← Book details Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 87

Sashe 64

Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk hirar da suke akan kunnen fiyah da yesmin wadanda basuyi bacci ba kowa da abunda yake damunsa,yesmin batasan Addarta batai bacci ba amman fiyah tasan yesmin idonta biyu.
Tun bayan data gama kukanta a toilet ta fito ta kwanta tana dana tasanin abunda ta gaya ma Abdul dinta.
Amman wani shashe na xuciyarta yana gaya mata gara ta ja ajinta gara ta nuna mashi ita din mai ajice hakan zaisake jansa ga kaunarta.don sun ganin su sunda abunda dole ma yarinya ta kware masu,wanda hakan yakeja wasu matan suna rasa darajarsu wajen maza saboda tun awaje kin xubar da kimarki........har ga Ko son Abdoul zai kashera baxata iya kallan idonsa tace tana sonsa ba,haba ina kunyarta take ai mama ma saita kusan dukanta saboda fada.haka taraba dare tana sakawa tana kwancewa,adduarta guda kada Allah yasa xuciyarsa tayi na,am da auren zakiyya domin tanajin tafafi zakiyya jin kishinsa axuciyarta,jitake muddin haka tafaru duk wani jindadinta yakau adoran duniya,kawai dai ita tana iya control din nata ne tana iya danneshi alokacin dayake sata abunda ba daidai ba......ta furta ya aureta ne don bata da wara mafita,don kuma zakiyyar ta dace dahaka tayi sadaukar da rayuwarta ne dominsa,bai dace ya wofintar da ita ba.ajiyar xuciya taja sosai har yesmin ta jiyo tace"Adda baki bacci ba kema"
Tama manta da yesmin wlh "aa nafarka ne keme ya hanaki bacci"
Kamar zatai kuka tace"Wlh Adda xuciyata wani iri take mun nakasa baccin tunani ya isan ni bansaba haka ba abun sai yake mun wahala"
Tausayi tabata don tabbas fadawa kogin kauna wadda ba,asan kanayi ba wahalane da ita,ba kowane zai iya jurewa ba sai mai tsananin hakuri da kauda kai,abune da kecin xuciya da ruhi abune dake taba dukkanin lafiyar jiki data kwalwa da xuciya ajiyar xuciya tayi tace mata"kije kiyi alwallah kizo ko raka,a biyu kiyi kidan karanta qur,ani ko sura biyuce zaki samu bacci mai dadi"
Babu musu tatashi ta shige toilet din,dafe goshi tai tana adduar Allah yasa kar so ya wahalar da yar qanwarta.
Komawa tai ta kwanta tana dasa tunanin nata,tabbas ayadda abdoul yafusata bata jin zaisake dawowa haka zalika zai nemeta,kuma zuciyarta tana raya mata abunda bata son,wani zafi taji ga kirjinta ahankali ta furta "bazan iya sharing dinka da kowa ba Yaya *NASSER* duk yadda xuciya ta kwallafa rai dakai dole xata barka,kishinka araina mai girmane bazai barni nazauna lafiya ba"
Saitaji kwallarta tana silalowa saitaji tana sakawa ranta hakuri dashi tun yanxu,tabbas tanajin ajikinta Abdoul zai dauki maganarta zaije ya daidaita da zakiyya,zai aikata abunda ta fada ba shakka hakan zata iya faruwa.......danasani ya shigeta yafi sau dubu na fadar abunda ta fada karshe dai wannan daren ya dade bai karema ta ba tana gani yesmin tayi baccinta hankali kwance itako saidai juyi,asubar fari baccin ya sureta tare da mafarkin *(ABIN CIKIN RUHINATA)*

motar Abdoul na fita ta su dady ta shigo cikin unguwar bin sa da kallo Abbi yayi yana cewa"Abdullahi motar Alfah ce naga tafita wlh shine Allah yasa gida yaxo Allah na rokeka Allah yasa hakane"
Murmushi dady yayi yace"Adduarka ba haka take ba,zance yaje. ga dukkan alamu kuma anbata ransa"
Hankalin Abbi atashe kamar zai kuka.
"Wlh tsakanina da mariya Allah ya isa Allah kadaukar mun mataki akan matarnan,ta cutar dani tana kan cutar da rayuwata data iyalina,mekake tunanin yafaru dashi Abdullahi"

