← Book details Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 87

Sashe 81

Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Wai kitchen naga time yana wucewa koba ku break da wuri anan"
Baisan meyasa gangar jikinsa takeson rusa mashi plans ba,runtse idonsa yayi sannan yace"xonan"
Ahankali take dawowa ta rabe gefensa ya ajiye computer ya matso kusada ita,kamar zai rike hannunwan saiya fasa yace"keda kike amarya waye yasaki shiga kitchen?"
Soke kai kasa tai batace komi ba.
"Ko kin manta amaryace ke?"
Girgirza kai tayi yace"halan kurma kika koma"
Shagwabe fuska tai bata san ma tayi ba tace"to ni ai nasaba agidanmu ko"
"Ai yanzu tattalinki ake idanma mami ta ganki kitchen nabani ai"
Kallonsa take cike da tambaya "to miye"
Zaro ido yayi yace"ai ita yanzu ma duk tunaninta kinan kwance babu lafiya me zai iya fiddoki"
Har lokacin kwalwarta bata bata komi ba,kallonsa take yadda yake murmushi tace"nifa ban gane ba,mezai sameni to bacin na warke"
Matsowa yayi yarage murya kamar wani yana jinsa yace"kin manta kenan,ina nufin ai kowa gani zai na angonce yau kinga ai zasuga kinan kwance ina..........bata san sadda ta tashi ta shige toilet ba ta rufe kofar.
Me zai inba dariya ba rabonsa da dariya irin wanan bazaie ga lokacin ba.
Knocking din kofar falon yaji anayi ya tashi ya fita yaje ya bude,ni,ima ce da kaya ga hannu tace"yaya ina kwana"
"Lafiya lau wadannan kayan fa"
"Anty safiyya mami tace akoma wa"
Bata hanya yayi tashigo ta ajiye su bisan kujera tace"mami tace karfe tara kufito ayi break su Abbima har sun iso"
Jinjina kai yayi yana daukar kayan yana wuce wa dasu ciki.
Har lokacin tana toilet din ya ajiye ya isa bakin kofar yace"ki budemun na shigo wanka zayi idan ke bakiyi"
"Don Allah yaya Abdoul katai falo idan na gama saika shigo nidai wlh kana sani jin kunya don Allah karka kara"tafada cikin muryar kuka har da kwallarta.
Dariya yayi yace"oky kiyo wankan bazan sake ba natai falon ina jiranki"
Ya haye gado yana dariya kasa kasa wankan ta tube ta shiga yi da ruwa mai dumi,tayi anfani da kayan wankanshi ta jima kafin ta fito daure da towel dinsa tunda yace mata yana falon,ko kadan batai tunanin yana nan ba,kanta tsaye ta fito bata kali gadon ba ta nufi kayanta tana dubawa ta dauki karamin towel taa tsane gashinta...........sakarai ya koma ya saki baki da hanci yana karewa halittarta kallo,bata ankara ba saida taji kamar motsin mutun sakin karamin towel din tai kasa tafasa kara don har ga Allah ta tsorata bata dauka da kowa ba aguje ya sauko ya riketa tamau yana rufe mata baki
"Keee karkitara mana mutane"
Shiru tai ajikinsa yarungumeta suna sauke ajiyar xuciya tare,shafa kanta yake ahankali yana bubbuga bayanta ahankali har yakaita bakin mirrow.ya zaunar da ita,
Kwalla sharrrr suka xubo mata saboda tsabar kunyar da taji tama rasa mezatai.
"Shiiiiitt kukan me kike"
Fashewa dakukan tai "nace maka katai falo meyasa ka zauna ehy,nidai don Allah karabu dani inshirya da kaina katai kaban waje"
Juyawa yayi kurin with out say anything,sai taji bata kyauta ba koba komi dai mijinta ne yanzu.
Amman kuma idan ba haka taiba bazata shirya cikin kwanciyar hankali ba,shiryawa take cikin natsuwa tasan fushi yayi bazai dawo ba.
Doguwar rigace irinta indiyawa tayi masifar hawan jikinta komi fito masha Allah,sai dan mayafin rigar pich color be da dark pink rigar sai style din ya sake fiddo kyan rigar da wadda ta saka ta.
Simple make up tayi don kayanda ni ima ta kawo harda kayan shafa tasan dakin namijine ba lallai asamu irin kayan shafe shafen mata ba.
Tasa turarensa kadan don karya ringa tashi dayawa,
Tafita falo jiransa shima baijima ba ya fito cikin suit yaa rike da rigar saman baikai ga sawa ba,sai farar dake cikin kawai sai agogo da bakaken takalma yayi kyau amma ta kasa fada wuceta yayi tabishi baya suka isa cikin main falon gidan kowa ya hallara su daman akejira daga nesa take hango zakiyya tana mata dariya,duk saitaji kunyarsu ta kamata kowa zai mata kallon sunyi wani abu bacin ba suyi komiba
[10/18, 5:00 PM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSEER*
*(ALFAH)*

