Sashe 28
Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tunda suka shigo ya wuce ya watsa ruwa sanan yyi sallar magrub a cikin dakinsa yunwa yakeji da gajiya baison yin magana kwata kwata yanzu,soyake ya kwanta yana bukatar tunani.
Yasan malik inzai shigo zai taho masu da abinci tunda kukun nasu baya nan.
Kasa ya kwanta yana filo da hannayensa idonsa rufe kafafunsa ya dora su bisa wani dan table,yayi crossing dinsu yana girgiza guda.
_haka kawai kasa mun wannan qazamin bakin naka mai shan giya gashinan ji nake kamar zanyi amai wlh.kaida Allah ban yafe ba_
Murmushi ya subuce masa mai shegen kyau,har fararen hakoransa kyawawa suka bayyana.
Kafin Annurinsa ya fara b'acewa saboda kalamanta na farko.
_ur highly welcome drinker guy_
Runtse idonsa yayi yana jin zafin kalamin cikin ransa,tabbas yasan ankirasa da wadanda sukafi wadanna ada bama da ba har yau akwai masu yi mashi wannan kallo,amman zuwa sadda ya rikice ya daina jin zafi da dacin kalaman shine lokacin da ya kulla damarar shanta.daga lokacin baya jin haushi baya jin radadi don ance masa mashayi.........ammman yanzu da yaji din rad'in kansa ya barta bari na har abada,sai yaji kalaman basu dace dashi ba,Allah shike ganin zukatan bayin sa amman yasan badan wannan yarinyar yabar giya ba,saidai yasan cewa kalamanta suntaka rawar gani wajen taimaka barinsa da ita,don tunda yaje Australia daya shata ma sai yayi amai kuma sai yayi masassara,lokacin ya dan gana da asibiti don radin kansa wanda shi knsa yayi mamakin ganinsa gaban likita wai ya kawo kansa,bacin kullum hanyar da zata lahanta rayuwar yake nema.
Amman baisan meyasa yanzu yakejin yashirya yin rayuwa mai kyau koda shokadaine cikin duniya,yaji haushin kansa lokacin da dr yohana yake gaya masa cewar wine din takai limit din da bata kara iya daukar hunhunsa,saboda ta mashi rauni a wajen wanda muddin ya sake yasha ta ko yasha lemo mai gas yana iya rasa ransa,haka zalika ya hana shi shan abu mai zafi sosai da kuma mai sanyi sosai,don zasuyi mashi lahani........sannan abun daya sake bashi mamaki da haushin kansa wai arne da baisan kansa ba wanda bai yarda da Allah da manzon sa ba yake mashi nasihar zaman duniya,da kuma abunda zaiyyi maikyau da marar kyau.
Ranar yayi kukan da tunda yabar gidan iyayensa baiyyishi ba,yayi nadama da dana sani yafi akirga,saida ya kwana biyu baifita ma aikin daya kawoshi ba.
Mafarin ya fara ansar magani daga shi dr yohanan yace masa duk bayan wata uku yazo aduba shi don zai iya yuwiwa amai aiki,idan kuma yana warkewa to basai anyi aikin ba......duk sanda ya tuna wannan lamarin saiyaji kansa yana sarawa,hakika yayi sake yabari shaidan da sherin zuciya sunyi galaba akansa.meyasa abunda ake masa kallo dashi bayyi yunkurin kiyaye kanshi dashi ba,yanzu kenan da Allah bai sa ya bar sauran shaye shayen dayayi ba Allah kadai yasan abunda zai faru da rayuwarsa.da mezaice ma mahaliccinsa baida bakin da zai iya kare kansa.
Hawaye suka silalo mashi yaji wata kaunar malik ta cika mashi zuciya,tabbas malik abokine na musanman duk wanda yasamu aboki amini irinsa yadace yayi dacen da har tutiya ma inyayi babu laifi.
