← Book details Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 87

Sashe 2

Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Taxi ya shiga yana cikin tsananin tunani,har tsoran farkawar Alfah yake,don shikadai yasan rigimar dasuke don dai Allah yabashi juriya da kuma hakuri,da zaman shi da Alfah bazaije ko inaba.
Yadda kowa ya gujeshi shima da tuni yadade da kama gabansa,saidai alkairin da yayi mashi bazai iya saka k'afa ya shure shiba,bacin haka yayi alkawarin da bazai iya karya shiba,hkr dai shine zai cigaba dayi watan watarana komi zai zo ya wuce.
Wani k'ayataccen pharmacy yaje kamar ba a nigeria ba yasiyo maganin,ya taho yana adduar Allah ya taimakeshi yasha maganin,duk da abun zai wuya Alfah ko ciwo me zai kasheshi idan ba yaga yana mashi kuka ba tofa bazai shaba,karshe har yagane inayin hakanne don yasha d'in.to dana fara kuka zaibar mun wajen.dafe kai yayi yana ajiyar zuciya kurun.......

***********

"Mamana Zan wuce isalamiya,duk da dai na makara,idan yasmen ta dawo don Allah ga hijabina nan ka igiya mama don Allah ta wanke mun."
Mahaifiyar tasu data fito daga d'akin sanwa tace"baki tausayinta Fiyah,tun safe fa bata gidanan. tana can tana wahala da gidan jamila,nasan in ta dawo ta gaji kiyi hkr kisaka wata mana."
Tsaye take bakin k'ofar d'akinsu tana saka safah,tace"shikenan mama idan nadawo na wanke,daman abunda yasa nace haka jinai nafara atishawa ina tsoran tab'a ruwa,gashi kinga yau akwai sanyi sosai."
Maman tace"subhanallahi,aikuwa in hakane kibari na wanke maki,inma dole sai ita zakisa,injin tsoran wannan lamoniyar taki Fiyah."
Jikkarta tad'auka tana murmushi mai tsananin kyau tace"kibarshi mamana,zan saka wata bari natai saina dawo in babana ya dawo ki sumbatar mun shi amadadin."
Duka ta kawo mata ta ruga waje tana dariya,ita ma uwar dariyar tayi tana cewa Allah ya shirya ki sofiyyah."

Tafiya take cikin estate d'in wanda babu kowa cikin unguwar tasu,hakan yazama dabiar yan unguwar badai kasameta da mutane sosai ba,sauri take ta isa bakin titi tasamu taxi batason ta rasa qarin ahalarin da za,ai masu yau............get d'in estate din taga an wangale,bayanta ta waiga ta hango wata dan k'areriyar G wagon fara tas zatafita. ta saba ganin irin wad'anan motocin cikin unguwar tasu *maitama estate* domin kaf unguwar babu karamin mutun duk manya manyan y'an siyasane da masu manyan mauk'ami,gaba ki d'aya unguwar sune suka fita daban,sune kaskantattun talakawa ababen kyama,don babu mai hudda dasu cikin unguwar inbanda gida guda.......don ana kallonsu wulakantattu wad'anda talauci yayiwa katutu,bacin su sunsan suna cikin rufin asirin Allah basu rasa ciba,basu rasah shaba,mahaifinsu yananiyakar kokarinsa don gani ya kawar da idonu aka kallon nawasu,taaye kan iyalinsa.........
wani uban burki aka taka gabanta,duk saurinta bata samu ta riga motar fita ba,ajiyar zuciya ta sauke tana kallon wadda ke cikin motar tana murmushi.
"Kin bani tsoro rafeea,ashe kin dawo shiyasa ma ban shigaba."
Dariya tayi tace "matoraciya kawai,shigo mu wuce baki ga time ba,nadawo wlh ko minty ashirin banba wanka nai nai salah naci abinci kurun nafito."
Bud'e motar tayi tashiga tace"kinfi kowa sanin Fiya bata da waya aiko.rabona da time tunkan nafito gida "
Dariya rafeea tayi tace"to uwar gasa magana namance,amman fah gaskiya ya dace ace yah jalal ya barki kirik'e waya hakanan."
Murmushi tayi tace"kinmance waye yah ko,to ni ai ban mance ba,amman nasan soon zai siya man tunda daman jira yake saina fara jamia."
Haka suka ringa fira har suka isa makarantar,kasancewar sometimes tare suke tafiya saidai idan daya bata dawo makaranta da wuri ba.

