskarnan ta koma jajir don bala,i
Idonsa kamar anrura garwashi.

Ganin haka da tayi tajawo jikkarta takalminta ga hannu ta ranta cikin nakare,shima kamar wani mahaukacin gaske yabita yana haki baida burin daya wuce ya kamata burinshi ya danne wuyar shegiya,ya tabbatar mata da cewar yes zai iya kashetan don ubanta.
Malik ma ya rufa mashi baya don hankalinsa ya tashi muddin Alfah ya kama Fiyah wlh komi zai iya aikata mata,baiwar Allah fiyah tana gudu tana faduwa tana tashi,duk ta guggurje k'afafu.data waiga taganshi sai tasake runtumawa har Allah yasa ta fice bata tsaya jiran taxi ba ta yanki titi saida taga tabacewa ganinsa..........

Mrs Bb ce
Mom muhseen.
[9/17, 3:37 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

🅿️.........17

Har k'ofar gida ta sauke ta yah jalal da wani abokinsa sai d'alha duk suna bakin shagon kofar gidanmu zaune,sukuku haka na nufo gida gaidasu nai na wuce cikin gidan........tun a soro na jiyo muryar Anty jamila nasan itace tazo,kowa ya sanar da ita da wannan tsohon cikin haihuwa yau ko gobe.
Sallama nai ina idasa shiga suna cikin inuwa zaune har lokacin dai fuskokinsu babu wata walwala sosai.
Sannu mama take mun itada yesmin dake duba littafinta,zamewa nai kusa da anty ina mata sannu da xuwa.
"Kamar wadda tadawo k'asa fiyah."
Murmushi tad'anyi tace"wlh yau ban samu nasaka komi cikina ba har nadawo yunwace keta cina nan dakika ganni."
Cikin mamaki mama tace"au dasafe dana ce kin karya me kikace mun safiyyah."
Yamutsa fuska tayi kamar zatayi kuka tace"mama wlh bakina ne babu d'and'ano."
Cikin fad'a mama tace"in haka ne kowa ma aida baici na,kimaida hankali wannan ulcer banzar tatashi wlh zaki gane kurenki,maza tashi ga abinci can kije ki zuba kina girma kina kara rashin wayau."
Daker ta mik'e ta wuce d'aki ta zube kan gadonsu tana sauke numfashi.saida ta huta sannan ta shige wanka tafi minty talatin tana wanka sannan ta fito.
Duk kayan fiyah dogayen rigunane siket basu wuce biyar ba.tayi shafa sannan taje tasa abincin ta dawo tsakar gidan suna ci gaba da hirar,mostly duk akan rufe baba ne da akai,saida nai rabin abincin nace"mama an samu wata nasara ne akan abun,yaushe zasu sakesa."
Tab'e baki tayi tana cewa"wace nasara kuma safiyyah,?nan yayanku ya sake komawa station din da duka suka rufesa cewa inyasake xuwa zasu hada dashi,wannan masifa dame tai kama nidai gaskiya nagaji wlh nagaji,shekara ashirin ana fama da abu guda nidai inhar yadawo to tashi nan unguwar yazama dole,ina dalili ina d'an mafari mutumen nan inba gani yayi munbar masa unguwar ba bazai shafa mana lafiya ba wlh haba."
Anty jamila tace"Aa mama wlh babu inda zaku aiba filin ubansa bane balle na uwarsa,dayake son ganin dole saikun tashi duk bakincikin sa wlh nan gidan yafi karfinsa.munafuki annamimi don dai uncle bai gari wlh da tuni baba yadawo,idan ta k'amarsa yana da kud'i ai bashi kadai Allah ya bawa ba,akwai wad'anda suka fisa."
Mama tace"Gara da baya nan jamila banson maganar tafita har takai ga wataran aimaki gori duk da bana fata,kuma dangin mijinki basu da wannan amman abun gudun shine yauda gobe."
Haka suka cigaba da hirar fiyah na jinsu ta kasa cigaba da tsoma baki............bayan sallar magruba driver anty yazo yadauketa suka tai gida.
Ina daki ina ta duba handout dina,naga sakon malik a wayata.
Na jima ina kallon text din kafin naduba abunda yace.
_FATAN MA,ABOCIYAR MURMUSHI DA FARA,A TA ISO GIDA LFY,ZANSO YAU TA KARE FARINCKI NA LULLUB'E DA XUCIYARKI KI KWANA LFY MUTUMENKI YANA GAIDAKI._
ta jima tana bin rubutun da kallo me yake nufi kuma oho abunda take fada kenan cikinn xuciyarta.......balaifi sakon ya yi mata dad'i amman bata mayar masa da ansa ba,karatunta take yesmin kuma tana can tare da mama dakinta.yah jalal ne ya shigo yana ma mama magana tayi bak'o yana son magana da ita,kasa kunne nayi sosai don nasan bai wuce daddy ba shine mukai dashi zaizo.
Saigashi kuma shid'inne ban fito ba inaji suna magana yana bata hkr,kuma ya je yasamu yayansa watau Alh muazzam na shawo kansa zuwa anjima ko gobe za asakesa.ashe yar hatsaniya ce tahad'asu,shi yaya yazo fita daga unguwar shikuma malam yazo shigowa shida mai taxi,sai mai taxi din ya banki motar yaya,to daman mai neman kukane aka jefa da kashin awaki nanfa yaringa yiwa malam rashin kirki har malam shima ya gaza hkr yashiga rama wa shine fa ya kira yan sanda suka tai dashi.....aman komi ya warware malam yana nan dawowa insha Allah,yanzu can zan nufa.
Godiya mama tayi tare saka masa albarka yace"haba ba komi ai malam namune sai inda karfinmmu yakare,Allah ya kiyaye gaba ga wannan asaima yara wani abu,ya jiye mata kudin da yaba fiyah bata ansa ba.
Har mota yaya jalal ya raka shi har yake tambayar dama yana nan,yace ai yazo hutune yana kaduna yana aiki....sundan tattauna sannan ya wuce gidansa ake cikin estate din.

Fitowa nai na samu su mama suna yabonsa don sunce tun zuwan su unguwar shine na farkon daya fara masu mutunci,bacin shi babu mai kallonsu da kima.
Anan mama take basu labarin abunda yafaru tsawon shekarunan dayasa Alh muazzam basa shiri shida malam kabir.
Chapter 20 · 0% Book details