← Book details Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 87

Sashe 61

Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Dady ne yace"malik kamashi ku wuce gida,indan kan sune kake wannan haukan to ubanwa ya gaya maka zasu kubuta,bana son hauka da shirme comon get up"
Mikewa yayi idonsa jajawur yana kallon Abbinsa,yana jin wata suya cikin kirjinsa bangare guda kuma yana jin wata irin kewa da soyayyarsa suna sake narkewa cikin ransa.nunasa yayi da hannu yajinjina kai har zai fita ya juyo yace"dady safiyya fa sukai kidnapped,suka mata allurar maye hankalinta ya gushe,kasan me likita yace akai?cewa fa yayi taci sa,a jininta yana da kyau in wasune har haukatar dasu take,wlh tallahi da wani abu ya sameta na rantse da Allah saina cirewa kowanensu yan yatsu,sannan na zuba dalma cikin kunnensu to kugode Allah babu abunda ya sameta. kaikuma yanuna Abbin sa,sai kuma ya girgiza kai
yana ficewa daga wajen,malik yana bin bayansa.
Ansar tukin yayi don yaga alamar zai iya saka su accident,
Huci kurin yake yana dukan hannunsa da dayan hannun,ya kwantar da kansa jikin makarin kujerar yana jin xuciyarsa tana tafasa soyake ya samu wanda xaima dukan mutuwa,soyake ya huce hanshinsa ko akan waye soyake yaga yafitar ma dawani jini ga fuska ko ya samu sauki cikin ransa,malik ya juyo yana kallonsa yace"ka ringa sassauta ma ranka wannan xuciyar Abdoul wahala zaka ringa sha abanza awofi,karshe ciwon ka yatashi ka samu a uku"
Harararsa yayi yana jan tsaki,malik dariya ya danyi yana cewa"ko akaina zaka huce ne"
"Idan kacigaba da bata mun rai babu mamaki na huce akan ka tunda neman wanda xan hucen nake"
"To bismillah sarkin karfi kai naga alamar ma kafi doki karfi"
Yafada yana dariya cikin fada da masifa yace"ba doki na giwa ce ni,karka sake hauda fushin da bana ka ba bazakaji dadi na ba wlh"
"Sorry sir" yafada yana sara mashi.
Tsaki yaja yana rufe idonsa kurin,har sukaje gida bai sake magana ba malik ma bai tanka mashi ba.

**********
Cikin kermar murya Abbi yake cewa dady.
"Abdullahi wacece safiyya,ya take wajen Abdoul dina meyasa su mamman suka yi kidnapped dinta?"
Bubbuga kafadarsa yake cikin nuna kwantar da hankali,yace wa dpo din "koda wasa bance a sakesu ba,inda hali acigaba a basu horo har sai sun fadi wanda ya sasu wannan aikin"
"Yes sir"
"Sannan ko kusa kar wanda yazo neman belin su abayar don sudin yan ta adda ne bama wannan kadaine laifisu ba,acigaa da asu horo mai kyau"
"Okay sir"
Riko hannun Abbi dady yayi suka fito.
"Ina zaka dani baka gaya man abunda nake tambayarka ba"
"Yi hkr yaya sonake muje inda zan baka ansar,don bama ita kadai kake bukata ba ansar akwai ansoshi da dama dakake bukatar saninsu."
"Ina zamuje yanzu"
"Gidana dake gwarumfa zamuje sonake yau kasan wata gaskiya da kadauki shekara da shekaru baka santa ba,kasan masoyanka kasan makiyanka.kasan makasanka dake bibiyar rayuwarka,wai da kai xuwa kai belin wadancen yan iskan dakau kayi nadama ba karama ba."
"Wai Abdullahi duk wadanna maganganun na miye,nifa tambaya guda nai maka"
"Shiga mota yaya,bari na sallami guards dinka da driver ka alabashshi idan mungama saika tai inda zaka amman yau bazan kyaleka cikin kokwanto ba"
Yaje ya sallami driver da sauran security dinsa ya dawo yashiga motar sa suka bar station din.

************

Tunda fiyah tabar gida ko kadan kalaman baba basu bar kanta ba,yadda yayi saurin na,am da muhseen din ne yake bata mamaki,dabadan tasan halin ba baban ba da saitace saboda hidimar da yayi masu ce sanda yana asibiti yasa baiyyi shawara da ita ba yabadata.
Haka tai wannan exam babu sukuni,amman tana kyautaya zaton ta rubuta abun kirki.
Feea ta isheta da tambaya meke damunta taga yau bata da walwala ko kadan,tafe suke suna tracking don samun taxi feea bata zoda mota ba........."bazan ji dadi ba ina tare dake kuma ki kasa gaya mun damuwarki,bacin ni idan ina ciki kina kokarin ganin kin warware mun ita."
"Ba haka bane feea kawai dai inaga bai dace na damu wani da damuwata ba"
"Karkice haka koda banda abunda zan maki ai na maki addua ko"
Shiru fiyah tai tana nazari,bazata sanar da feea abunda ke faruwa itada Abdoul ba,har gara ta gaya mata baba ya badata ba tare da sanin ta ba.
"Feea baba ne ya bada aurena ga kanen uncle yahya,fea bana sonsa ban taba son sa ba ko sau daya,kwatsam yaje ma baba da batun son aurena shikuma ya amunce mashi kaitsaye."
Zaro ido feea tai yana cewa"aure waye wannan mai sa,ar.........hararar da fiyah ta sakarwa feea tasa tayi shiru tana dariya.
"Sorry gaskiya banji maki dadi ba,irin haka babu dadi su daman irin samarin nan idan sukaga sun kasa samo kanka da kansu kurin sai su kai maganar ga iyayenka,inda sun san wasu baza a ki ansar tayinsu na"
"Bayaga haka kuma abunda na lura dashi feea yesmin tana son guy din,din sadda baba yake sanar damu maganar fita tai ta kware tana tari,dana bi bayanta kuka naga tanayi aboye,alamar meye haka feea idan ba sonshi take ba"
Jinjina kai feea tai tace"tabbas haka ne ma fiyah,son shin take don haka inaga wannace damarki da zaki kubcewa aurensa tunda har kin tabbatar yesmin tana son sa."
"Daman abunda na yanke kenan zanje ma mama da maganar muyita cikin fahimta nasan zata yi wani abu akai"
Da haka suka tari taxi suka wuce gida,aranta tana kewar Abdoul gashi wayarta bata nan jikkar ma duka bai bata ba.

