← Book details Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 87

Sashe 77

Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Zuwa safe jiki yayi sauki sosai ta nemi ciwon ta rasa saidai abuna ba,a rasa ba na gajiya da rashin kwarin jiki,nurse din ta rubuta magani tace asiyo ta ringasha saida aka siyo sannan tatafi,sai lokacin Anty da inna suka jata dole saita kewaye gidan ta gani,daker ta iya binsu sako da lungu data gaji ta dawo falo ta zauna tana kalonsa,hakika komi sai sambarka yanzu damuwarta tafiyarsu anty gashi sunce gobe zasu juya,ai tunda sun kawota sunga waje Allah yasaka albarka,sai sundawo suna wannan kalmar ta sai sundawo suna ita tasata kuka har kanta yayi ciwo.
Dadaddare suna hira falon ga kallo sunayi wanan mai murya irinta malik yayi sallama ya shigo,bayansa wasune dauke da kwalaye da ledoji manya yaudai saitaga waye wannan mai muryar yaya malik........jiyowa tai ta sauke idonta akansa yana murmushi suna gaisawa dasu Anty............duk idanunta ta fiddo tana zuba mashi su cike da tsananin mamaki da alamomin tambaya,amman sai ya wayence yana gaidata.
"Amarya barka da dare ya bakunta".sarawa kanta yayi mehakan ke nufi miyanta ya kafe daker tayi gyaran murya tana yake tace"ina wuni"
Kin ansawa yayi yana dire kayan gabansu yana ware wasu yana bayani.
"Inna ga wadannan kayayyakin zaku tai dasu gobe duk nakune,inji angon yace kuyi hjr da safe zai zo kuyi sallama wadannan kuma amarya bari ashigar maku dasu store"
Ya fada yana duka wa yana daukar su ya nufi store din,da murmushi fuskarshi bin bayansa tai da kalo kamar wata sakara kafin ta sauke wata nannauyar ajiyar xuciya tana dafe goshinta,duk a rikice take wannan lamarin da daure kai yake.
Fitowa yayi yana cewa"zan wuce Anty saida safen zamuzo tare yayi maku sallama"
Godiya sukai sosai suna saka mashi albarka.
"Gaskiya mutanen nan suna da kyauta Allah dai ya zaunar daku lafiya safiyya kiyi hkr kinjiko,aure babu inda baya kai mutun kuma ki saki jiki da yan uwan mijinki suna sonki suna ji dake,shima kiyo kokari ku gyara tsakaninku Allah yabarku tare"
Inji inna hasana na mata gwalo da dariya.
Cikin muryar kuka tace"inna kinganta ko,dariya take mun tana mun gwalo"
Murmushi innar tai tana ma hasana fada tace"kema kwanan nan zamu tsayar da magana ai,nagaji da laben da jalal yake mana duk sadda yazo,ana fakewa da zumunci"
Duk mamaki da al,ajabi ya kama mu nida anty,itakuma tana rugawa daki tana cewa inna tayi shiru.
Anan innar kecewa ai sun kai shekara suna soyayya shirutai dai taga gudun ruwansu,ganin basu d niyyar baiyyana kansu yasa tace zata gaya ma su baba.
Abun ya mana dadi sosai har hakan yasa nasaki jiki dasu muka sha hirarmu ta bankwana,jinake inama zasu zauna dani amman nasan hakan ba mai yuwuwa bane.
Bamu kwanta ba sai karfe daya ranar banyi bacci ba tunanika suka cika xuciyata,ina cikin kokwanto komi ya cushe man.duk yadda naso baccin gagarata yayi nai salla raka,a biyu na roki ubangiji daya sakamun salama acikin xuciyata,ya sanyaya mun raina nayi zaman aurena kamar kowace mace,ya ban ikon yin biyayya wajen mijin da bansani ba yaba ikon danne duk wani miki na soyayyar danake ciki.
Rashin baccin yasaka na kamara sadda na tashi na nemi su inna ban gansu ba,duk inda zan ga daya naduba babu su dakin da suke kwana arufe falo na dawo na zube gefen kujera ina kuka,meyasa xasu tai bamuyi sallama ba meyasa haka kuka nake sosai da sosai.
Gashi ko karya wa ban ba kuma yunwar nakeji sosai,na kasa tashi naje dining naci abincin tunda gashi can ankawo.
Ina nan zaune naji anshigo mata ne biyu suka shigo turawa ne suduka,gaidata sukai suna cewa sune masu aikin gidan dayar zata iso.
Kallonsu tai cike da haushi tanuna masu hanyar cikin gidan,tana binsu da harara kamar sune sukai mata laifin.
Saida taji yunwa na niyar kassarata taje tahau cin abincin,tana hawaye gashi bata taho da waya ba mama ta barwa wayarta.
Haka ta wuni cikin kewa daga tai salla taci abinci saita kwanta,har gajiya tai da yin bacci ita bata saba zaman haka ba babu aikin fari balle na baki,ahaka dare ya cinmata duk atsorace take haka tayi wankan ta ta dawo falo tai sallar magriba,itama sallar badan alam dake bugawa ba duk time dinta bazata gane ba,don bataga agogoba,itafa atakure take bata saba da wadannan abubuwan ba tafisaba wa dana kasarta nigeria.
Tana gama salla mai aikinta linder ta iso cikin girmamawa tamika mata waya.
Ansa tayi tana binta da kallon tambaya,cikin harshen turanci tace mata"ogane yace abaki akwai sako aciki kiduba"
Harara ta maka mata amman ba gane metake nufi da hakan tai ba,ta juya ta koma bangarensu.
Duba wayar ta cigaba dayi tana shiga ko ina bata ga komi ba,tsaki taja ta ajiye tana rabka tagumi,bayan minty biyu taji sako yashigo har kerma hannunta yake ta dauka tana dubawa.