"Kodai baisamu abunda yaje nema ba,kokuma mahaifinta ya ganshi ya dakatar dashi cikin daya biyu kokima duka"
Abbi muryarsa tana rawa yake cewa"duk duniya bayan iyayena damuka rasa banda abunso sama da Abdoulnasser,kuma saboda farin cikinsa babu abunda baxan iya ba,har kwamciya ina iyayi kasa malam kabir yabi ta kaina inhar zaibashi farin cikin dayake nema,inhar zai mallaka mashi yarinyar nanan,don naga kamar son ta yake kamar rayuwarsa"
Dady yace"rayuwar tasama bai adauketa da muhimmanci ba kamar safiyyah,shi kanshi baisan soyayyarta taimashi mugun kamu ba sai nan gaba tukun."

Har cikin compound din gidan yakai Abbi sojojin dake tsaron gidan wani yazo ya bude mashi kofa yana sara mashi,bama tashi yake ba.
Koke koke keta fitowa daga bangaren umma,cikin kuluwa yake tambayar sojan dasuke kula da bamgaren magana.
"Ubamme yafaru acan wajen suke wa mutane ihu"
Cikeda mamaki sojan daya kame don yasan baida magana mai dadi saita su umma,kullum daya zo zaice suna lafiya babu wani abu dai ko,amman yau sai yaji sabanin hakan.
Cikeda bala,i Abbi yace"dakai nake shege ka tsaya kana kallona"
Jikinsa yana bari yace"yallabai madam ce........itace......daman......dama......"dakai nake kana mun ina ina zan ci ubanka wallahi"
abbi ya daka mai uwar tsawa saida ya daskare,yana nuna part din yana cewa"itace ta......ta hauk.....ace......ta yayyaga kayanta tana iface iface,tayiwa haulat dukan tsiya har cikinta yaxube,yanzu haka zuwairat na wajenta ca asibitin,ta jiwa khadija rauni ga kai saida aka daureta aka rufeta adaki sannan,amman taki shiru itace keta wancen ihun,ankiraka yafi sau ba iyaka yallabai naka dauki waya ba kagafarcemu"
Murmushi yaga Abbi yanayi cikeda jin dadi yace"daddaden labari kana da kyauta ta dubu dari,ka tuna man da safe ban kuma ce uban kowa yashiga ba kunajina ya fada yana nuna sauran security din dake wajen.
Dady yace"karkayi haka yaya..........Abdoullahi idan baka son raina yabaci kaimun shiru kama hanya kuma ka nufi gidanka iyalin ka najiranka"
Ya wuce part din su Mami yanajin wata matsananciyar kewarsu ita da ni,ima.har tun tube yakw ya shiga jikinsa har wata tsuma yake,falon shiru sai karar Ac kallon falon yayi furniture's duk sun lalace,gabaki daya ma part din ya Lalace babu kulawa bawai rashin tsafta ba,aa komi ya lalace yana bukatar canji,wasu kwalla suka xubo mashi.
Sako da lungu na part din yake dubawa yana hawaye.
Motsi yaji kitchen ya leka mami ce keta kokarin sarrafa yar cus cus din data rage masu rabin leda tayi ma dady waya basuda abinci yace sai xuwa gobe.
Julluf tayi ta juye ga plet zata bar kitchen din don ni,ima ce keta amai bata lafiya dataci abu saita amayar dashi,mafarin ta yimata ita.
Juyowar da zatai taganshi tsaye bayanta yana goge kwallarsa,saboda tsorata sakin plet din tai kasa tana ja baya,don bazata iya tuna rabon data ganshi ba.......tsora ya kamata tuni hawaye sun wanke idon ta.

*_ABDOUL-NASSER_*

Ya na isa gida dakin zakiyya yayiwa tsinke................

*naga adduoin ku ina godiya sosai Sannan ina rokon Alfamar ku cigaba da man uxiri saboda yanayin jikina,ngd da nuna kauna*
[9/30, 3:43 PM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSEER*
*(ALFAH)*

