← Book details Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 87

Sashe 47

Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Duk suna zaune baban shima ya jingina da filo ya gama cin abinci,suna dan hira da juna har uncle yahya yazo da Anty jamila,basu jima da tafita ba ma.
Bude kofar akai aka shigo duk suka juya don ganin ko su waye,zaro idonta Safiyya tayi tana zubasu akansu,meya kawo su nan na shiga ukuna ni safiyyah.
Gaida su mama sukai sanan sukayi ma baba ya jiki da adduar fatan samun sauki,kallonsu nake ta gefen ido ban so wani cikinsu ya anbaci sunana.
Mama "tace samari daga ina bamu ganeku ba"
Malik yayi murmushi yana shafa kanshi yace"mama daga wajen duba Abbi muke shine yace mushigo nan ma muga baban su fiyah shima abun ya shafeshi,Allah ya kyauta gaba ya rufa asiri."
Jinjina kai mama tai tace "Ameen mun gode sosai,Allah yasaka da alkairi"
Yace "Ameen bari mutai Allah yakara afuwa."
Yana kallon fiyah suka juya suka fita,zakiyya na bin bayan sa
"Yaya malik injin tsoron yan gidanmu su ganni nan wajen komi zai iya faruwa wlh,zasu cigaba da bibiyata har sugane inda nake sukasheni,wanan abun daya samu Abbi wlh shine shirin da su umma suke shiryawa,kuma nadaukeshi cikin m.card dinan yanzu idan kace mashi umma ce tayi wannan abun wlh yaya malik bazai taba yarda ba,shiyasa nakeson kakunna ma Dadday yaji da kunnensa,sannan shiyasan yadda zaije yi da Abbin har yasan komi,don haka kamai dani gida akwai hadari zamana anan."
Ajiyar xuciya ya sauke yace"hakane zakiyya,tunda kinga ma bai saurareni ba alamun dai har yau yana kan bakanshi."
"Hakane yana kan bakanshi anma cikin xuciyarsa yana jin wani feeling din wani abu,nayi imanin Abbi yana kewar yaya Abdoul,yakasa yardar ma kanshi abunda yake tunani,saboda asirin dake cinsa umma bata bar Abbi haka ba,wlh wajen boka zata kai sunan sa aimata aiki kanshi.kasan yadda Abbi yake da zafin rai da bin kwakwakwafi wlh da tuni yagano ta,amman saboda abunda tayi mashi baya jin maganar kowa sai tata,baida wasu y'ay'a dasuka wuce su zuwairat,sune yake jidasu ya mance da mami ya manta da ni,ima to balle wani Abdoul."
Numfashi ya fesar yana cewa"zanje na ga daddyn da daddare idan Allah ya kaimu,komi kenan zuwa gobe fiyah zata fito exams saimu hadu can gidan dadyn,yanzu mukoma gida"
Fita sukai daga asibitin suna shiga mota motar yan gidan ta tsaya,umma ce da dasu haulat da Amina.sai zuwairat din da khadija suduka dai yan dakin,sai mamman shine ya kawosu.fuskarsu babu alamun jimami ko tashin hankali,illa khadija daketa kuka haik'an har suka shige suna binsu da kallo,sannan malik ya tada motar ya fita daga cikin asibitin.

