← Book details Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 87

Sashe 65

Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau da shirin koma wa wajen aikinsa ya tashi,tun wajen bakwai ya gam shiryawa yafito bai saka ran samun abun kari ba,don yasan irin wannan lokacin daga ita har malik basu isa tashi ba.
Amman sai yajiyo wani kamshi wanda ya ankarar dashi cewar tatashi,dandanan yaji yunwarsa ta ake yunkurowa.
Agogonsa ya kalla yaga ya kusan makara kuma yanzu haka mutanen da ya ansa zama dasu suna can har sun iso tun da asuba jirginsu ya sauka.
Hanyar kitchen din ya nufa yana dan daidaita fuskarsa.
Ta juya baya tana soya kwai ga dankali nan ta kwashe cikin gwagwa,saman gas din kuma farfesun yan cikine take idasa dafawa.ga placx nan komenene ta hada ciki kilan tea ne,inji xuciyarsa,
Rungume hannu yayi ga kirjinsa yana kallon bayanta,doguwar rigace ta bacci iyakar guiwarta amman mai kauri baka ganin jikinta,gyaran murya yayi wanda ya sata tsorata har tana yadda ludayin datake juya kwan dake cikin kasko.lumshe ido tayi tana ajiyar xuciya ta duka ta dauki spoon dinta tana juya tace"ina kwana"
Murmushi yayi ya ida sa shigowa sosai yana cewa"uhmmm wannan kamshi dakika bude gidan dashi haka,mekike aikata mana ne"
Banza tayi dashi amman kasan ranta murna ce fal kamar me.
"Don Allah ataimaka mun ahada mun cikin basket sauri nake kuma bazan iya jira naci ba,Allah yasa andafa dani"
Nanma taimashi banza ta gama soya kwan ta dauko kwandon da yaje xuwa office dashi da containers din da take xuba mashi,ta fara xubawa ko inda yake bata kalla ba.
Jinjina shariyar da take dashi yayi amman sai yaji hakan kuma ya burgeshi,hakika ballagazar mace marar aji batai ba ace kina mace Mai daraja kina watsar da ajinki da kimarki.
(Yan mata take not akula da kima da martaba,suna da matukar muhimmanci ga rayuwarki ko kau ga mijinki ne balle saurayi)
"Wai har yanzun fushin ake dani zakiyya"
Wani kallo ta jefa mashi ta dauke kai ta cigaba da aikinta kurin.
Dariya ya danyi kadan harta kalleshi don shidin bai cika fiddo dariya ba sai ta kama,gira daya ya daga mata ta dalla mashi harara.
Ta gama xubawar ta ajiye mashi gefensa tana tattara wanke wanken wanda zatayi yanzu.
Matsowa yayi kusa da ita kamar zai rungumeta muryarsa kasa kasa yace"I'm very sorry kiyya,nasan laifina yasa har yau kike fushi ko?"daskarewa tai awajen don gabaki daya jikinta ya dau wani sanyi,don abun yazo mata abazata.
"Idan nadawo zamuyi magana oky"
Daga kai kurin tayi yadauko abincin yafice sai lokacin ta sauke wani gauron numfashi.