WRITTEN BY

MRS BB
MOM MUHSEEN

FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970

🅿️..........53

Saida yashiga falon yaga baidace yashigo mata acikin yanayin dayake ciki ba,frig dinta ya bude ya dauko ruwa har zaikai bakinsa yatuna da dokarsa,saurin dakatawa maimakon yasha saiya fito waje da robar ya tuttulewa kanshi ruwan har xuwa ga fuskarsa,yana sauke ajiyar xuciya sanyin yana ratsa xuciyarsa yana sauke mashi duk wani zafi daya debo.
Jingina bayansa yayi da bango yana yin relax,saida ya kwashe minty biyar ahaka sannan ya samu sauki ya najin duk wasu makamai dake cunkushe cikin ransa suna sauka,duk da ba duka ba.
Har yanxu kunnensa yana sake jiyo mashi munanan kalamanta,wannan ya nuna cewar hasashensa akanta duk gaibune,yana tunanin yadda yakejin masifar kaunarta cikin ransa yazaji itama haka,koma fiye dahaka ashe haukan banza yake.yana bukatarta cikin rayuwarsa da zai dora agaba idan Allah yabashi iko,yana ma yaransa tanajin uwa da tagari da zata dorasi bisa daidai.yana mafarkin zamun hasken acikin rayuwarsa agaba,amman duk wani burinsa da fatansa ta rusa mashi su.
Saiwani nanata mashi maganar auren zakiyya take,ina ruwanta da aurenta da rashin auren ta dazai,amman yanaga wannan ce kurin damar shi.yadda ta nuna bata yi dashi duk maitarshi shima ya kamata yadaga mata kafa hakanan,karon farko yaji xuciyarsa ta raya mashi daidaitonshi da xakiyya,har xuwa sanda zai yanke shawarar data dace dashi.
Bedroom dinsa ya nufa kurin ya fada toilet ya saki ruwa ya jima yana sauka jikinsa yafito da Alwallah yayi sallar isha,i sannan ya canza kaya yaje ya hado tea marar zafi sosai,yana sha ya gama ya duba system dinsa sakonnin costomers masu son ganawa dashi,yayi accepting wasu wasu kuma yayi reject.
Haka yayita aikin da zai dauke mashi hankali daga tunaninta da bacin ranta,har dare ya tsala ya ajiye ta kwanta daker da sidin goshi baccin yayi nasarar daukarshi.

Muryarta cikin kuka kukanda duk wanda yaji saiyaji kamar ya tayata,tundaga kasan xuciyarta kukan yake tahowa,numfashinta har sama da kasa yake maganar ma bata fita sosai,don muryar ta dishe saboda kuka.
Yana rungume da ita cikin kirjinsa yana tayata kwallar shima,don shima kukan kurin zaiyi yaji ya samu saukin xucoyarsa.
"Na gode ma Allah da wannan jarabtar domin na yi imani dashi,hakan yana cikin kaddarar rayuwarmu nida yarana,kuma bazan butulce mashi ba zan gode mashi da har ya waiwayo maka da hankalinka akanmu.hakika wannan hukuncin sa ne ba na kowa ba.sai kuma sila da dalili,banda kamar wannan yarinya aduniyata hakika Allah zai mata kyakkyawan sakamako aduniya da kuma lahira,malam kabir daka tsana arayuwarka shine dalilin dayasa kake raye ahalin yanxu,haka diyarsa safiyya itace dalilin dayasa muka tsinci kanmu cikin wannan halin na farin cikin daidaituwar komi,idan baka nemi yafiyarsa ba Allah saiya tambayeka matayinsa na makocinka mai hakki akanka,amman kasa kowa ya tsanesa bada wata hujja ba Abbin ni,ima kadawo cikin hayyacinka idan baka gina lahirarka ayanxu ba yashe zaka ginata,kana da tabbacin kana da kwana ki dayawa arayuwarka..........rufe mata baki yayi yana kwalla harda shashsheka yace"insha Allah nai alkawarin gyara kura kuraina mamin ni,ima nai alkawarin dawowa mutumen da al,umma zasuyi alfahari dani kuma zan dage da neman tsari daga shaidan da makarrabansa,domin hada rashin kiyaye azkar yasa koma me mariya tayi mun ya sameni.amman na dauki hakan matsayin darasi da kuma hanyar gyarace Allah ya nuna man,hakika zan gyara alakata da malam kabir inhar yaban dama xuria zan hada dashi."
Jawota yayi suka zauna kan kujera yana rike da hannunta,yasoma bata labarin duk abunda ya sani ayau dinnan,kuka ta kamayi tana fadawa jikinsa yana sake godema Allah daya kawo silar fitarsu cikin wannan kangin.
Wannan dare haka Abbi ya rungume mami da ni ima ajikinsa har garin Allah ya waye.

*********
Chapter 64 · 0% Book details