← Book details Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 87

Sashe 79

Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Baice komi ba illa kyawawan idanunsa dasuke ta kallonta kamar yauce rana tafarko daya fara ganinta.
Malik da zakiyya suka iso wajensu zakiyya tariko hannu fiyah shima malik ya riko na Abdoul suna kallon juna,photographer ya yi masu kyakkyawan hoto sannan kiyya ta jawo fiya malik ya jawo hannun Abdoul suka hade hannayensu waje guda,suduka bin hannuwan nasu sukai da kallo kafin su dago mai hoton ya daukesu,nan fa yacigaba da kashe masu kala,wani dayayi kyau sun kurawa juna ido su kansu basu san ma hakan tana faruwa ba,don baki daya abun yazo masu acikin bazata.
Kafin akaimasu baki daya na family,dady da Abbi ne kurin babu sai gobe zasu iso.
Kafin sujuya baki dayansu,wajen zamansu suka nufa suka zauna amman gabaki daya fiyah gani take kamar mafarki take,saita kallai ta sadda kai shima saiya kalleta ya dauke kai.fuskarsa bazaka ce yana murmushi ba haka bazakace yasha mur ba,kadaran kada han yake itace dai kallo daya zakai mata kasan cewa tana cikin farin ciki,kidan ya cigaba da tashi masu rawa nayi masu shan drinks nayi,fiyah kallon zakiyya take yadda duk inda malik yayi tana biye dashi,kuma hannunsu cikin najuna.kuma bata ga wani ya nuna hakan wani abu bane,mami ce ta iso wajenta ta dafa kanta.
"Diyata mekikeson ci"
Sadda kai tayi tana murmushi cike dajin kunya tace"aa mami ba yanzu ba"
Kallon Abdoul tayi tace"son kaifa"
Dage girarsa yayi yace"ba yanzu ba"
Murmushi mamin tai tana cewa oky ..........bayan wani lokaci kuma akazo za,a yanka cake wukar tana hanunta saiya dora nashi hannun bisan nata suna yankawa tare,mai hoto yanata daukarsu.
Cirowa tayi ta kai bakinsa ya tsura mata ido yanata kallonta,baidace komi ba yajima idonsa kamar zaifado saboda kallonta sannan ya bude bakin yagutsira,haka shima ya bata sannan sukabi kowa suna saka mashi ga baki.sune har karshe shabiyun dare anata abuguda,karshe har nafara hamma hakan da mami ta gani yasa tacema malik atashi hakanan kowa yaje ya kwanta,ai angode Allah ita dama bada son ranta aka hada partyn ba duk zakiyyace da ni,ima.
Hanuna cikin na mami tajani har dakinta daya gaji da haduwa komi yayi gwanin sha,awa.
Zaunar dani tai bakin bed dinta ta shiga toilet ruwan wanka tahada mun daga inda nake inajiyo kamshin turaren wankan da take xubawa,don inajin ma ba daya bane gaskiya.
Fitowa tai da towel ga hannunta ta bani.
"Shiga kiyi wanka kifito saina rakaki dakinki,abincin ki yana can yana jiranki"
Cikin jin kunya tace ansa da to mami,sannan ta shiga toilet din tajima tsaye tana kare mashi kallo,kamar wani wajen shakatawa gaka bayin yake komi gwanin kyau da burgewa.
Kayan ta cire ta shiga cikin komin tana lunshe ido,ruwa mai dumi mai gasa jiki ga kamshi na gaske dake tashi,tabbas wanan zai jima jikinta bai fita ba.
Akallah ta dauki minty goma sha biyar kafin ta iya fitowa tana tsane jikinta sannan ta dauro towel din,ta fito.
Wasu kayan bacci ta gani riga da wando dogon wandone har kasan guiwa,sai rigar mai gajeran hannu kayan masu tsananin kyau da taushi.lotion ta shafa sannan ta fesa turare tasaka farar powder kasan da lipstick,ta gyara gashinta ta daure da ribon ta saka hular kayan.
Tayi kyau Sosai da sosai har saida tayi murmushi,wata natsuwa takejin tana shigarta ta daban,jitake yanzu bata da sauran damuwa baba ya riga ya gama mata komi illa ta dawwama tana mashi fatan Allah ya biyasa da aljanna.
Mamince ta shigo ta bata hijib kamar tasan bazata iya fita ahaka ba murmushi tai tana sada kai ta ansa ta saka.
"Kibar jin kunyata har haka safiyya kamar ni,ima nake kallonki don Allah karki doraman nauyinki nima nafison muna yin abu irin na diya da uwa,kinjiko ki saki jikinki nima kamar mamanki ce"
Tana wasada yatsunta tace"insha Allah mami zanyi yadda kikeso"
"Yawwa Allah yayi maki albarka muje na rakaki"
