← Book details Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 87

Sashe 45

Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tabbas aikinsune nafarko kila suna son kasheshi su kwashi dukiya,na biyu wannan yaron mamman da suka biyo zakiyya umma tana son ya maye gurbin Alfah koma ince ya mayen,suna ganin asirinsu nangab da tonuwa yasa suka yanke wannan hukuncin,tunda har suka iya farautar ran zakiyya ta silar haka to kau babu makawa shima farautar ran nashi aka biyo yi don su smu cimmabumtr su sugudu.lallai akwai marasa imani cikin mutane dayawa,har ki iya saka wa akashe yarki sannan kisa abi mijinki shima akashe saboda abun duniya,wannan rayuwa abun tsoroce yayinda rai ya zama ba abakin komai bamutame sun maida kudi sune rayiwar duniya,akansu babu abunda bazasu iya ba.
Har suka isa asibitin tana wannan nazarin.
Dakin da aka kwantar da baban suka tambaya,dalha yake masu jagora har xuwa dakin.
Togewa mama tai tana hawaye bata san mezata tarar ba,tanajin tsoron ganin abunda zuciyarta bazata iya dauka ba.......riko hannunta fiyah tayi cikin lallashi tace"mama kiyi hkr ki natsu babu abunda yasamu baba mai girma insha Allah kisaka natsuwa cikin ranki kar kitada mashi hankali"
Da haka ta kwantar mata da hankali suka tura kofar suka shiga,
Kwance yake yana bacci har lokacin ga kafarsa nan andaure da bandage,alamun itace keda matsalar.
Kallonsa suke cikeda tausayawa yesmin har lokacin kuman take likitanne yashigo.
"Sannunku kunxo ganin mai jikiko"
Dalha ne ya iya bashi ansa yace "eh dr,yajikin nashi"
File dinsa ya shiga dubawa yana cewa"he is very lucky,bulet din bai shigeshi sosai ba don kadan ya hana bai bita cikin kashin kafarsa ba,wanda da hakan ta faru sai anyi mashi aiki sosai.amman anyi sa,a hakan bata faruba ku godema Allah don cikin sati guda zai iya warkewa insha Allah.inhar yana shan magunguna yadda ya kamata,gasunan ma har ansiya tun dazun.yanzu da ruwan nan ya kare zai iya tashia amman bazamu baku saama yanzu ba akallai zai kwana biyu anan din."
Ajiyar xuciya mama ta sauke tanajin sanyi cikin ramta Allah abun godiya dayasa babu wata babbar matsala.
"Dr waye yasiyo magungunan?"
Inji safiyyah "Alh ne ya bayar da kudin komi harna tsawon lokacin da za sallamai,shima mun bashi gad don shi ciwon da sauki bai kai ma wannan bawan Allah ba"
Mamaki ya kama su sudukan mama har bakinta saida ta hangame saboda tsananin mamaki,Alh muazzam din zai iya yiwa baba wannan abun,to dalili dame? Mehakan ke nufi mamadai ta shiga shakku tace"likita anya kasan mekace kuwa"
Daroya yayi yace "hajiya kenan to menene,koba shiba kowaye zai iya yin fiye da hakan akan mutumen dayayi saving rayuwarsa,yaji dadine kuma na tabbata ba iyakar abunda zai yi ba kenan bari dai har ya warke,don bacin mijinki hajoya bana tunanin iyanzu Alh muazzam ba,ai janazar sa ba"
Kallon karin bayani suke mashi amman sai ya nufi hanyar fita kafin ya juyo yace"kuna iya zuwa kudawo anjima sai kudawo yafarka zuwa karde biyu amman kina iya barin wannan saurayin"
Kowa da kalar tunaninsa akan wannaa sabon al,amarin.
"Dalha ka zauna da baban ku zamuje gida in aka gama hada kalacin sai akawo maka."
"Aa mama ki zauna ke sautai tare da su safiyyah idan suka hada sai akwo maki nakin,idan nakwo maki saikitai ni inzauna"
"Toshikenan kuje din"
Tafiya sukai gidan akabar mama wajensa.