************
Kamar karya shiga d'akin don yana gudun ace ya farka,saidai kuma inhar Yafarka tokuwa bazai zaunaba ficewa zai...........ahankali yashiga d'akin ya ajiye ledar magungunan yana kare mashi kallo,yanajin tsananin tausayinsa yana ratsashi......kwallah suka cika idonsa ya kalli hannunsa da aka nad'e da bandeji ya girgiza kai yana tunano abunda yayi dalilin faruwar hakan.

_Waiwaye_

Exercise yake d'akin motsa jikinsa,don shikadai yake yi malik baida ra,ayin sa yakai one awa yana gudu kan injin gudun,kafin ya sauka ya dauki wani gingimemen karfe yana d'agawa shima yajima yana d'agashi kamar ba karfe yake d'agawa ba saboda yadda yake d'ashi kamar wani tsinke.......malik ne yashigo wajen dauke da tiren breakfast,ya ajiye gefensa yana cewa"tun bakwai nasafe kake nan wajen gashi har sha biyu saura ka ajiye kasaka wani abu cikinka."
Kamar yana magana da dutsi haka yayi mashi,kasancewar malik baya fushi da Alfah duk abunda zai mashi,saboda Nauyin da yadaukar wa mahaifiyarsa da kuma wanda ya daukar wa kanshi.............maganar yasake nanata mai yasake banza dashi tashi yayi ya isa inda yake,ya dafa shi yace "Alfah duk wannan abun da kake baya canza komi,kuma bazai canza ba kayarda da kaddara mana,akwai fa wad'anda suka fika shiga kunci kuma suka fawwalama Allah,saikai kace bazaka yi biyayya ga hukuncin Allah ba.sannan Nariga nayiwa momi alkawarin kulawa da............... *malikk!!!* ya kwatsa mai tsawar da saida tasaka malik firgita,jefar da karfen da yake d'agawa yayi yana zazzaro idanu,dandanan fuskarsa ta idasa rikicewa da tsananin masifa.......tunkaro shi yake yana ja baya har suka dangane da bango.hannunsa yana kerma ya daga shi ya kaiwa bango naushi,dan danan hannun ya fashe,saboda bangon ba kamar irin na bulo bane,wani sumfarine nadaban.
donsa yayi masifar jaa cikin voice d'insa mai firgitarwa yafara magana cikin dakiya,
"Wlh wlh wlh kajidai rantsuwa uku ko in kasake gigin anbata mun sunan wani cikinsu saina kashe kaina,har sau nawa zan jamaka kunne ne wai ehy."
Furzar da iska yayi yana huci ya matsa daga kusada malik yana jan numfashi,duk da tsananin tsoran temper dinsa da yake,hakan bai hana shi sake magana ba,don yana ganin inyace zai ringa kyale shi bazai ta6a sauraren sa ba,balle har ya samu zuciyarsa tayi sanyi.
"Wallahi Alfah kome zakai saina fad'a maka gaskiya,ayanzu bakada wani wanda zaigaya maka gaskiya saini,dole nafada maka kokayi aiki da ita ko karkayi nidai saina sauke nauyin alkawarin mahaifiyar.............wani uban naushi ya kawo wa malik,yayi aurin kaucewa azafafe,yanzu ma bangon ya kaiwa bugu amman saboda zafin rai bai damu da halin da hannun nashi yake ciki ba.
Cikin wani irin yanayi ya ya kalli tiren daya malik shigo dashi,wata yar wuk'a ya gani baiyi wani tunani ba ya daukota,babu wani jinkiri ya saita hannunsa ga6ar hannunsa na dama ya yanke jijiyar dake wajen.dananan jini ya 6alle kamar an kunna famfo.
Wata k'ara malik ya fasa yana tunkaro inda yake,shikuma yana ja baya yana cewa"karka nufoni,indan ka iso nan wlh saina sake yanke wata jijiyar,kafita anan inb fita ba nizan fita malik karka matsoni,kabarni na mutu kabarni natai inda zan fi samun jindadi,kuka malik keyi yana cewa"Alfah waya gaya maka mutiwa hutuce,mekayi wa Allah daza katai dashi matsayin guziri,inhar kamutu ahalin yanzu wlh wuta ce makomar ka......karka fita Alfah katsaya katsaya nace..........amman bai saurari malik ba ficewabyai daga cikin d'akin,waje ya nufa yannunsa jini kurun yake fitarwa b kadaba........kfi Malik yafoto tuni alfah yafice daga gidan,tafiya yake baisan inda yake jefa k'afarsa ba.........ko minute biyar bai da fitowa ba zai tsallaka titi,mota tayi sama dashi ya zube wajen babu numfashi.

