← Book details Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 87

Sashe 48

Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Dabaki daya kan fiyah ya kulle jin abunda mama take fada,yesmin kau tayi sukuti taji me Addar tata zata fada dagaske ta fara soyayyar.
Idonta duk awaje tana kallon mamar tama kasa furta kalma guda,duk wata basirarta ta karya ta kare ta nemeta tarasa.
"Kiketa kallona safiyyah kina mamakine dana gane?"
Girgiza kai tayi cikin dawowa hayyacinta tace"mama mekike fada,soyayya?ni nake son wani mama to waye?ni bansan saba gaskiya"
Murmushi mamar tayi tace"karki daukan sakarai mana,nifa na haifeki babu wani abu da zaki boyemun cikin ranki,don haka saiki san abunyi koma waye inhar ba neman iznin mahaifinki yazo yayi ba,na abashi damar neman ki to wlh yana aikin banza,kuma duk randa babanku yaji labarin anganki da wani ko jalal yasamu wannan labarin wallahi safiyya karki rokeni inxo cetonki,tunda har kinyi wayon boye saurayi kuna haduwa awaje ko,saboda ke bakida hankali duk tarbiyyar da akai maki tatashi abanza kenan."
Kuka ta fashe dashi mai rikitarwa,ita wallahi ba son wani take ba towaye ma zata so amman mama ta kama mata masifa tana cewa bata da hankali.
"Kukan me zakiyi,don ina maki nasiha ina nusar dake abunda yadace da wanda baidace ba."
Cikin kukan tace"wallahi Allah shine shedata shaidata ni bana soyayya da kowa,idanma zargina kike mama wlh nidai kin shiga hakk.........dungure mata kai tayi cikin fada tace"don gidanku nizan zargekin,nizan shiga hakkin naki to kinyi daidai kije kiyi duk abunda kikaga yadace da rayuwarki"
Tatashi zata shige daki don ranta yabaci da fiyah sosai.
Rarumo kafafun mamar tai tana kuka"kiyi hkr mama wlhh kinji na ramtse maki babu wanda nakeso,kuma babu wanda nake tsayawa dashi atiti,kiyarda dani idan da akwai aibazan yarda kisan halin danake ciki ba,nidai kiyi hkr idama don makaranta ce kike ganin ina fakewa da ita ina haduwa sa wasu to bazan sake fitaba,shikenan sai hankalinki ya kwanta mama"
Janye kafarta tayi ta shige daki tabarsu da yesmin,kukan ta cigaba dayi tana data sanin yanayin data shiga har haka ya jawo fitina itada mahaifiyarta,abunda suka jima basuyi ba irin wannan fadan ita mamar.
Yesmin keta bata hkr tana cewa"kiyi hkr Adda mama ba tayi bane don bata sonki ba,ita don tarbiyyarki takeyi wani idan ya ganki xai maki wani kallo na daban,kiyi hkr karki kullaceta."
Kallon yesmin din take tashare kwallarta tace"kintaba ganin da nagari ya rike uwarsa mahaifiya garai,duk girman laifinta kuwa,don haka kibar cemun haka."
Tatashi tashige daki tana shirin kwanciya,amman kalaman mama na mata yawo akai,hakika mama iyakar gaskiyarta ta fada,kuma tana tsoron lalacewar tarbiyarta shiyasa.
Wayarta tadauko tana ma malik text,sai taga gara takirashi tayi mashi bayani.
Ta gama komi ta kwanta yesmin dakin mama zata kwana,shiyasa ta sake ta kirasa.
Lokacin sun rabu da Dady shikuma yana zaune gefen Alfaj daketa bacci,kallon wayar yayi ya yi picking.
"Yaya malik ina wuni"
Shima muryarsa tadan disashe yace"lafiyalau qanwata ykk yagidan"
"Yaya malik baka da lafiyane?"
Ajiyar xuciya yasauke yana kallon Alfah yace"dasauki dai qanwta,Alfah ne ba lafiya yayi doguwar suma daker akasamo ransa,Qanwata ashe Abdoul yana da wani ciwo bamu sani ba,nan yayi mata bayani atakaice,kuka yaji tanayi kasa kasa.shiru yayi yana tunanin daman sai haka ta faru barinta yayi take kukan ta samu natsuwa.