Don yasan irin wuyar dayasha kafin ya rabashi da sauran kayan mayen.sannan binciken dayasa akai mashi ya nuna mashi cewar shine ya kawo wannan yarinyar cikin rayuwarsa,don ta taimakeshi yadawo dashi daidai..........meyakai wannan arayuwa inda wanine fita sabgarsa zaiyi yaje koma me zayyi yayi aiba dan uwansa bane ko wami nashi.........wannan dalilin yasa yaji zuciyarsa tayi sanyi tayi cool dinda baisan rabonsa dajin haka ba,yaji natsuwarsa na dawowa yaji happenes dinsa cikin kaso dari kashi arba,in yana dawo wa jikinsa da ruhinsa.dalikin kenan yasa ya nuna masu canjin da suke ta fafatukar nema shida wannan yarinyar da baisan sunan taba har yau.
Kuma yyi kudurin basu goyon baya har sadda zai idasa dawowa normal,insha Allah bazai sake daga hannu da sunan duka gareta ba,don tana yin komene don yaji haushi yabar abunda yake,kuma sunyi nasara kuma suna kan yin nasara.
Amman alwashin sa guda daya dauka shine koda gaskiya ta bayyana tsakaninsa da iyauensa bazai sake komawa cikin zuriarsa ba,don kozai manta komi bazai iya manta wa da irin tozarcin da yafaru dashi ba shekara ta shidda kenan.
Sun bata mashi suna ga duk mutanen dake masankallon nagari kuma natsatstse,tome ma zaije yayi masu baida zuciya kenan.........."Abdoul!!!"
Muryar malik ce ta dawo dashi daga hayyacinsa,goge fuskarsa yayi dake ta hawaye,mamaki tsantsa ya kama malik tunda suka farazaman kansu cikin wannan gidan baitab'a ganin hawaye afuskar saba sai yau.kallonsa yake sosai yana idasa shigowa cikin dakin ya zauna yana ajiye takeaway din daya shigo dashi.
Alfah tashi yayi zaune yana tankwashe kafafunsa irin zaman nan nacin tuwo,bai kalli malik ba ledar yajawo yana budewa don yunwa yakeji sosai.
Bai kallesa ba yace"i need water pls."
Tashi yayi yaje yadauko mashi cikin firg dinsa dake cikin dakin.
"No pls bani marar sanyi in akwai."
Kallonsa kawai yake yace"Kaoda baka shan ruwa marar sanyi."
Hanunsa yasa yana shafa fuskarsa zuwa gashin sajensa konace kasumbarsa data kwanta tayi lub yace"yanzu kuma inso."
Komawa malik yayi yadau ko mashi ya dawo ya tusa si yana son tamayarsa kukansa amman yasa ba zaishi ba shi ansa ba.
Ruwa yasha kadan sanan yafara cin kazar dae ciki don bai iya cin shinkafar zata saka cikinsa nauyi,gashi yakwana wajen biyar bai motsa jikiba duk ba yajin dadin jikin.
Saida ya cinye kazar an tas ya idasa shanye ruwan yana adduar gama cin abinci kasa kasa.
*Alhamdulillahil lazi ad'a amana wasa qana waja alana muslimin.*
Duk yada yayita ciki ciki hakan bai hanaa malik yaji ba.
Shidai yau Alfah duk ya zamar mashi wani daban,Alfah da baison ma katusa shi gaba inzaici abinci,kuma bai magana ko kadan sannan bai tabajin koda wasa ya yi wata addua ba.
Ko salla ya gama zai tashine kurin inya gama tazbihi,baya rokon komi.
Amman yau shine da adduar gama cin abinci!lallai akwai wani abu,wannan aikin asu shida fiyah bai kai har hakaba,
Yana gama wa tashi yayi ya hau wani abun exercises yana yi,don abunda yaci ya narke yaje ya kwanta.
Gajiya yayi a kallon da alik yake mshi yace"man what's happen"
Ajiyar zuciya yasauke yana sake kallonsa yau Alfah ke tambayarsa meke damunsa gaskiya lamarin azimunne.
"Katai ka kwanta kagaji kila,ko kabar yi mun wannan kallon"
Cewar Alfah
Malik kamar jira yake yace"ba dole nake kallon ka ba."
Bai jiyoba yace"dana yi me kenan?"