Tunda suka fita gidan hanklinsa baya kwance ya kasa zama koda na minty gudane,duk ya firgice ya fita natsuwarsa.
Duk yadda yaso cire dauwar abun ya kasa,wani irin kewa da tausayin Abbin nasa yakeji,ga kuma tausayin fiyah da ya gama kewaye gabaki daya jikinsa da xuciyarsa,kota wane hali yanxu?koya jikin baban nata Allah yasa bai tsanata ba,Allah yasa bata kuka duk jikinsa ya rikice zaman dirshen yayi kasa falon yana dafe dakansa,da zai iya zuwa da yaje yagansu kozai samu sukuni,tunda ya baro gidansu yauce rana ta farko dayakeji. Tsananin son ganin mahaifiyarsa da mahaifinsa,Allah sarki mami koya takeJi koya takejin kewarshi,wane irin kunci take ciki.jiyai wasu zafafan kwalla sun xubo mashi,yayi alkawarin duk wanda yayi silar jefasu cikin wannan kuncin da bakin cikin na shekaru shidda,shikuma yayi mashi alakwarin kare rayuwarsa agidan kaso,batare da hutawa ba kota dakika guda.
Tashi yayi kamar antsikare shizai dauki makullin mota yaje yanemi asibitin yaga wane hali suke,yadda yakejin zuciyarsa da kirjinsa bazai iya jure rashin sanin wane yanayi suke ba,safiyya ta tsaya mashi garai yanzu haka tana can tana kuka har kanta yayi ciwo,kanshi ya sara,wasu zan tika suna mashi yawo cikin kai,har yakejin kan nashi yana sarawa.

_kadauka cewa banda wani da acikin gidan nan mai kama dakai,babuni babu kai,ko ahanya kar kasake inga bakar fuskarka,na fiddaka daga cikin xuriata namance da na haifi da namiji,dana san zan haifeka Abdoul da ban auri uwarka ba,Allah ya isa tsakanina dakai.............._

Xubewa yai kasa numfashinsa yana sama da kasa alamun dai zai dauke..........idanunsa sun kakkafe,dandanan ya rarumo jarkar ruwan sanyi dake saman wani table ya kafa ga bakinsa,yaringa kwankwada ya mance da dokar likitansa na hanashi shan ruwan sanyi.zafi da kirjinsa yake mashi yasa ya ma mance dawata doka,kamar jira ruwan yake ya shiga cikinsa wani murdedden ciwon ciki ya mashi wata irin damk'a babu jinkirtawa ya fadi kasa sumamme.

"Mama kibar wani tantama babu yadda Allah baiyyi da bawansa,kilan lokacine Allah ya kawo da zasu shirya ko baba"
Murmushi yayi yace"uwata waye yace maki daman waye yace dake muna fada"
Dariya tayi tace"baba ai bama ni ba,duk wanda yasanmu cikin wannan unguwar yasan cewa basu sonmu,shine mutun nafarko daya fara kyamatarmu,nafa sani baba don haka kilan wannan abun da kai mashi shine silar daidaitawar ku,kuma nima zanji dadi don banson inga ana gaba wlh"
Mama tace"dadin ubanwa,bacin duk cin kashin da yamana ai taimakon da yayi mashi badon ya samu hanyar shiga jikinsa bane,kokuma su sasanta don yaringa taimakonmu,Allah ne yasa ma babanku xuciyar tausayi,kuma yaga yana da halin taimakon nashi shiyasa yayi,don haka ni bazan lamunci wata hidimarsu ba,wannan ma da sukai mungode "
Dalha da baba na darita yesmin na taya su.
Fiyah tace"baba kaji abunda mama tace ko,to wlh karka biye ta tata inhar yazo ya nemi sasanci wlh karka wani dauki maganar mama ku shirya ai Allah yasani babu kyau riko"
"Iyye!don gidan ku ninake rikon kenan,?zaki rufe mana baki anan ko saina makeki,marar zuciya to ni bazan lamunta ba,azauna hakan yafi da aga rana guda ya shishshige mana ace son abun duniya ne ya kaimu"
Nan dai kowa yaita fadar ra,ayinsa akan lamarin baban najinsu baice masu komi ba banda dariya da murmushi da yake.
Wajen karfe shidda da rabi mama ta cewa sutashi sutai gida ayo sanwa akawo masu,aka shigo masu da wasu manyan kuloli,wajen guda hudu.wadda ta shigo da kayan safiyya take ta kallonta,tabbas wannan koba afada ba tasan jinin Abdoul ce babu mamaki ma itace ni,imah don komi na fusmar ta irin tashice,saidai kace shi na mijine ita macece.
Gaidasu tai tana durkusawa tana ma baba sannu da jiki.
Tace"mamina tace akawo nan tana gaida maijikin xata shigo"
Mama tace"mungode amman ki mayar kice angode muma muna da namu........babane ya katseta da cewa"Aa ajiye yarinya kinjiko kice mun gode kigaida baban naki da jiki"
Tace to ta juya ta fita tsunbul fiyah tayi tabita abaya mama na kiranta bata saurareta ba,

