← Book details Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 87

Sashe 40

Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Tunda na shiga daki kuka naitayi ni bazan ce ga abunda nake ma kuka ba,kawai dai nabarwa raina cewar yadda ya banzatar dani awajen bacin yaga irin halin da muke ciki,shine dayaga cewar masoyiyarsa zata zata rasa rayuwarta yadawo............saida naji kaina yafara ciwo sannan na hakura,m.card din da zakiyya tabani na ciro daga cikin aljuhun doguwar rigata na kura mashi ido,zanso jin abunda yake ciki amman ba yanzu ba sai tare da yaya malik,cikin jikkata naje nayi mashi kyakkywar ajiya sanan ta nufi bayi,don jikinta duk tsami yake mata.
Gyare jikinta tayi tsaf sai kamshi take fitowa tayi don cin Abinci yunwa takeji.
Sallamar muhseen ce tasaka ta juya shikadai ne daga bayansa kuma saiga uncle ya shigo shima,hira suke ta kwallo sai muhawara suke shi uncle dan arsenal ne shikuma muhseen dan Manchester united ne,sai gardama suke.
Anty ta fito tana cewa"aifa kun fara halinku ko,wai meyasa baku gama duk gardame gardamen ku acan waje sai dole kunshigo mun gida da hayaniya."
Fiyah dai na kan dining tana tsakurar tuwon shinkafa da miyar agushi taji zallar naman kaza.
Uncle bai kula Antyn ba sai muhseen ne yake bata ansa suna ta fadansu itada shi dasuka zaba,
"Safiyya babu magana"
Yake take tace"uncle naji aikuna ta magana ne sannuku."
Muhseen najin ankira sunan ta yai saurin juyawa yana washe baki,cike da jin dadin ganinta barin Antyn yayi yana nufar wajen da fiyah take.
"Aa ah ashe kina nan nazo da yamma bakinan"
Ta na Kai cup din ruwa bakin ta tace cikin sanyin murya"ina wuni yaya muhseen"
Murmushi yayi yana shafa kanshi yace"lafiya lau ya kike,nayi kewarki yau zuwana biyu bana samun ki"
Idan dayasan yadda takeji yanzu dayake isarta da magana da ya kyaleta,amman bata son yaga tayi mashi wulakanci dole ta ke dannar xuciyarta take bashi ansa.
Uncle yace ma Antyn"meyasamu safiyya ne?"
Dariya Anty tayi har muhseen yana juyowa yace"kinga kina hana mu sakewa wallahi"
Harararsa tayi tace"nan gida nane kabari sai kayi naka idan naje saika mun iko kajiko"
Ta share sa tana bawa uncle ansa"waifa daga tayo na biyar isalamiyya shine take fushi,da kuka ma ta shigo gidan nan don ta sana yo na biyu ko na ukku anbata na biyar take ta fishu"
Murmushi yayi yajiya ga fiyar daketa cin magani yace"safiyya haka abun hake ba kullum kake nasara ba,dole daman wata ran kaga juyin mulki badan hakan nanufin kasawa ko rashin maida hankali ba,aa hakan na nufin rabon wanine ba naki ba kiyi hkr next exams saiki dage ki dawo da position dinki"
Murmushin dole tayi tace"nagode uncle insha Allah zan gyara"
Muhseen yace"kice dai yar gidana akwai kokari ban result din in gani tawan"
Batare dataji komi tace"yana gida na barsa wajen mama"
Duk yadda yaso hirar tayi tsayi abun ya gagara don taki bashi hadin kai,tashi tayi ta yi masu saida safe ta wuce dakinta.
Bata da natsuwar yin karatu amman ya ta iya dole zatayi saboda baifi saura kwana biyar sufara exams ba,haka ta runtse ido tanayi ba laifi kuma yana shiga don fiyah inhar tasa kanta abu ba kamar in kan karatu ne tofa ba dagaske yitake har saitaji ta gamsu da abunda ta karan ta.

💞💞💞💞💞💞💞💞💞
Chapter 40 · 0% Book details