"Yaya malik don Allah idan Allah yasa ya farka kace ina mashi sannu,zanso nazo na ganshi amman yaya malik Im sorry to say bazan sake zuwa inda kuke ba,domin kare abunda zaizo yaje mamana ta fara harbo jirgina,har tayi dogon fushi dani.kasan kuma fushin iyaye akan y'ay'ansu masiface babba,don Allah yaya malik kuyi hkr da rashina nayi iyakar abunda Allah ya bani iko,sauran kuma na barshi gareka da Zakiyya,ku karasa ni banyi don wani cikinku yabiyani ba nayine domin Allah da kuma tausayin sa daya shigeni ganina dashi na farko.don haka kuyi hkr zaku daina ganina,amman kila mun ringa gaisawa don gujewa fushin mamana"
Hakika baiji dadin wannan labarin ba,don ya sake dagula mashi lissafi baiso ba yaso ace komi anyishi da ita,amman kuma iyaye suna gaba dakomi,shima mai goyon bayanta ne akan hakan.
Numfashi yaja yace"bakomi safiyya ai aiki kam yazo karshe insha Allah,kin riga kinyi komi da kikai alkawari insha Allah ladarki naga Allah,haka nima daga gareni zan baki tukuici badan biyanki zanba,saidan yabawa da kokarinki don kinyi abunda dayawa mazan ma bazasuyi ba,ki sadaukar da lafiyarki,lokacinki kudinki da jin dadinki duk aka Abdoul ya dawo cikin hayyacinsa,to Alhamdulillah mungode Allah ansamu nasara don haka karki saka wata damuwa,Abdoul yagama dawowa *ABDOULNASEER ALFAH* Dinsa kuma insha Allah da kafarsa zaizo maki godiya,don haka ayima mama biyayya sannan abata hkr har sai ta sauko,kinjiko kanwata."
Hawaye take sharewa sai takejin sunayin bankwana ne,kamar bazasu sake haduwa ba har abada.ga wani nauyi da kirjinta ya mata Abdoul take hangowa ranar da suka hadu Asibiti an sallami zakiyya,shigarshi cikin taci dinta da abunda ya faru wajen sai kurin taji kuka ya kubce mata.
Shiru yayi yana saurarenta tabbas safiyyah ta kamu da soyayyar Alfah,Amman ita kanta bata sani ba don wannan kukan yasan duk akan shi takeyi,saiyaji tausayinta ya kamashi.
"Kuka kikeyi safiyyah,miye abun kuka."
"Yaya malik ka kula dashi don Allah,karka bari wani abu ya samai kagani baya da kowa saikai,kaine yake gani yana jin dadi,kamun alkawarin kulawa da shi yadda ya kamata."
Baisan murmushi ya kubce mashi ba yashafa kanshi yace"indan wannan ne qanwata namaki alkawari,kidauka ma anyi angama kuma ai zamu ringa gaisawa time to time ko"
Muryarta kasa kasa tace"insha Allah"
"Oky to share kwallar,ki maida komi ba komi ba ai daya tashi zuwa safe ma zan kiraki saikiyi mashi yjikin da kanki ko"
Shiru tai tana ajiyar xuciya.share maganar tai tace"yaya malik zan rako ni,ima nan asibitin yau mun hadu taje kawowa baba abinci inji mami munyi magana da ita har nai mata alkawari. Kawota wajen yayanta don haka idan zanje exam zan taho da ita na ajiyeta natai,kai saika sata taxi ta koma gida.wane asibitine kuke"
Jinjina kokarinya yake lallai masu xuciyar fiyah sai antona.
Gaya mata sunan asibitin yayi sukai sallama tana cewa yaje ya kaima daddy m.card dinnan komi kenan shiyasan yazaiyyi.
Haka suka rabu kamar tabiyosa taganshi.

Malik ya ajiye wayar yana nazarin hirarsu,duk abunda suka tattauna akan kunnensa,tas yaji wani babine mai girma ya budewa yarinyar cikin birnin xuciyarsa,hakika ita din wata fitilace mai mugun haske ga rayuwarsa,shin dame ya dace yayiwa wannan yarinyar sakayya.ta kawo cigaba arayuwarsa tayi tsaye tsayin daka akan rayuwarsa ta baya,ta sadaukar da ranta da kominta akansa,duk don ya dawo da rayuwarsa kamar baya,tana son dawo mashi da kimarsa daya rasa.
Bai nuna ma malik ya tashi ba,cigaba yayi da kwanciyarsa yana nazarin kalamanta da yanayinta.
Har wani sabon baccin yasace shi.
Chapter 48 · 0% Book details