"Ni,imah" fiya ta kirata juyowa tai tana kallon fiyar harta karaso inda take kallon juna sukai ni,ima tana mata kallon sani itakuma tana mata kallon tausayawa.
"Kamar na taba ganinki unguwarmu"
Cewar ni,imah murmushi fiyah tayi itama sai yanxun ta tuna sun taba haduwa,har suka gaisa ni,imah ce ta fito daga gida zata fita,ta yarda wata takadda to daidai fitowar fiyah daga gida kenan ta ganta,taje ta dauketa,tana sauri harta isketa tabata suka gaisa tana mata godiya.

"Daman baban kune ya ceci Abbi,Allah sarki Allah yasaka mashi da Alkairi mungode sosai."
Ta fada idonta yana ciwowa da kwallah.
Riko hannunta fiyah tai suka zauna saman wani dogon table tace"kuka kike ni,ima meyafaru?"
Share kwalar tayi tace"bacin babanku shima Abbyn da kila mun rasashi,kamar yadda tsawon shekaru kuma rasa yaya.........kukanta yakara karfi dakaji kuka kasan maiyinsa yana cikin halin kunci da damuwa.
Tausayin ta yasa fiyah jin kwalla sun cika mata ido,yanzu umma ina zata da wannan hakkin,lallai mutane suna kusanta kansu da jahannama,kadauki hakkin wani saboda son xuciya da son abun duniya,wai ko suna mancewa da cewar duniyar karewa zatai oho.
"Kibar kuka kinjiko,insha Allah shima yaya Abdoul din zai dawo kinjiko,ina mamin take"
Tana share hawayenta tace"tana can gida bata zo ba,tadaice inkawo maku abinci"
Shiru fiyah tai tana bukatar ganin mamin donta kwantar mata da hankali,don tabbas yadda ni,ima take cikin kunci da damuwa tasan mamin ta fita sau dubu.sun bata tausayi ta dafa kadarta tace"Allah yana sane daku qanwata,insha Allah komi ya kusa daidaita kicigaba dayiwa Abbinki da yayanki Addua Allah ya karesu daga sharrin mahassada da makiya,insha Allah za kaiki wajen yayanki amman kiyimun alkawarin zaki daina kuka kuma zaki sanar da mami itama,amman daga ita bance kigaya ma kowa ba,ita don tasamu natsuwa ki kwantar mata da hankali kice yaya Abdoul dinta yana nan cikin koshin lafiya,shima kuma kullum yana cikin kewarku."
Mamaki da al,ajabin abinda fiyah kefada yasa ni,imah sakin baki tana kallonta da mamaki.
Cikin doki da murna ta rungume fiyah tana cewa"na gode Antyna ngd Allah ya biyaku don Allah inzo yanzu muje"
Murmushi fiyah tai tace"Aa ba yauba kiban no dinki idan na shirya zan kiraki gobe sai kizo muje karfa kigaya ma kowa"
"Bazan sanar da kowa ba sai mamina nhd Antyna,bari intai driver yana jirana"
Tatashi tatafi daka kalli fuskarta kasan tana cikin farin ciki.
Juyowar da zatai don komawa dakin da aka kwantar da baban taga mama da yesmin tsaye bayansu.
Iayakar rudewa tarude har saida hakan yabayyana ga fuskarta.

"Mama kune........

Kuyi maleji plssss
[9/17, 3:42 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

🅿️.........38
Chapter 47 · 0% Book details