← Book details Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 87

Sashe 38

Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tana tafiyar gabanta yana faduwa har xuwa bakin kofar shiga,togewa tayi hasana ta jata suka shiga da sallama..............idon malik akan su yana cikin kujera,hasana cikin fata ta nemi waje ta zauna tafara gaisa malik.
"Kece yar rakiya kenan,ya kike yagidan"
"Lafiya lau wlh anzo lafiya"
"Alhamdulillah ansha suna Allah yaraya me akasamu"
Dariya tayi tace tana nuna fiyah"gata nan itace aka samu"
Cikin murmushi d mamaki yake kallon fiyar yace"iyye qanwata ashe takwara akayi,"
Murmushi tayi mashi bata ce uffan ba,hasana ta juya ga Alfah tana gaidashi,banyi tunanin zai kar mata fuska su gaisa ba.
"Lafiya lau ya kike kunsha suna Allah yaraya"
Cike dajin dadi ta ansa tana tambayarsa aiki.
Malik ya ce"qanwata baku gaisa da abokina ba"
Kamar karta kallai suna ta hira da hasana cike da wayewa da sanin makamar zance,kallonsa tayi sosai taga irin yadda yayi mata masifar kyau,har ta shaga da kallonsa saboda yadda kayan suka ansheshi,ga hasken dakin dake haskawa sai hakan ya karawa fuskarsa kyau.
"Kinga yar uwarki zata cinyeni da kallo bacin ko gaidani batai ba"Alfah ya cewa hasana.
Dariya duk suka saka mata wadda jitai kamar ta nitse don kunya,wai garin yaya ma har ta shagala da kallonsa haka.
Sadda kai tayi tana murzar yatsunta hasana tace"kinji to fiyah,baki gaida bakon naki ba."
Kasa magana tayi wai meza tace mashine itafa bazata gaidashi ba,malik yace"qanwata harni ma din bazaki a magana ba"
Bata kallai ba balle ta tanka,hasana tace"kila fa kunyata takeji,kinga bari nabaku waje sai anjimanku fa mun gode"
Sallama tayi masu ta wuce,malik yace"tunda ko ruwa baza,abani ba nibari nayi karanbanin dauka insha."
Sai lokacin tayi saurin tashi tana ajiye wayarta ta matso da tabke din gabansu tana bude kwanukan tare da zuba lemukan acikin cups sannan ta zuba ruwa shima,dauka tayi ta ba malik cikin sanyin murya tace"kayi hkr yaya malik ga ruwan,don Allah kudan taba wadannan don ku Anty tayi"
Ansa yayi yana cewa"ainayi hkr qanwata kece za,aba hkr don nasan fushi kike damu,tun jiya wayarki akashe meyasa?"
Satar kallon Alfah tayi taga idonsa akanta ya shige cikin kujera yasaka yatsa guda yana sosa girarsa.
Dauke kai tayi tace"ba haka bane yaya malik kawai dai nayi hakane don a barku kuhuta don naga alamar xuwa wajenu danake ysa ake cin xalina ake yimun ugunta ana gaya man aganganu babu suger"
Malik yakalli Alfah yaga har lokacin fiyah yake kallo kamar zai hadiyata.har cikin ransa tayi masifat yi mashi kyau,amman bakinsa yayi nauyin da bazai iya furtawa ba,bayajin ma koda wasa zaiya furta hakan amman yadda tayi mashi yasa yaji wani abu yatsaya mashi ga makoshi,babu sannu da zuwa babu ina wuni babu karramawa.malik ne yace
"Kiyi hkr to insha Allah baza akara ba,,ga Abdoul nan ma yazo taya ni baki hkr ko Alfah"
Yajuya yana kallon Alfahn.
Tashi yayi zaune yace"hakurin me zan bata bacin nida ba,a dauka da mutunci ba ko ruwan ba,a bani ba bae nasaka ran zan samu sannu da zuwa kaga kuwa zuwana baida anfani,kaida keda mutuncin da har za,a kulaka kana iya zama zanjira fitowarka."
Ya mik'e ransa ab'ace don har cikin karshen ransa fiyah ta kuntata mashi,badan yaso yataho ba amman shine zai samu wannan tarbar.
Dandanan taji hankalinta yatashi,haushin kanta ya kama ta bazata so yatai da fushinta ba koba komi bakonta ne,tara sa gane kanta zuciyarta rawa take inhar tana sauraren muryarsa,idaniyarta bata hutawa inhar yana mata wannan kallon,takaza control din kanta akan wannan sabon yanayin data kejin kanta,cikin sanyin muryarta tace ma malik.
"Yaya malik kace yayi hkr yadawo wlh niban wulakanta shiba"
Murmushi malik yayi yace "aa aibani nayi mashi laifi ba qanwata kece don haka kibishi kibashi hkr kafin ma kidawo bari naci wannan yana jawo kwanon snacks."
Jikinta amace zuciyarta ta cushe bata son yatai da fushinta harga Allah bata so ransa yabaci ba,
Kallonta yayi yace"kije mana"
Kamar Mai tausayin asa tatashi tafara nufar kofar fita,dariya yake son yayi amman baison tagani.