_back to story_

Likitanne yashigo yace"bai tashiba kenan,"malik yayi ajiyar zuciya yace"eh dr gashinan naga ma kun cire jinin,gashi ruwan shima ya kusan karewa.......akwai sauran ruwan da za asake saka maine."
Dr have"sauran leda biyu hudu ce ansaka biyu,saura biyu da wani abune?"
Shafa kai malik yayi yace"bani son ya farka ba agama saka ruwan ba,don ba lallai ya zauna ba daya farka zai iya fixge carnula ya fice."
Jinjina kai yayi yace"wane irin mutunne shi haka,na lura yana da wata irin zuciya amma da gani akwai abunda ya faru dashi baya,don nidai nasan wannan fuskar sai yanzu na tuna inda nasanta.watarana na bar wajen aiki nan ina sauri zanje gida saboda maidakina tamun waya gidan babu lafiya,saurin danake yasa har nabanki wani mai anoconder kuma nai mashi babbar 6anna.........dandanan titin ya cika yafito yana ta bala,i saina biyashi gashi ko sisi ban dashi ga aljihuna,ga shi yaci kwalata duk hkrin da ake bashi ya rufe ido cewa saina biyashi,saiga wannan bawan Allah cikin mota shida driver sa,fitowa yayi yana tambayar lafiya? don titin ya cinkushe babu hanyar wucewa.
Bayani nai mashi da halin da nake ciki na sauri inje ga iyalina.wlh malik check ya rubuta ma mutumen,na five hundred thousand bacin kuma kudin duka dubu dari uku ne..........naita mashi godiya ba karamin dadi najiba kullum ina adduar allah ya had'ani dashi inyana neman taimako nima nataimaka mashi."
Malik ya yi ajiyar zuciya yace"Dr labarin mai tsayine kuma bazan iya baka shi ahalin yanzu ba,saidai ko nan gaba,amman tabbas Alfah yana cikin halin taimako,wlh nikad'ai bazan iya shawo kanshi ba."
Gyara tsayuwa dr yayi yace"na fahimceka malik,karka damu ga ID card dina nan duk sanda kake bukatar taimakona,ga address dina nan ajiki da contact dina,insha Allah nima zan bada tawa gunmawar karka sare kacigaba dayin iyakar kokarinka har mukai ga ci...............shiru sukai ganin yana jujjuya kai yana ya mutse fuska,kafin ya bud'e idinsa yana kallon rufin d'akin..........idonsa ya sauka kan Malik da dr suna kallonsa suma.
Da alama yana nazarin abunda yafaru dashi ne.duk sunyi zuru suna kallonsa gaban malik na fad'uwa saboda gudun abunda yake tunani.......ai baigama nazariba yaji wata irin shak'a da ya kawo mashi ya gama shi da bango,idonsa saboda tsabar masifa da zuciya kamar anzuba mashi garwashin wuta.
"Meyasa kakawoni nan ehy,banace karka sake ka tab'ani ba,meyasa bazaka barni nabar masu duniyarba!"cikin tsananin tsawa yake maganar ya cigaba da cewa"malik!ka cuceni kacuce ni nace,yafada yana jijjigashi kafin ya tunkud'a shi ya fad'i. Kallon carnula dake jikin hannunsa yayi yayi mata wani irin fizga,dandanan ini yace yaga hanya k'ofa ya nufa atsananin fusace ya bude yafice tare da bankota da mugun karfi........Dr da malik binsa sukai agune don ahalin da yake ciki komi zai iya faruwa dashi yadda yake tafiyar zaka gane cewar gentle guy ne kuma k'ak'k'arfane.........gudu suke yana sauri shikuma amman sun kasa kamoshi,har sun bar titin asibitin sun yanki wata hanyar daban,duk yadda suka zo iskeshi abun yacitura........titin nasarawa suka hangoshi zai tsallaka kenan wata mota ta rugo da mugun gudu jikake..........kuuuuuuuuu karar burki da cin taya.

Command share pls.
Mrs bb ce
Mom muhssen
[9/17, 3:34 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

🅿️.......3💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

🅿️.......3
Chapter 2 · 0% Book details