"Assalamu alaikum"
Fiyah tayi sallama cikin gidan lokacin karfe hudu daidai,mama na alwallar sallar laasar ta ansa mata tare da cewa"sannu da dawowa safiyya kinsha yunwa dai yau,tunda baki wani ci abincin kirki ba kuma baki anshi kudin abincin ba"
Dakinsu ta nufa tana cewa"bana jin yunwa feea ta siya mana abinda mukaci"
Tshige kurin don so take mamar ta fahimci tana cikin damuwa kozata fara tambayarta abunda gake damunta.
Anan saita zayyane mata abunda ke ranta,yesmin ta gani tagama salla tana linke sallayar.
"Adda sannu"
Kallonta tai taga bata cikin yanayin jin dadi,ba haka ta saba ganin yesmin dinta ba,zata iya rantsuwa da bata taba ganin ta cikin irin wannan yanayin ba.
"Yawwa sannunki kema yauba islamiyar yamma kenan"
Abayar ta ajiye saman kofar dakin tana cewa"aa akwai nice dai bazanje ba yau ban yi hadda ba"
Wannan yasake jaddada mata cewar yesmin na da damuwa sosai,don bata fashin islamiya kuma ba,a taba biyota hadda ba.duk sanda ta dawo zatai bitar haddar har saita iya sannan.
"Amman jiya ba naji kina yi ba,kuma banji inda baki iya ba"
Gajiya tai da tambayoyin addar tata ta haye doguwar kujerar dake dakin ta kwanta tana juya mata baya.
"Yesmin ba dake nake ba"
Cikin kosawa tace"yaya muhseen yazo dazun ya kawo maki wasu kaya suna wajen mama"
Dogon tsaki taja tace"ba shi na tambayeki ba ai,ina ruwana da kayan daya kawo tambayarsa nai ina son wasu kaya?ko zindir yaga ina yawo,yama dawo ya anshi abunsa don bana so maye kurin ana turesa yana kawo kasan wlh zaigane wanda yayi ma shishshigi ni banson maita,nace banayi ko dolene"
Jiyuwa yasmin tai fuskarta babu fara,a ko walwala kamar zatai kuka tace"Adda kibar zaginsa babu kyau kana aibata wanda yake sonka"
Kallonta take tana mamakinta lallai yesmin tayi nisa sosai,don ta sake tunxurata tace"anje anzageshin idan yaji haushi yace yafasa,ina ruwanki ma da zagin sa danake da aibatashin banson shishshigi kinajina,angaya mashi zai siyeni da abun duniya ne wofi dashi kurin."
Idonta cike da kwallah cikin sanyin murya tace"Adda tunda bakison sa kibarshi da haka amman kibar aibatashi banajin dadi wlh don Allah"
Ta fada tana jiyawa tana goge kwallarta.
Mamakinta kashe fiyah yayi tace"yesmin mekike cewa,sake maimaita wa don Allah in tabbatar ma raina."
Kukanta ta jiyo kasa kasa tama rasa me zatai saidai murmushi ya kubce mata,Allah sarki yar salihar qanwarta ta shigo layin manya.indai sone abunda yafi kuka ma yi mashi zakiyi.
Kaya ta cire ta shige wanka tana jin dadin yadda ta tabbatar da abunda take zargi kan yesmin din.
Wanka tai da Alwallah tayi salla sannan tazo tahau shiryawa,riga da siket ne ta saka ta yi simple make up tasaka turare tafito tsakar gida.
Mama ke shara ta ansa tana yi mata suna dan taba hira,
"Babanku tunda kafa tafara takuwa yafice agidan nan,kinganshi har yanzu bai dawo ba"
"Ai haka akeso mama inkinga mutun zaune kamar baba to ba lafiya ba,Allah ya kara mashi lafiya.wai mama yaya jalal lafiya baizo ba"
"Yayanku wata yar matsala ce ta faru can wajen aikin,mataimakin principal yayiwa wata yarinya fyade,to matsalarce aketa fama da ita shiyasa yace said satin sama"
"Innalillahi fyade vice principal da kanshi,Allah ya kyauta gaba to"
Mama tace"ameen iyakarta kenan"
Shiru fiyah tai tana nazarin maganar da zata yiwa maman.
"Kamar kina da magana dani ko safiyya?"
Murmushi tayi tace"mama ai yadda zaki fahimceni nake tunani"
"Karki damu ni uwace koma menene zan fahimcenki zan kuma dauki hanyar da zata daidaita matsalar."
"Na gode mama,dama akan muhseen ne"

********
Chapter 61 · 0% Book details