Tafiya suke har xuwa wani part din na daban,shima ba baya ba wajen kyau komi ya hadu har bakin bed room ta rakani tace"akwai abinci nanan an ajiye maki kici kisha ki kwanta saida safe"
"Nagode mami mu kwana lafiya"
Ta ansa mata cikin kulawa sannan mamin ta juya tatafi,fitowarsa wanka kenan yana shiryawa cikin kayan baccinsa hankalinsa kwata kwata baya tare dashi,abubuwa sun cunkushe mashi kai!wai suna nufin anyi aurensu da safiyya how comes tayaya bacin tace bata yinsa kuma babanta yace bazai bashi ba,duk ciwon dayayi akanta hakan baisa ya ce ya amunce ba su dady da Abbi babu irin zaryar da basuyi wajensa ba ya rufe idonsa to shine kuma bayan ya warke anga bai mutu don itaba aka daura auren.uhmmmmm tabbas sun bashi surprise kuma yagode don baiji koda daidai da kwayar zarra na sonta ya ragu ba,amman saiya rama abunda tai mashi.ya ajiye duk girman kanshi da ajinsa ya furta mata yana sonta yaringa zarya gidansu,amman ita anbata zabi tarufe ido tace bata san haka ba.murmushi yayi bai taba zaton cewa zai sameta ba,ba kamar dayaji labarin aurenta wajen malik...........turare yake sawa yaji anbude kofa jiyowa yayi yana kallon kofar,don yasan kowa ya kwanta saboda gajiya tun kwana biyu basu zauna ba sai hidima suke yasan dai an daura auren malik da zakiyya,duk tunaninsa hidimarsu ce ba tashi ba.
Tsura mata ido yayi kamar yadda ta tsura mashi nata.jikinsa mutuwa yayi irin mutuwar da baitaba ji ba har saida ya runtse ido sannan,ya ajiye kwalbar turaren tana rungume hannuwa sadda kai tai tana murzar yatsunta cikin abayar,bata dauka daki daya zasu kwana ba aida bata shigo ba.
"Lafiya malama,ko kinyi batan hanya ne"
Kallonsa tai da mamaki jin abunda yace girarsa ya daga yace"ehy,waye yace nan ne dakinki"
Kamar mai koyon magana tace"mami ce ta rakoni niban sani ba ai,kayi hkr"
Tana jiyawa tanufi fita.
"Wait"
Ta tsaya tana jin gabanta yana faduwa ga duk alamu Abdoul fushi yake dan ita,kuma tasan hakan zata faru don abunda tai ita kanta ya dameta amman bata da yadda xatai da baba alokacin.
Bayanta ya tsaya yana rungume da hannayensa yace"ina kuma zaki,bakince mamice ta rakoki ba its oky shigo ki kwanta"
Jiyowa tai tana narai narai da ido ta girgiza kai"kabarshi zanje falo kayi hkr pls"
"Okay kijamun abun magana ko,to ban amunce ba nace ki wuce halan ma wancen abin ba nau bane shiyasa kiyya har take rawar jiki waje jerawa"
Ya nuna wani table da aka jera kuloli masu kyau da lemuka.
Jujjuya kai tayi cikin sanyin jiki tace"ban sani ba ance dai abincin yana nan"
"Okay muje ki dan sanmun yunwa nakeji"
Ya wuce wajen table din tana biye dashi baya,kallonsa take kamar ancanza shi yayi rama sosai kuma ya kara haske da kyau.gashi ya sake barin gashi afuska saiya kara mashi kyau,dakin sai kamshi yake.
Kujera yaja guda biyu dake zagaye da table din ya zauna itama ta zauna kan guda,shiya bubbude kulolon ferfesun kifi sai faten Irish yasha ganyenyaki,kaza gasassa da lemuka masu sanyi.
Kalonta yayi yaga duk ta takure ya dauke kai,ya zuba nashi ya hauci baibi ta kanta ba,yana gama wa yaje ya haye gadonsa ya juya mata baya.
Duk abunda yake na karfin haline,ba har xuciyarsa ba yana son dai ta gane cewar shi Santa yake da xuciya guda ba wani abu yake nema ajikinta ba.
Hawaye suka silalo mata tashare,tatashi ta kwanta kan kafet din dake malele adakin tana dunkulewa cikin hijab dunta,me hakan yake nufi me yakesin nuna mata,wanan daren daga shi har ita basu runtsa ba saida ya tabbatar tayi bacci ya daukota ya sata gabanshi,tusata yayi kamar tv yana kallo haka asubar fari taxo mashi

Kuyi hkr zuwa anjima zan sake wani postinig din kkda read more biyune
[10/17, 4:57 PM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSEER*
*(ALFAH)*

WRITTEN BY

MRS BB
MOM MUHSEEN

FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970

🅿️............64
Chapter 79 · 0% Book details