"Uhmm kaima kasan abunda kakeyi wai shin wani abune yafaru can da bazaka iya gaya man ba saidai kazauna kayita rusa kuka"
Saukowa daga kan machine din gudun yayi yana kyalkyala dariya malik hangame baki yayi yana kallonsa cike da rudani,after six years saiyau Alfah yake dariya. dariyar ma irin wadda tun taletale yakeyi.
Saida ya gajiyace mashi"ni ake rusa kuka malik,na lura kafara koyon karya wajen wannan marar kunyar yarinyar,ols kace mata tadaina koya maka karya babu kyau."
Toilet yashige donyin bush yabar malik da saki baki galala.......(nikau ace maza dao sauro ya atayaciki🤣🤣)
gajiya yayi da zaman ya fita yabarsa shima ranar yajima bai bacci ba,yana mamakin lamarin Alfah kamar wani mai aljanu.
💞💞💞💞💞💞💞💞💞
Wayarta dake ta ring ta tasheta daga baccin bayan sallar asubah data koma.
Tana murtsike ido tatashi badan baccin ya isheta bata lalubo wauar bata ma tsaya kallon mai kiran ba ta dauka.
"Assalamu alaikum"
Cewar fiyah da muryarta cike da bacci.
"Wa alaikumussalam,sorry na tasheki daga bacci"
Ciro wayar fiyah tayi don ganinwsye sunan zakiyya data gani yasata idasa wartsakewa.
"Aa ba komi wlh ai gara ma dakika kira intashi haka nan ashe ma har shadaya tayi inanan ina bacci."
"Aikuwa dai tayi,dama.kira nai ince maki don Allah kozaki zo mu hadu tun jiya da muka rabu awaya kin barni cikin tunani wlh."
Mik'a fiyah tayi tana salati tace"zuwa karfe nawa kenan?."
Tace"arond 4:00"
"Okay ba damuwa kimun text din wajen da zan sameki saina zo karki damu ba wata matsala babba bace,inhar kin bani hadin kai yadda ya kamata"
"Kome kenan dai sister sai kinzo."
Ta kashe wayar saukowa tayi ta shige kewaye .
Wanka tayi tay brush ta dauro alwallah harta mance rabonta dayin walha.
Shirya wa tayi tana tunanin yau wayayi masu karin safe don ita bata masan yadda ta kaya ba bayan sallar asuba data dora masu ruwan wanka,tasan dai ta dawo daki kila daga nan bacci ya saceta b'arawon banza shida bai kunyar satar kowa.
Dariya tayima kanta ta shirya cikin doguwar riga mai kyau,dirarren jikinta ya bayyana yadda rigar take dashap sosai.
Turare tafesa dandanan kamshinsa ya fado mata arai da dramer su ta jiya kamar wata zararra ta kama dariya kafin tace"mugunbanza saina rama wlh"
Wayar ta ta saka caji tabarta tarufo kofar ta fito kasancewar jibi suna yasa gidan tun yanzu da yawaitar jama,a amman ba sosai ba.
Dakin maijogon ta nufa tun kan ma ta karsa take jiyo kukan princess dinta.
Da sallama ta shiga tana cewa.
"Mun shigesu princess wannan kuka haka kamar ana zarar ranki,Anty mekika ma haka da zafi nasan dai princess dina bata kukan banza."
Wata kanwar uncle dake gefe ita da wata mata inajin kawar Antn ce tace"aikuwa safiyyah wannan princess din taki bama kukan banza ba hardana wofi yi take,tunda ita bata son uwarta ta huta bata son goyo kuma bata son adauketa azauna kijimun wana mulkin mallakar."
Dariya fiyah tame tace"Uhm Anty falmata kenan don bakusan yadda Anty jamila ta ba wa mama walaba ba da ba zakice haka ba."
Harararta antyn tayi tana jijjiga babyn tana bata nono tace"aikau safiyya kin cuceni da kikai fatan ta biyoki,da yesmin ce nayi imanin har nagama goyonta bata mun wannan masifar,amman yarinya tun randa tazo duniya sai azabtardani take."
Duk dariya suka saka mata nan kuma suka shiga hirar kuruciyar juna suna raha saida fiyah taji cikinta naniyar kullewa tatashi taje tayi break.