💞💞💞💞💞💞💞💞💞

"Bafa ka isa kace zaka ajiye mun wannan yarinyar ba,inbacin inda sauran xuciyar imani wallahi bazan kaita asibiti ba saidai ta mace acan bisa titin,sannan taci darajar wannan yarinyar wallahi da ko sake bi ta kanta bazan ba,don haka inhar kana son muzauna lafiya ka dauketa daga cikin gidanna,inba haka ba bollah azim nizan fita kuma bazan sake dawowa ba,au kinci nasara wancen lokacin bai isheki ba akaina har sai kin sake biyoni cikin duniyar dana sake kin chaza mun kwalwa ko,to baki isaba tunda naga take-taken ki bakison kiganni ina rayuwa adoron kasa,to karya kike kinci karya kin kwana da yunwa wallahi."
Tunda yafata balbalin masifarsa tana durkushe kasa tana kuka bilhakki da gaskiya..........malik kallonsa yake cikin takaici amman har yau baiga laifinsa ba akan abunda yake ma zakiyyar,laifinsa anan dayake hakikancewa lallai lalai bazata zauna agidan ba.
"Yanzu ina kake tunanin zan kaita,shin kana ringa lissafi mana Alfah,wannan xuciyar karinga sassautama kanka ita kanada ciwo tare dakai kasan da wannan,don haka mubar tada jijiyar wuya akan wannan,zakiyya tana nan gidan bazataje ko ina ba"
Kukanta ya tsananta tana cikin bakin cikin Yadda Abdoul dinta ya koma,tsanarta tayi guri tatare cikin ransa taya zata iya fahimtar dashi cewar bata da saka hannu cikin lalacewar rayuwarsa.
"Fine,nandai zata zauna dai ko shikenan"
Hanyar barin falon yayi cikin zafin rai,dagaske tafiyar zai kuma yayi alkawarin bazai dawo ba...........kamar antsikareta tatashi aguje tabi bayansa tana shashshekar kuka,part dinsa ya nufa yabanka kofar cikin fushi,don da ace ba kofar kirki bace saita balle.
Akwati ya jawo yana hada kayansa,ko likewa babu cusawa kurin yake idan ya cirosu daga hanger.
Shigowa tai cikin dakin Kamar anjehota tana nishi,rike hannu sa tai muryarta na rawa tace"na rokeka yaya Abdoul karka tai,muddin kabar nan bazan iya yafewa kaina ba,bacin wancen mikin dana sawa xuciyarka bazan iya daukar wannan ba,yaya Abdoul na gwammace ni inbar maka gidan inhar hakan zai saka kaji salama cikin ranka,zantai zantafi inyaso kome suke so suyi da rayuwata suyi mun,na cancanta da hakan."
Ta durkushe kasa gabansa tana rike da kafarsa guda sosai take kuka mai tsuma xuciya.
Wani irin ciwo yakeji cikin ransa,bai zaton har akwai sauran feelings game da zakiyyar ba cikin xuciyarsa,wani tausayi-tausayi yakejin yana tao mashi,yanajin kukanta har cikin kokon ransa.mezaimata?mezaice mata?bazai iya hucewa da wuri haka ba xuciyarsa yaudararsa take akan hakan,amman zakiyya bata cancanci yafiya da wuri ba.
Tuntse idonsa yayi yana jin wani radadi,kalamanta suna sake dawo mashi cikin kunne.

_yaya Abdoul na gwammace inbar maka gidan,inhar hakan zai saka kaji salama cikin ranka,zantai zantafi komi zasuyiwa rayuwata suyi mun na cancanta da hakan_

