← Book details Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 87

Sashe 31

Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Malik yini yayi yana tunanin Anya ba fushi fiyah tayi ba,ganin tun safe yake nemanta baya samun ta.
Soyake yabata hkr da abunda Alfah yayI mata airport,kartun yanzu tace tagama aikin bacin akwai saura,duk da ganin cewa canjin da Alfah yazo dashi maigirma ne bai dace tace zata barsa a haka ba,zaiso muhimmin al,amari maigirma yawanxu cikin xukatansu,abunda yaketa ma fafutuka kenan don ahalin yanzu baiga wadda tadace da Alfah ba bayan safiyyah.Amman yaga babu hakan tattare da ita to balle shi da Idan yabotsare babu mai iya daidaitashi bayan itan.
Gajiya yayi da kwanciyar yatashi yayi wanka San an yawuce masallaci,don Alfah tun bakwai da rabi na safe yana company.
Yana kan hanyar dawowa daga masallacin ya hango kamar tsayuwarta,wani dadi ya kama shi ganin dagaske itance tana kokarin kiransa,murmushi yyisaddakiran yashi go mashi dauka yayi yana cewa"nayi tunanin kinyi fushi qanwata"
Sautin murmushinta yajiyo yana kallo fuskarta data Kara yin kyau sosai.
Jiyai wani iri cikin ransa,inama baiyyi alkawarin hadasu da amininsa ba,da babu abunda zai hana yayiwa kanshi kamu,da ace sannan kwanakin dasuka wuce da tsotsai yasa salon da yake mata ya Kama ta tuntuni,to tabbas a bun nasu zaijuye yarikide ya koma zazzafar kauna,Amman saita kibashi hadin kai Wanda shi kanshi hakan ya burgesa ba macen da za,akamace da wuriba........."yaya malik inata magana ko baka nan,gashi nazo maka da labari mai shegen dadi."
Ajiyar xuciya yasauke yana murmushi yace"oh qanwata a u serious."
Tana dariya tace"yes yaya malik,I'm serious,kayi nisa ne."
"Gani nan bayanki ai"
Juyawa tayi tana rike da wayar ga kunnenta.
Tana ganinsa ta ya mutsa fuska kamar karamar yarinya tace"kai yaya malik,shine zaka cinyemun dan katina."
Dariya yayi yana nufar kofar shiga gidan karamar yana cewa"abu mai sauki ba samarinki na nan ba ai saisu sakamaki wani."
Binsa tayi ciki tana cewa"uhm,kai kasan wasu samari yaya malik,Allah yasa wannan dan giyar baya nan kasan har yanzu tsoronsa nake karfin haline irin nawa."
Dariya yake Mata yace"naga alama ai,Amman ai kina kokari ko ni bana mashi tsage tsage kamar yadda kike mashi,kinga kuma ai muna samun cigaba"
Yau wani part din daban suka shiga shima yasha kayan more rayuwa,don yafi yi mata kyau sosai akan wancen data tab'a shiga.
"Zauna qanwata mezan kawo maki tukun?"
"Uhmmm,barshi yaya malik sauri nake ance Karna yo Dare kasan yau muka hadu da zakiyya."
Dalalo idonsa yayi yana kallonta cike da mamaki"dagaske kanwata?Allah yasa komi ya tafi lafiya lau"
Gyara zama yayi yana saurarenta.jikkarta ta zuge ta did do wayarta tana cewa"ai bakina ma bazai iya baka wanan labarin ba yaya malik gara in kunna maka kaji da kunnenka."
Ta fada tana danna wayar don gano recording din datayi dasuna magana da zakiyya,har taci Sa,ar ganoshi takunna mashi ta kure ma shi volume.........muryoyinsu suka fito tar cikin speaker wayar,kanajin komi dalla dallah har kukan zakiyya data keyi gashinan Kamar gabansa take yinsa.
Shiru yayi yakama habarsa ya rike cike da mamaki da al,jabin abunda yakeji bakin zakiyyar,har Zuma karshen tattaunawar da sukai ya gama ji yana kallon fiyah,shi tsabar iya Lauya maganarta da Ku ma kaifin tunaninta yake mamaki,yajin jina kokarin ta don kau ba kowane zai iya wannan dubarar ba balle yatsaro irin kalamanta,yasan tahada dawayau da dubara harta yarda da ita ta kuma bata amanarta.duba da yadda zakiyyar tayi saurin yarda da ita.
"Gaskiya qanwata kinyi bala,in burgeni naji dadin wannan lamarin ba Kadan ba nake gaya maki Allah yayi maki Albarka yakuma baki miji nagari wanda zai kula dake har illa masha Allah."
Sadda Kai tayi tana murmushi aranta tace Amen yaya malik,Amman afili kasa ansawa tayi.
"Yanzu kenan in share waje na zauna najiraki, komi kenan zanji daga gareki"
"Insha Allahu yaya malik,Aikomi yataho karewa kasan har na k'agu na kammala aikin nan."
Murmushi yayi yace"nima zanso komi ya kammala Amman kuma banson rabuwarmu dake,mun saba sosai sai nakejin kamar yar gidan muce ke."
Dariya tayi batace komi batana sadda kanta,hakika kamar yadda yace sun saba haka a bun yake itama cikin ranta sun saba sosai,duk randa suka rabu zasuyi kewar juna.......koba komi yaya malik ya iya zama da mutane,ga barkwamci da Fara,a.
"Yaya malik Zan wuce gida kasan har yanzu inacan wajen Anty sai anyi suna zan koma gida,Wanda daker kuma in nakoma in ringa fita inba school zanjeba."
"Ba damuwa ba,arasa yadda za,ai ba muje saina tarar maki taxi don nasan baza kiso inkai kiba."
Fitowarsu kenan aka bude get din gidan motarsa zata shigo,wani lugude kirjinta yake mata. Bata shirya haduwa dashiba ahalin yanzu don Sauri take shidda tayi takoma gida hakan,gashi Anty ta tsirar mata hada wani abun banza saboda wani muhseen.
Tsaye sukai itada malik,ita tana tararrabin yadda zasu rabu shikuma yana murnan zai samu damar hada su.
Cikin rawar murya tace"yaya malik karka barshi ya tabani wlh sauri nake idan ban koma gida da wuri ba Anty fada zatayi mun."
"Ki kwantar da hankalinki bazai maki komi ba,shizan saka ya mayar dake gida yanzu."
Xaro kyawawan idanunta tayi tana kallon sa cike da tsoro tace"bana so wlh so kake mutai ahanya yaje yayi cinikina wani waje aa barni infita salin alin."
Fitowa yayi daga cikin motar cikin kayansa kana na masu masifar kyau,fesincap ce Sam an kansa kalar rigarsa light blue da rubutun *ME&YOU* ajikin rigar fuskarsa da walwala ba kamar yadda tayi tunanin ganinsa ba,direct wajensu ya mufo idosa akan ta hannunsa guda rike da briefcase dinsa,ya ratayota ta kafadarsa said gudan Hannun kuma yana rike da wayarsa.shan mur fiyah tayi tana kauda Kai harga Allah yayata Kyau babu karya.
"Malik tsayuwar me kuke,halan jirana kuke inzo inbata giyar tasha"
Murmushi malik yayi yace"Aa ita ai batasha ko sOfiyyah."
Chapter 31 · 0% Book details