← Book details Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 87

Sashe 29

Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

DA yake babu aiki daya wa ta gama duk abunda zatayi har sanwar rana ta gama ta koma daki ta dauko handout dinta tafara karatu don tasan exams is around the corner.
Ta jima tana karatun kuma cikin yardar Alkah da kuma jajircewa da takeyi duk abunda take karatun yana zama,wani kuma dan dubawa zatai tariga ta rike bayanin sa tun cikin class.
Ana kiran la,asar ta ajiye tayi alwallah tayi sallar sanna tafoto ta tambayi antyn idan akwai abunda za,ai tace mata"babu komi gaskiya amman fa inason kidan hadama Muhseen don wani abu zuwa anjima zaizo ko bakuyi waya yace maki yazo ba."
Wani irin faduwar gaba taji ta sameta rasss ita yau ita tashiga ukunta ,wai wanna kaddarerren mutumin bazai shafa mata lafiya ba,wlh ita fa bata son sa.
Yak'e tayi tace" kai anty nafa sani Amman bai gaya mun time din da zai zoba gashi xanje yanzu makaramta xan anso hand out don exam tataho zuwa next week insha Allah."
"Yace sai dare inhar bazaki dade ba ai har kinje kidawo"
A haka suka rabu tafice don inba haka tayi mata ba balbalin masofarta ma sai ya hana fitar.

Mrs bbce.
Mom muhseen
[9/17, 3:37 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

🅿️.........25

Tana fitowa sukai cibis da yaya Jalal shida wani abokinsa sunxo ganin baby,wani duka kirjinta yayi don wlh yana iya hanata fitan ma gabaki daya.
Kallonta yake Sama da kasa cike tuhuma,ita Kau banda yak'e babu abunda take,ta gaida abokin nashi ya na tambayarta baby tana ansa mashi cikin kulawa.
"Yaya ashe zakazo nai zaton yar taka ma bazaka zo ganinta ba."
"Ina zaki haka da yamma?"
Bazata banbanta karyar da tayi ma Anty da wadda zatayi ma shi ba ana iya samun Matsala,."yaya na gaya ma Anty zanje makaranta kasan exams tataho shine Zan anso handout in fara karatu."
"Salan kikai dare,naga take takenki kafafunki sunfara sanin gari kin iya yawo."
"Bazan Kai dareba yaya Amman don Allah kakara man kudin taxi wlh basu isata wannan."
Kafinma yafiddo abokin yaciro Dari biyar yabata,godiya tayi mashi sosai sannan suka shige.
Wucewa tayi itama tana murmushi itadai ai hankalinta ya kwanta tunda tayi nasarar ficewa,text din data turo mata babujima ta shiga dubawa.
_ina nan magic land,inkinzo ki kirani saina zo na shigo dake._

Dandanan ta tari taxi ta gaya ma shi inda zai Kai ta,jingina tayi da kujerar da take tana tunanin hikimar daxatayi Mata anfani da ita wajen shawokanta harta gaya mata abunda take bukata,Amman muddin taji gaskiyace zatafada bawai karyaba dole zata kunna recording,don shine abumafi sauki damutun zaiji yayarda dakai,Yakuma yi amanna da cewar wancen bashida laifin komi sharrine na mahassada.
Duk da cewar abunda take shirin fadan tanajin faduwar gaba kuma tana tsoron faruwar wani abu,Amman dolene tayi hakan don shine hanya mafi sauki data dace tatunkari zakiyyar.

Amman harga Allah tana tsoron wani abu guda dayake mata yawo cikin kai,wata xuciyarce takegaya Mata "inaruwanki safiyyah,kedai ba burinki gaskiya tafito ba to inaruwanki da duk abunda zaifaru tsakaninsu."
Ajiyar xuciya tayi tana jin wani zuka cikin kirjinta,duk da haka dai batason hakan ta kasance.
Har bakin Kofar shiga wajen ya sauketa ta salameshi ta fito,
Kiranta tayi awaya saigata ta fito,wannan ne karon farko da tahadu da ita.....gabanta taji yafadi ganin zakiyyar kyakkyawar gaske duguwa Mai dirarren jiki,gaskiya dole Alfah take rikicewa akanta,aman tana tantamar idan gaskIya tafito tabbas wannan tsuhuwar soyayyar zata iya tashi.
Wani lugude taji kirjinta yayi Mata saitaji haka kurin tana tausayin kanta,murmushi shimfide akan fuskar zakiya Wanda ya sake bayyana ainahin ruwan kyanta,Amman kuma azahiri safiyya tacewa zakiyya kauban wuri Amman saboda wani abudake ranta yasa ta kasa tantance itada zakiyyar waye yafi wani.
"Assalamu alaikum."
Zakiya tafada tana mikawa fiyah hannu.
Cikin rashin kwarin jiki ta na mata yake ta mika mata nata hannun tace"Wa,alaiki salaam,zakiyya muazzam ko?"
Cikin Fara,a tace"haka yake sunan,muje ciki to nima har kinsanar dani naki."
Jerawa sukai suna tafiya hakanan zakiyya taji fiyah ta kwanta mata arai,Ku ma ta yardarma ranta bazata cucetaba.
"Ai tun ranar dana kiraki nafada maki sunana kindai manta ne"
Cewar fiyah dake kusada ita tana kallon wajen gwanin burgewa.
"Ohhh anyi haka,Amman wlh na manta kasancewar abubuwa sunmun yawa."
Fiyah tayi murmushi tace"haba aiba komi kasancewar ki amarya aianama amare uziri hidima ce tayi masu yawa."
Dandanan fuskar zakiyya ta canza,yanayinta ya canza sosai harta kasa cewa fiyah komi akai.
Tun anan fiyah taharbo jirgin,zarginta ya tabbata cewar zakiya bata son auren Alh kwangila,to meyasa zata auresa.?
Chapter 29 · 0% Book details