← Book details Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 87

Sashe 10

Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fiyah ta gama komi yau da safe kasancewar yau Wednesday baba baya fita da wuri sai takwas na safe koda ya fito yaganta har takwas bata yi shirin fita ba yace"sofiyya yau babu makarantar ne."
Tana sauke tukunyar danwaken da zasu ci da safen tace"baba ina kwana"
Ya ansa cikin kula tace"aa baba akwai amman sai ten saboda malamin bazai zo ba da zai ma na seven to nine thirty baida lafy"
Ta gilla mai karya nashi ta zubo mashi da kununsa na gyada data dama,yana kalacin suna hira har sadda mama ta fito daga d'akin sa ta gama gyara mai,itama ta zauna aka hau hirar tare yesmin ce cikin uniform na makaranta ta fito tana ma su saita dawo,naira dari yabata ta yi break sannan ya bata dari uku tayi abun hawa.
Godiya tayi sosai ta fita tana d'aga ma addarta hannu.
Shima tashi yayi bayan ya gama yaba fiyah kudin ta itama ya yimasu saiya dawo suka bishi da addua,mama tace"tunda bazaki makarantar ba ki tashi ki kwab'a alkubus yayanku yana tafe yace mun kiyi mashi."
Gabanta ya fad'i don sunyi da malik zasu had'u karfe goma,intace saitayi wani alkubus bata san ranar fita ba,cikin murna tace"mama dagaske yah zaizo aikuwa zanso in shirya mashi abinci wlh,amman karfe goma inada lecture wlh kuma kanta zai mana test gobe,bacin haka aida bama zan je ba."
Maman tace"to abunda zai ai kafin lokacin yayi tashi ki d'ebo fulawar ki kwab'a mun,saina idasa nima da fita zanyi inje gidan yaya balara ba,ingano hasana bata da lfy."
Tashi tayi ta je ta dauko kayan had'in tazo ta fara kwab'in tana cewa"meyasa meta mama"
Tace"kinsan tana da iska to daga makaranta aka maidota sun matsa mata wlh,basu bari ma tayi karatun karshe dai kilan day zata dawo."
Nan suka ci gaba da hirar suna jajanta abun,hasana diyar yayar mamace dake can wata unguwa bama nan cikin abujar suke sosai ba.
Karfe tara da rabi tayi wanka ta shiga shiryawa doguwsr riga tasa mai dan karen kyau,don Antynsu ta tsaya tsayin daka wajen ganin ta tare masu sitira,duk da shima baban ba baya ba duk salla kala biyu yake masu,jamila ta kara masu kala gida da gyaluluwa da takalma,har mada kayan kwalliya da turaruka shikuwa jalal shike dauke duk rabin hidimar gidan,yana da kokari sosai don inzai zo daga kaduna d'unkuna yake zoma baban dasu da kuma takalmomi kayan abinci da dadai sauransu.
Tana cikin saka turare text d'insa ya shigo wayarta,saurin ajiye turaren tayi taduba.
_ina silver bird place guiding yanzu haka ina jiranki._