Su waye?me zasuyi mata?metayi masu.tsoro ya kama shi akan hakan,karsu cutar da ita dandanan yaji bazai iyabarinta tabar gidan ba,shima kuma ya hkr da barin gidan zaijira har koma me suke kullawa malik da wannan yarinyar ya bayyana,kafin ya san mizanin da zai dora zakiyyar.
Juyowa yayi yasaka hannu riko kafadunta yadago ta,biyosa tayi idonta yayi jaa saboda kuka hawaye share share,take kallonsa da mamaki ko kadan batai tunanin zai saurareta ba balle har ya iya tabata.
Malik yana bakin kofa yana kallonsu,murmushi yayi yana jinjina kokarin fiyah,na sassauta zafin ransa da saukowa da wuri.
Zaunar da ita yayi bakin gadonsa ya juya baya don baison kallon idonta,don zata raunana mashi xuciya har yayi abunda bai niyya ba.
"Kina iya zaman nan din,har xuwa sadda komi zai lafah sannan karki daman da wani ban hkrinki,kirike abunki bana bukata."
"Bazan zauna ba inhar kaima zaka bar gidan don bakaine zakabar gidan ba nice"
"Babu inda zanje inkinga kina iya zaman ga fili nanda dakuna"
Ficewa yai yabar malik tsaue yana binsu da kallo.
Isowa yayi gabanta yana mika mata hanky yace"ki kyalesa zai sakko,inha Aah komi aksan uwa karshe."
Girgza kai tayi tana tace"zasu kashe Abbi sutsara yadda zasu farmashi,ban sani ba ko harma sun aikata abunda suka shirya din,saboda jiya zuwa yau sukace zasu aiwatar.inajin tsoron abunda umma dasu zuwairat da yaya mamman zasu aikata,yaya malik duk yadda kake zaton rashin imanin umma ya wuce nan,inhar akan kudine zasu iya yin komi wlh.yanzun haka kusan shekara guda kenan umma tayi yadda tayi Abbi baya kula Ammi,ko inda part dinta yake baya zuwa,suna cikin wani hali itada ni,ima.hakan yasa naje na sanar da dady halkn da ake ciki mafarin kenan yake hidima dasu,duk abu da suke so yake yi masu."
Hankalin malik yayi masifar tashi,dajin abunda zakiyyar take fada saurin rarumo wayarsa yayi yana no layin Daddy.
"Assalamu alaikum,daddy kana gida inason ganinka emergancy ne"
"Malik,akwai matsala yanzun haka ina nan asibiti Abbinku ne baida lafiya ankawo mashi harine,Allah yakawo mashi mai taimakonsa mahaifin safiyya shine ya taimakesa,ta dalilin haka mahaifin safiyyar suka halbesa ga kafa shima ayanzu gashi nan asibitin."
Cikin tashin hankali yace"baban safiyya dadyy,innalillahi wa inna ilaihir ra,ju un"
Silalewa malik yayi kasa yana jin xuciyarsa kamar zata fito waje "daddy wane asibitinne,fatan suna lafiya babu dai wanda yarasa ransa cikinsu ko."
"Anci sa,a Allah baibasu nasara ba Amman baban safiyya yafi Abbinku jinjiki gaskiya"
Kashe wayar yayi duk ya gigice.
Haka zakiyya kukanta yadawo sabo fil,duk abunda sukeyi Abdoul yana bakin kofa bai bar wajen ba yana jinsu,wata xuface take wanke mashi fuska da jikinsa,mahaifinsa da mahaifin safiyyah.
Soyake kar abun hadamai soyake ya yakice tashin hankalin dayake ciki,amman ina abun ya ci tura abun ya gagaresa.
Idonsa yayi wani irin fitinennen jaa,mezaiyyi meya kamata yayi?
Aa babu abunda zan mashi ko addua bazan mashi ba,bai dace da samun addua ta ba koma mai zai fatu dashi yaje yayita faruwa bai damai ba.
Fitowarsu kenan suka hanhi shigewarsa cikin part din malik,
Ayadda ya fahimci tafoyarsa tabbas yaji komi bazai iya gane wane irin hali yake ciki ba.
Shida zakiyya suka shiga mota suka bar gida xuwa asibitin.

Badai editing kuyi hkr da typing error.

Don't share it pls i beg.
Bcos its for sale inkina bukata ki tuntubi wannan number.
09034722970.
[9/17, 3:42 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

🅿️.........37

"Mama kune,banji tsayiwarku ba"
Kallonta mamar keyi cike da tuhuma yayinda fiyah cikinta ya duru ruwa,tashiga ukunta inhar mama taji abunda take gaya ma ni,imah.
"Mike gaya mata har yasata kuka safiyya?ke rayuwarki yan shige shige ya maki yawa,da kinga mutun na cikin damuwa saiki shishshige mashi,ina ruwanki da ita dake nake kinmun xuru da ido,mekikai mata"
Kamar zata fashe da kuka tace"nikuwa mama mezan mata,daga na mata yamaijiki mungode da abinci,shine ta fashe da kuka tana cewa da badan baba ba da shima Abbin nasu sun rasashi kamar yadda suka raya yayansu,shinefa nake lallashinta"
Harararta mamar tai tana nuna hanya "wuce muje,banson wannan shishshigin na gaya maki,ga dalha can zai kwana dashi muje kidauki takadda kicigaba da karatu tunda kinsan gobe iwar haka kin dawo daga jarabawar"
Tafiya sukai gida don basai ma sun kawo masu abinci ba wanda ni,ima ta kawo ya wadacesu.

💕💕💕💕💕💕💕💕💕
Chapter 45 · 0% Book details