WRITTEN BY

MRS BB
MOM MUHSEEN

FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970

🅿️............65

Bayan angama break dady yajawo hankalin kowa anan yafara nasiha da nuna karfin kaddara da kuma rabo,duk inda kake inhar abu rabonkane saiya tadda ka yabada misali da auren fiyah da Abdoul yake cewa.
"Har Saura sati daurin aure bamusan da cewar babanki zai bamuke ba,mun riga mun hkr shima kuma ya hkr kwatsam saiga kira daga maigadin gidan yaya(watau baban Abdoul kenan)yace malan kabir yana neman mu agaggauce,cikin hanzari muka samu visa bamu sanar dasu ba nan mundai ce kirane daga wajen aikinmu.
Alokacin yake gaya mana yana son mubada sadaki da komi sati mai xuwa za,a daura auren tare da kanwrki,amman yace muyi shiru soyake ya maku bazata abun yayi bala,in yi mana dadi Abbinku kamar zai mashi sujjada din jindadi,haka muka bayar da kudi da komi sanan nayowa maminku waya cewar zan turo salamatu ta tayata hada lefe kala biyu,don mun yanke hukuncin harda na malik za,ahada rana guda ayi.
Kuma ranar na zagayowa aka daura danaku dana malik da zakiyya,malik din kadai na sanarma wa saboda hidimar zuwanki don haka kudauki wannan matsayin darasi,inhar rabonka ne abu to kocin rami saiya bika saidai idan rabon yana nesa zaijima baizo ba.
Don haka ina mai jawo hankulanku daku zauna da juna lafiya,kuyi hakuri da juna duka rayuwar bakomi ke isarbawa ba sai hkr,zamane bana yau ba bana gobe ba anafatan mutuwace zata raba,don haka ku matan kuzama masu biyayya ga mazanku sannan kukuma kuxama masu adalci da kyautatawa garesu,don haka ina maku fatan alkairi garayuwar aurenku Allah yasa maku albarka yabaku xuria dayyiba,ga tawa kyautar ga amare."
Ya ciro check guda biyu yace"gashina kowace tana da miliyan biyar biyar"
Zaro idanu mukai nida zakiyya muna kallon juna ya mika ma Abdoul guda ya bawa malik guda
"kubasu kyautace daga gareni"
Harda kwallata nake mashi godiya cike dajin dadi naimashi addua sosai,zakiyya ma tayi godiya sosai.
Abbi yace "duk abunda zan fada dadynku ya fadeshi,saidai nace maku Allah yayi maku albarka kudukanku Allah ya kawar da shedanin mutun dana aljan tsakaninku,kuyawaira yiwa juna uxiri rayuwa babu uxiri zaizama babu zaman lafiya Allah yayi maku albarka,nima ga tawa gudunmawar."
Ya fiddo keys na motoci ya mikama zakiyya ya mikomun.
"Motocine sabbin shigowa yanzu haka ana kan hadasu,zuwa sadda zaku gama yawon amarci suna zaune agida suna jiranku"
Sunkuyar dakai nai inajin kunya kamar ta hallakani.
"Mun yi maku visa daga nan zaku zaga kasa uku sanan ku tsaya saudiyya kuyi aikin hajji sannan ku jiyo gida."
Saboda jin dadi kuka nasaka ina jingina kaina kan kafadar mami ta rungumeni tana lallashi,godiya nake masu maitarin yawa da addua mai kyau.
Mami tace"nima ai ba abarni baya ba ga tawa kyautar ni ima miko mun box din dana baki ajiya"
Ta dauko ta kawo mata ta bude shi sarkokine na xinari sai daukar ido suke masu masifar kyau,ta ciro guda ta zagaya ta bayana ta saka mun ta cire yankunnen dake kunnena ta samun na sarkar sannan ta samun zobenta.
Haka zakiyya ma tasaka mata rungume mamin mukai nida zakiyya muna gode mata itama,sannan Abbi yace"kuzama cikin shiri karfe shidda na yamma zamu bi jirgin Nigeria zamu koma gida,don sati mai zuwa daurin auren su zuwairat."
Sai naji baji dadin tafiyar tasu ba,kenan mu muna nan ni wlh duk atsorace nake da wannan miskilin mutumen.
Chapter 81 · 0% Book details