_"KIYI WANKA KISHIRYA IN THE THIRTY MINUTES AND WAITING FOR ME"_

kallon wayar take kamar zata cinyeta don haushi,au bazai iya kiranta ba saboda girman kai,shin wai taya ma zata iya zama da wannan bahagon mutumen.kodan yana ganin yana da kudi zaimun wulakanci shiyasa ya kawoni kasar da babu uwa babu uba babu dangin iya balle na baba,hawaye suka silalo mata tana sharewa itafa tasan sun kulla amana da kuka yanxu.daman gata sa arhar kuka,kallon jikinta tai taga bata jima da wanka ba,kawai dai kayan baccine jikinta.
Tatashi tanufi bedroom din cike a tsoro,bata saba zaman gidansu babu kowa ba balle wannan uban gida mai girma ga sako da lungu gani take kamar wani xaixo ta shaketa ya kasheta yajefar da gawarta..........wani marron less ne da zanen manyan flowers milk sai kyalkyali yake,baya da nauyi shiyasa ta daukoshi riga da siket ne siket din yayi bala,in fitar da shaf dinta don randa ta fara sasu ranar alhamis din auren mutane sai magana suke gaskiya amarya tasha kyau,masha Allah tubarkallah.karshe saboda haushi ciresu tai saboda bata son ma abunda zai sa ace tai kyau abikin da ba sonshi take ba.
Ajiyar xuciya tai bayan ta sak kayan,rigar irin mai budaddar kafadar nan ce akai mata,an kawata gabanta da wani style mai kyai.
Powder ta saka da marrom din janbaki wanda ya sake fiddo ruwan kyanta kunsan fararen mata idan suka saka jan janbaki ko marrom sosai yake masu kyau.
Saida tasa taji kamar ta goge,amman ganin bata fuskarta zatai yasa tabarshi.gyalenta dan karami wanda iyakarshi rolling shita dauko ta nade kanta dashi bayan gashinta data gyara ta saki jelar baya,bata aka kallabin ba rolling din kurin tayi tana saka kwalli ta gyara girar idonta sannan ta saka turaruka dake jere akan mirrow dinta,kala waje biyar kowane da kalar kamshinsa.
Yar pos dinta milk da high hills dinta suma milk,ta saka masha Allah saita fito sak amaryarta tayi kyau sosai don fiyah bata taba kyau irin na yau ba,don ita kullum cikin hijab shiyasa baka gane dirin da Allah ya mata.
Ahankali take takawa tana barin dakin,ita kanta saitakejin ta wani iri jinta take kamar wata sabuwar halitta,tasha ganin mata abuja irin yadda tai wannan shigar,saitake ganin Allah ya sawake tayi wannan shigar tafita,saigashi yau tayi kuma tana ganin tayi kyau amman kunya takeji tafita haka kamar za,aita kallonta saboda bata sa abaya ba.
Falon ta koma tadora kafarta daya kan daya,tana kallon wayar da linder ta kawo mata.
Minty talatin yana cika aka danna dow bell cikin sassarfa wannan arniyar tazo ta bude tana risina wa.
Kalon kofar fiyah keyi tana kallon mutumen dake bakin kofar,bakinta taji yace"yaya mali"
Murmushi yayi mata yana sallamar linder dake sunkuye.
Hanya ya nuna mata da hannunsa yana dan rissinawa irin girmamawar nan,kamar sakara take binsa da kallo.ta kasa shigewa gaban kasa shanye mamakinta tayi karo na biyu tace"yaya malik kaine"
Murmushin yake yana shafa kanshi baice komi ba yace"plzzzz let's go"
Idonta yayi kwalkwal zatai kuka yagirgiza kai.
"Karki bata kwaliyarki mana muje"
"Bazanje KO ina ba saika yimun bayanin me ake boyewa man,ni nagaza gane wa"
"Sorry muje zaki fahimta yanzu lokaci yana kurewa"
Dole ta hkr ta shige gaba ya rufe kofar yana binta abaya har waje,wajen mota ya bude mata baya ta shiga ya shiga gaba shida driver suka dauki hanya.
Gaba daya tunaninta ya rabu kashi kashi,xuciyarta tayi rugurugu da tunani wai wata aura ne meyasa ma tun tuni bata damu da sanin waye ba,saiyanxu da take son sani ake ja mata rai.
Chapter 77 · 0% Book details