Shiru tayi tana tunanin yadda zatai ta isa wannan wajen,anya Malik yasan kuwa inda yake cewa ta samai,wannan wurin ai ba na irinta bane,kuma kudin taxi kansu sun isheta don dari bayar bata kaita ta maidota..........abayarta milk ta saka tana jimamin abun,wsta yar jakace mai kyau ta dauka ta fito mama na tsakar gida tana yankan alayyahu na taushen da za,ai tace"har kin fito."
Tace"mama don Allah in anshi dari uku wajen dalha,hand out zan siya na manta ban gaya ma baba ba."
Kalonta take kafin tace"shikenan kije ki ansa allah ya kiyaye kiyi addua idan zaki fita."
Sallama tayi mata ta fita ta anshi kud'in ta wuce.
Taxi ta tata bakin titi ta gaya mai inda zai kaita saoda sukai ciniki sannan suka tafi.
Sadda suka je get din arufe ta rasa yadda zatai don wajen yana da k'a idoji wayarta ta fiddo ta mashi text cewar ta iso yazo yayi mata iso.
Tana nan tsaye na wasu minty na sannan taji an bude wajen,malik ne yasha kananan kaya sunyi masifar ansar jikinsa,don shima malik badai kyau ba,murmushi yayi mata yayi mata nuni da cewar ta taho.
Itama ansar murmushin ta bashi ta isa inda yake suka jera har cikin palace din,waje ya had'u yahad'u iyakar had'uwa,fad'an yadda yake b'ata bakine don wajen sai wane da wane suke zuwa don wajene na shak'atawa ne.
Wajene na musamman ya sauketa rumface wayayya anjera kayan cinye cinye da lashe lashe.
Zama tayi shima ya zauna yana kawata fuskarsa da murmushin shima,lemu ya samata tare da tura mata plet d'in snacks gabanta.
"Bismillah tukunna,kafin infara zuba maki surutu in kwareki."
Dariya tayi tace"haba dai yah malik."
"Ehy mana,inason in sanar dake waye ABDOUL-NASSER ALFAH,don kisan ta ina zamu shawo kan abun."
Jinjina kai tayi ta d'an kurb'i lemun ta d'anci springros ta goge bakinta da tishu.
"Yah malik ina jinka,naci ai wlh bana jin yunwa nayo kalaci sosai."
Baice komi ba ya gyara zaman shi yafara magana kamar haka cikin sanyi da tausasa harshe.
"Abdoul Nasser muazzam kabir canji d'ane ga Alh muazzam canji shugaban y'an canjin Abuja gaba d'aya,yyi suna yayi fice a k'asa baki d'aya,domin bai anan kadai arxikin sa ya tsaya ba,ya rik'e minister a oxport sannan yana da kamfanin motoci M.K motors dake cikin garinnan,wande kika sani sannan yana kasuwancin shinkafa babu inda motocin sa basa zuwa,legos,ibadan,adamawa,maiduguri state daban daban.atakaice Alh muazzam mashahurin mai arzikine na bugawa ga jarida,babu inda sunansa baiyyi yawo ba sannan manyan yan siyasa Suna hudda dashi saboda jama,arsa mutunne shi da Allah bai hore mashi yawan kyauta ba,ba marowaci bane amman kafin ya bayar ana jimawa,baidamu da talaka ba hasalima baisonsu baison su rab'eshi ko kadan,inkinga wani na cin arxikinsa to kuwa abokinsa ne mai kudi irinsa,ko wanda bai kaisa ba.wannane babban kalubalensa.
Agefe guda Alh muazzam matansa biyu hajiya mariya itace uwar gida,Allah ya basu zuria itada Alh duk mata guda hud'u,akwai Amina da Haulat zuwairat sai khadija.sai agolarta data zo da ita gidan zakiyya duka yarinyar bata wuce shekara ashirin da daya ba ayanxu sa,ar ni'imah ce kanwar Alfah.
Amina da haulat yayyene ga Abdoul-naseer yayinda zuwairat da khadija suke k'anensa,hajiya Ushe itace mata tabiyu ga Alh muazzam kuma uwa ga Abdoul,Allah ya azurtata da samun d'a namiji daya tamkar da dubu ko ma ince miliyan,don shine d'a na farko wajenta dayar macece maisuna ni,imah don su biyu kadai Allah yaba mami.
Hakikanin gaskiya zaman lfy yayi karamci gidan Alh muazzam,domin hajiya mariya wadda ake kira da umma wstau uwar gidan tana bala,in jin zafin mami badan komi ba saidan ita kadai ce wadda ta haifa ma Abbi magaji,kuma magajin jarumi mai dakakkar zuciya,mai tsayuwa kan lamarin gidan baki daya,don komi dakika sani game da dukiyar Abbi Abdoul shine ja gaba wajen tafiyar da komi,har su matan nashi komi suke so to shi zasu tambaya,haka kannensa da suma yayyen nashi.