Waigowa tayi kamar zatayi kuka tace"yaya malik karya dakeni,karya zuciya ya mun tsawa."
Girgiza mata kai yayi yace"bazai maki haka ba kidai bashi hkr kisamu yadawo ya ci wannan garar don wlh yamun dadi sosai maza jeki"
Haka ta bude kofa ta fita aikamar jira yake ta fitan ya dunga kwasar dariya,lallai tarkon nan yayi kamu sosai,insha Allah komi zaizo da sauki.
Yana cikin mota ya kwantar da kujerar zaman banza ya kwanta ya rufe fuskarsa da fesin cap di sa.
Jikinta wani irin sanyi yayi ahankali ta kwankwasa glass din window din,tunda ta tsaya kamshinta ya iskoshi jiyai xuciyarsa na mashi kai kawo,ahankali ya sauke glass din baiyi magana ba baikuma dago ba,lawallar kuda ta kamayi tarasa abun cewa bakinta rawa yake wana mutun yana ata kwrjini cikin kwana biyunnan.
"Sauro yana shigo mun inbakida abun cewa plss zan rufe glass dina"
Bakinta yana kerma muryarta kamar zatai kuka tace"pl....s kayi hkr.....karka tafi kadawo don Allah"
Wani sanyi dabai san daga inda yake ba yaji yana sirarowa cikin ransa,amman sai yayi shiru yana adduar Allah yasa ta sake bashi hkr karta tafi.
Bata san dalilin hawayenta ba muryar na rawa tasake cewa"plssss kaji,im sorry........"maganar ta katse sanda kukanta yake fitowa
Wani suka yaji ga kirjinsa jin muryarta na fidda sautin kuka,ahankali ya tashi jiyake kamar anzare mashi duk wata lakka daga jikinsa muryarsa kamar tafito daga cikin frig yace"come in"
Ahankali ta zagaya wajen zaman driver ta shiga kanta akasa hawaye na bin fuskarta,tunda yake rayuwarsa bai tabajin kwatan kwacin irin halin dayakeji yanzu ba.koma wa yayi ya kwanta yanajin wani irin yanayi na sake bin gabbansa.
Ahankali take sharar kwallah,inza,a yankata bazata iya cewa ga dalili ba.
Hanky taga ya miko mata babu musu ta ansa tana kaishi ga fuskarta,wani kamshi ne ta shaka daya saka taji duk wani kunci na xuciyarta yaya yaye,ahankali take share kwallar har ta samu kwallar ta tsaya.
Sannan ta mika mashi bai ansa ba yace"nabar maki"
Tanajin yadda xuciyarta take bugawa numfashinta kanshi ya canza salon fita,
Kamar mai koyon agana tace"kazo muje kayi hkr ko lemun kasha don ku akai"
"Danshi dai,ni awa za,ayi abu danni daman ban saka ran samun tarba daga gareki ba saboda baki daukan mutun ba"
Juyowa tayi duk da ba ganin fuskarsa take a tace"amman ai nabaka hkr ko"
Murmushi yayi yace"baimun ba kije kawai ngd kin baroshi shimadai bacin dnke yazo"
Kamar zata rushe da kuka tace"plsss mana kayi hkr to"
Malik ne yafito shida uncke suna hira cikin fara,a duk sai taji ta kunyata.
Fitowa Alfah yayi itama ta fito tana jin kunyar uncle tasan dole zai dauki wani abun,tunda gasu acikin mota su biyu.
"Tunda kunya ta hanaka cin kayan tarban bakon Abokina gashinan na saka an yimaka takeaway dashi,don Allah karkace bazaka ansa ba tasha wuya fa wajen hada maka"
Duk uncle ne yake wannan maganar.
Kanta akasa malik ya isa inda take cikin kasa da murya yace"qanwata kuka kikai mashi"
Tabe fuska tayi kamar zatayi kuka tace"kai yaya malik shine fa........kasa magana tayi tana sadda kai"
Dariya malik yayi yace"qanwata gaya mun meyayi maki yasaki kuka"
Kasa ansa shi tayi don bata san ma me zata ce mashi ba.
Hanyar shigewa tayi zata shige gida uncle yace ah safiyya bakiyi sallama da bakon naki ba,xokuyi sallama aimun gama maganar."
Sake musabaha sukai dasu yakoma cikin gida yana cewa maigadi idan ta shigo arufe gidan.
Malik tuni ya shige mota yana jiransu kasa motsawa tayi daga inda take saidai shine ya isa inda take,ta juya baya ya tsaya daga bayanta.
Tsayuwarsa yasa taji kamar ta koma kankara saboda wata irin mutuwar jiki tasame ta.
"Goodnight amman karki manta banyi hkr ba,zan tai da cewar nazo kin wulakanta ni saboda..........juyowa tayi kadan yahana ata fda kirjina ba tayi saurin dan ja baya,
"Don Allah..........lumshe idonsa yayi yana girgiza kai wanda kadan yahana numfashinta bai kare ba.
"Goodnight"
Haka yabarta kamar anshuka ta har motar tabar kofar gidan sannan ta samu karfin guiwar daga kafarta tashige.

Wannan dare xukatan mutane biyu basu huta ba.

Mrs bb
Mom muhseen.
[9/17, 3:38 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

🅿️.........31
Chapter 38 · 0% Book details