************

Bayan fiyah ta dawo daga jarabawa yau wajen karfe shidda harda wani abu ma,tana shigowa gida akafara kiran sallar magruba.
Baba bai dawo ba saida aka gama sallar yesmin na kitchen yau ita ke shirya abincin dare,tuwon shinkafane miyar agushi baba ya siyo naman rago an xuba aciki (harnaji miyauna ya tsinke🤭)
Tunda fiyah ta dawo tana daki bata jin dadi ko kadan,don har wata masassara takeji.tana cikin tsananin kewarsa tana kan nadamar abunda yafaru,jitake inama ta fada mashi cewar soyayyarsa itace weakness dinta,itace farin cikinta da bakin cikinta.rashinsa gareta wani babban bigirene da bazata iya misalta shi da komi ba.
Mamace ta shigo dakin don yesmin tace mata tana daki kwance.
"Safiyyah lafiya kike kuwa"
"Bandai jin dadi ne mama kamar xanyi xaxxabi"
"Subhanallahi,ainace ku daura net kun kiya badole sauro ya cije kuba,bari dalha taxo saiya siyo maki ACT,kifito kici abinci harda yunwa ma kilan"
Babane yashigo yasa mama ta fita tana ansa sallamarsa.
Take gaya mashi abunda ke damun safiyyar,yaje shima ya dubata yace ta fito yasa mata tabarma tasha iska,saitaci abincin tasha magani.
Gaba daya suke cin abincin a tire guda,sun hirar su gwanin ba sha,awa,kallon safiyya baban yayi yace"bayan masassara akwai abunda yake damun ki uwata ko?"
Yake tayi tace"aa baba babu komi bayan ita,hada gajiya kullum ina kan hanya babu hutu shiyasa ma kila ta saukomun"
"Allah ya baki lafiya,muhseen ya kiraki kuwa"
Kanta yana kasa tace"eh ya kirani ina cikin jarabawa saida nafito na yasake kiraa"
Jinjina kai baban yayi yace"idan ya sake kira ka safe,kice ina son ganinsa idan ya samu lokaci"
Da to kurin ta bishi,tana jin dadin abunda zaifarun don tasan maganar yesmin zai mashi.
Dalha ya shigo da maganin nasha yafita,bai jimaba ya dawo yace ana sallama dani.
"Waye"
Inji baban.
"Kanen uncle yahya ne yazo"
"Kace ya shigo batajin dadi bazata iya fitowa ba"
Dadi ya kamani don kona fitar bansan me xance mashi ba.
Yesmin naga ta shige daki tana jin ance haka,murmushi nai nace araina makira tasan ta samu abunda takeso.
Sallama yayi mama ta ansa mashi baba na nuna mashi tabarmar dayakai.
"Bisnillah anan dana zauna"
Ya na murmushinsa na gado ya zauna yana gaidasu cikin girmamawa,hakika muhseen mijin aurene kawai dai ni banda ra,ayinsa ne shie kawai.
"Yaya muhseen ina wuni"
"Lafiya lau safiyya ashe bakiji dadi ba sannu Allah ya sawake"
Tace"ameen nagode"
Baba ya kalleta yace jeki ciki zamuyi magana dashi,kekuma mamansu xubo mashi tuwo karkace ka koshi zan dauka baka daukemu iyayeba"
"Zanci baba kayi hkr"
Mama tatashi taje ta xubo mashi ta kawo ta ajiye tana samun waje daga gefe itama ta zauna,yana ci baban yana janshi da hira kadan kadan har yaci dayawa yana ajiye spoon din.
"Na koshi mama ya isan haka nagode sosai kuma tuwo yayi dadi ba kamar tuwon jawaheer ba"
(kanwarsu dake bi mashi agida)
Dariya mama tai baban yana tayata tace"kadai raina nata ne amman ba dadine babu ba"
"Wlh mama karma ki hada da wanan nakin,don ita tuwonta kamar talge haka yake,kanaci zai ka nemesa karasa"
Dariya suke ita baba ta GB wuce ta kai kwanonin kitchen baban yace"wannan din kuma da kake yabawa qanwarka yesmin tayi ai"
Zaro ido yayi"dagaske,gaskiya ta yi kokari sosai zan turo jawaheer ta ringa koya wajenta.
Gyaran murya baba yayi yace "muhseen"
Jin yadda baban ya kirashi yasan maganace mai matukar muhimmanci,yadago yace"na,am baba"
"Magana zamuyi dakai mai muhimmanci,ina fatan zaka fahimce mu kuma xaka dauki abunda muke nufi da kai"
Jinjinakai yayi yace"insha Allah baba xanyi duk yadda kace"
Gyara zama baban yayi yace"ammm muhseen alokacin dana ansa maka kan maganar uwata ashe munyi kuskure kadan,wanda har hakan yake son kawo damuwa.
Inason nabaka hkr abisa abunda xance maka,don Allah ka hkr da safiyya ka nemi qanwarta yesmin.wasu dalilai suka nace haka saboda ganin cewar uwata batayi na,am da maganar ka ba kuma bata fadi cewar bata so ba,sainaga wannan zai iya kawo cikas ga zaman takewar ku maimakon kuji dadin zama da juna ana iya zamun akasin haka,saboda kaunar danake maka yasa naga bazan iya kyaleka ban maka tayin auren yesmin ba,ko ita za a mu dace amman idan kanaso bazan ta kuraka ba don bazan so wani ya cutu ba ya kagani,inbaka lokaci kaje kayi shawara agida kokuwa."
Ajiyar xuciya yasauke yana jin wani dan ciwo kasan ransa,hakika babu abunda yakai kaso akika amman kuma hakan yafiye mashi sauki daya aureta bata sonsa,bazaiji dadin zama da ita ba koda kau ta danne ta nuna bakomi,amma ita ai abun zai cutar da ita,sannan itama yesmin din baida tabbacin zata soshi balle har yayi saurin na am da maganar baban,hakika yana son safiyya so marar iyaka,amman hakan bazai sakashi yaso kanshi ba don haka ya hkr da ita maganar yesmin kuma itama dole yasan idan ita tanuna tana ra,ayinsa shikuma zayyi alkawarin kulawa da ita fiye da tunani kuma zai yi iyakar bakin kokarinsa wajen sakata cikin xuciyarsa,har Allah yasa mashi sonta.