Wannan ne ya jawo matsanan ciyar tsana da kiyyyar su wajen umma da yaranta.
Bata kaunar Abdoul ko miskala zarratin,yayinda shikuwa kamar ya kwanta mata wajen biyayya,domin wannan umurnine daga mami ta bashi shida ni'imah,cewar kome umma zatayi masu karsu kuskura suyi mata koda kallon banza.
Bayan yaran yaran umma daga baya ta d'auko d'an kanwarta rik'o gidan mai suna Mamman.saika rantse anan aka haifeshi,Abbi bai ce don me ba don shi bai cika damuwa da irin wadannan abubuwan ba,sannan rigimar cikin gidanshi yasan da ita amman bai tab'a magana ba.
Shiyasa umma take tsula tsiyarta yadda takeso sannan abu na mai ciwo ga halayen Abbi shine duk abunda akazo akace mashi wane yayi,bazai tab'a bincike ba zai yarda kuma yayanke hukunci,ko waye kau amman banda Abdoul,don babu wanda yayiwa yar da irin wadda yayi wa Abdoul.umma tasha kai mashi karar Abdoul cewar yayi mata kaza yayi mata kaza amman kullum maganarsa guda itace "Naseer baxai yi abunda zai b'ata rai na ba mariya,kidai ji tsoron Allah."
Shiyasa ta dauki tsawon lokaci batayi nasara akan Alfah ba,don kuwa Abdoul ya zama tauraro mai haske xuciyar iyayensa,mutunne mai fara,a koda yaushe zakiga fuskarsa cikin walwala,ko b'ata mashi kayi zaiyyi murmushi kawai ya wuce bazai tab'a ce maka don me ba yanada jama,a sosai don yana hud'd'a da talakawa sosai,yana kuma sakarmasu aljihunsa ko fita sukai da Abbi marok'a suka rufesu tofa shizai ringa masu b'arin kudi.Alfah Allah yayi shi mai dogon hannu,jin dadinsa da Abbi keyi yasa ya gina mashi Wani kantamemen store dake cikin garinnan nasan zaki sanshi ALFAH STORE SHOPPING MALL ya cikashi da kaya ta ko ina kuma du abunda kikeso na b'angaren more rayuwa inkika shiga Alfah store kin samu.
Bacinan ya sakarmashi ragamar kamfanin MK motors duk wasu kudi dake shiga da fita to sai sun biyo ta wajen Alfah sannan suje ga Abbi.
Fiyah ta katseshi tace"waye daddy wanna da muka ganshi station."
Ajiyar zuciya yayi yace"Daddy babban aminin Abbi ne,kuma d'an uwansa guda tal dasuka fito ciki guda,shima yana cikin estate dinan cikin mai tama."
Shiru tayi ta sake cewa meyasa aka samai Alfah."
Murmushi yayi yace"wannan sunan daga mami yake,don tace tunda tataso wajen yayarta bayan rasuwar iyayensu take son yaron yayarta mai suna Alfah,sunyi soyayya kamar su cinye juna karshe uwar mijin yauar tata ta zab'a mashi mata.mafarin kenan mami data haifi Abdoul tace inkiyarsa kenan Alfah shikenan Abdoul-naseer ya b'ace saidai Abbi kawai ke kiransa da ABDOUL-NASS,wlh fiyah Abdoul ya fuskanci bak'in ciki ta dalilin umma,don kau umma tun Abdoul yana cikin ciki take son ganin bayansa Allah bai bata dama ba,domin kuwa Allah yace sai yafito saiya rayu rayuwa mai kyau.Abdoul yana son y'an uwansa yayinda sukuma babu abunda suke son gani irin mutuwarsa,don mahaifiyarsu ta riga ta dasa masu tsamarsa tun suna y'an kususan su,haulat da Amina sunyi aure suna gidan mijinsu sai zuwairat da khadija da kuma zakiyya.
Ana cikin wannan hali fiyah Abdoul ya fad'a soyayya da zakiyya diyar umma agolarta data zo da ita gidan.
Wanda zakiyyar itace ta fara nuna mashi tana sonsa,don tunda tazo gidan Allah ya dasa mata kaunarsa,amman komi suke yi babu sanin uma,ab'oye sukeyin kaunarsu ni kadai na san da wannan soyayyar."
Sake katseshi tayi da cewar "yah malik ina kai banji taku alak'ar ba,nai tunanin kaima d'an gidanne."
Ruwa ya d'ansha sannan yace.......

Mrs bb ce
Mom muhseen.
*Comment and share it*
[9/17, 3:36 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

🅿️.........11
Chapter 10 · 0% Book details