"Kayi shiru muhseen,idan kaga akwai takura wlh babu tilasci kafafi ra,ayinka naji"

Ya sake sadda kanshi yace"baba hakika na fahimce ka kuma abunda ka fada gaskiyane,ban boye maka ba tun wancen lokacin inason safiyya,amman sonta bazai saka na cutar da ita ba,don haka na hakura da ita Allah ya bata wanda takeso nagari wanda yafini,sannan maganar yesmin.
Baba karku tilasta mata bazamu san meke ranta ba,kar axo ayi abunda zai kawo damuwa inhat yesmin bata da ra,ayina baba don Allah ayi hkr da maganar nan Allah xai bani wata makamanciyar safiyya"
Tausayinsa ya kama baba da mama,baban baiso fallasa yarsa ba baiso sanar dashi son da take mai ba,amman ya xama dole kodan ya samu kwarin guiwa,don harga Allag yana son yaron yanason sake hafa xuria da ahalinsu.suna da kirki da daddatako.
"Muhseen karka damu inhar akan haka ne,yesmin ta nuna mana kai takeso mafarin kenan uwata tazowa mamansu da maganar daba don haka ba,har ayi bikinku bazamu san bata sonka ba,kuma kaima nai imanin baxata nuna maka ba.amman saboda ta gano yar uwarta tana cikin wani hali akanka yasa ta yanke shawarar sanar damu,kaji dalilin zamanmu dakai.don haka kaje kayi shawara da mamanka ko dan uwanka,duk abunda sukace saikayi aiki dashi."

Murmushi muhseen yayi yana tuna wasu abubuwa dasuka faru ranar dayaje gano baba asibiti,da lokacin daya daukosu daga asibitin,sai randa ta biyosa ya kawo mama gida sanda fiyah bata lafiya,hakika tana da hankali da wayau tana sonsa bata bashi wata dama dazai gane ba,saidai zata ringa janshi da labari na ban sha,awa da dariya.bazaka taba ganewa ba,tabbas da matan wannan zamanin ne damarta tafarko data samu sanda ya daukota bayan sun ajiye mama alokacin zata barje kolinta ta gaya mashi,amman tana da kunya da kawaici ta danne saidai aka gane amman badai ita ta furta ba.
Murmushin yakeyi yanajin kaso sittin na amuncewa da ita yana saukar mashi,cikin sanyin murya yace"baba na amunce nima ina sonta,duk da haka zan sanar da su halin da ake ciki nasan bazasu ce aa ba,suma ai suna sonada daya daga cikinsu,Allah yasa hakan shiyafi alkairi"
Dandanan fuskar baba ta washe hakika yaron yana da hankali Albarka yayi ta samai shida mama,da zaitai ya ajiye masu dubu goma yafice,baba nacewa ya barshi amman bai dawo ba.
Chapter 65 · 0% Book details