← Book details Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 87

Sashe 42

Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Sunyi sallama da Anty jamilar tana tayi mata godiya akan hidimar da tai mata,kamar zatai kwallah haka taji don dan zaman da sukai saitaji inama taita zama da qanwar tata,koba komi sunyi wasa da dariya kuma ta rage mata ayyuka,amman tasan baba bazai yarda ba kuma itama fiyar tafison kusada mama da baban.
Suna tafiya yana janta da hira tana biyesa,har yazo kan maganar abokinsa.
"Nikau safiyya ina kika san Alfah,ayadda na fahimta ranan ba bankeki yayi ba,karki boyemun inason in sanine saboda wani dalili"
Saitaji bazata iya boyewa uncle din nata ba ta sadda kai ta fara bashi labarin haduwarsu da kuma dalilin shigarta rayuwarsa,har kawo abunda ya tsayar da ita bata dawo gida da wuri ba,harda cigaban da ya samu tadalilinta.
Shiru yayi yana jinjina kai kafin yace"niyyarki mai kyauce safiyyah,amman kinsan hakan akwai hadari ga rayuwarki,wannan aikin namiji ne ya dace dashi ba ke mace ba,saboda yadda amana tayi karanci cikin rayuwar nan,kuma nima nasan da wannan labarin,shiyasa na tambayeki tabbas nima raina ba yadda Alfah zai aikata haka ba,duk da kowane lokaci mutun zai ita canza wa,amman da kamar wuya gaskiya.don haka ki kula ki kiyaye ya dace tun farko ki sanar da mama koyaya dai in wani abu yabiyo baya duk da ba fata ake ba,atleast tasan mekike ciki"
"Uncle wlh bazata barni na taimakesa ba saboda abunda ya faru tsakaninsu da mahaifinsa,gabace maitsawo tunma ba aifemu ba muduka,abun ya faru shiyasa duk unguwar babu mai kulamu bamu banda yan tsirarunsu,shiyasa na boye abun babu wanda yasani cikin gidan mu don kar ahanani kuma Alhamdulillah komi yana zuwa da sauki nanda dan lokaci komi ya kammala,nima inhuta in samu natsuwa."
Murmushi yayi baice komi ba don yayi imanin shigarta rsyuwar Alfah baya nufin ta fita,don ga dukan alamu ita dashi kowa yana jin wani abu game da dan uwansa,shiyasa bai bada karfi wajen ganin muhseen din sa ya sameta ba,yana da burin ta dawo da abokin nashi cikin hayyacinsa,kuma zaiso ace sunyi aure sauran halayyarsa ta idasa daidaita shi,shiyasa ma zaifara nema wa muhseen din Auren yesmin,don bazai so ace ya rasa daya daga cikinsu ba,don yarane da suka samu kyakkyawar tarbiya yadda ya kamata.
Sauketa yayi suka shiga ya gaida mama lokacin baba bai dawo gida ba,yaba fiya dubu goma ladar aikin data sha na zaman bakwai.taba kowa naman sa na ajiye nata gaba tanaci saida tayi rbin ledar sannan mama dataga bata da niyya saurara mashi ta anshe tana fada.
Wajen karfe sha daya na safe tana dakin mama yesmin taje islamiyya,maman kuma tana kitchen. Ta dora sanwar rana.
Karatu take sosai duk da xuciyarta bata gareta hankalinta ya kasu kashi daban badan,ga zakiyya tana son jin halin da take ga Abdoul tana son sanin koya tashi jikin yayi sauki bata sani ba,shikuma wanda xai kiratan ya gaya mata shiru bai kiraba...........tana cikin wanna halin wayarta tayi kara,saurin kallonta tayi yaga sunan sa tai saurin dauka tana kanga wa ga kunne.
"Yaya malik ina kwana"
"Lafiya lau qanwata ya kika tashi,fatan kinyi bacci daren jiya"
Juya ido tayi alamun me yake nufi da tayi bacci jiya lobatai ba,
"Na tashi lafiya yaya malik"
Kallon Alfah yayi dake kurban tea mai dan gumi don ya gasa cikinsa,kamar baisan da wadda yake waya ba.
"Kinjini shiru ban kira kiba,walh sai yanzun ya tashi babu jimawa inbashi ko"?
Tana son ansa kodan taji muryarsa,don harga Allah Abunda take son jikenan,amman idan tayi hakan wane irin kallo zai mata,kenan ma fushin nata baije ko ina ba,tunda daga jin baida lafiya duk na rikice.
"Kinyi shiru"
"Kyalesa yaya malik,kadai gaidashi da jiki Allah ya sawake"
"Aa karmuyi haka dake,sannu fa kurin zakiyi mashi"
Rutse idonta tayi tanajin kamar tace eh yabashi amman ajinta zai zube,
"Ka kyalesa yaya malik,aibadole saina yi magana dashiba daga nan ma idan na mashi Addua zatazo,rabu dashi yanzu ma karatu nake zan ajiye wayar,kila idan na samu time anjima da yamma infito inga jikkin zakiyyar"
"Shikenan,amman banji dadi ba da kikace kar abashi,kingashi nan fa har ya miko hannu sa...........karka mun sharri ta dauka dagaske kake ban son wanna game din"
Cewar Abdoul dake shan tea din sa.
Ras taji abunda yace wani abu ya tsaya mata ga makoshi,watau shi ko ajikinsa bai damu ba.kwalla taji sun silalo mata ta kasa gogewa muryarta na rawa kamar zata fashe da kuka tace"yaya malik sai anjima,kayo mun text din asinitin da aka kaita da no din dakin"
Saiyaji ta bashi tausai,hands free ya saka wayar yadda Alfah zaiji muryarta wata kila shima yaji abunda tajin.
"Shikenan qanwata zan turo maki,amman kizo nan basai muwuce tare ba"
Kwamciya tayi ta dora kanta kan filon mama hakanan kuka yana son kubce mata tace"yaya malik aina ce maka bazan sake xuwa gidan nan ba,kayi hkr bazan iya zuwaba mu hadu dakai Asibitin akwai maganar da zamuyi"
"Shikenan saikinzo din"
Kashe wayar tayi tana kwantawa ta dunkule waje guda tana kuka kasa kasa,wanan abun ya cuceta wai meke faruwa da xuciyata ne haka,Allah kaga niyyata karka saman Abunda zai wahalar dani bacin taimakone nayi,.......ta jima tana kukanta kafin bacci ya sureta.

Tunda suka gama wayar ya silale inda yake ya kwanta,idonsa alumshe sautin muryata yake jin yana amsa kuwwa cikin kunnensa,tabbas kuka take wannane karon na biyu dake iya gane kukanta ta sautin muryarta,yana jin bai khauta ba abunda yayi matan shekaran jiyan,ya zaiyyi ba laifinsa bane zuciyarsa ce ta buga da ganin zakiyya,wadda tsawon shekara shidda ko mai kama da ita bai gani ba,haka xalika baya iya cewa ga lokaci guda daya zauna yayi tunaninta,saboda ya dora ma kanshi wata irin tsanarta da kinta gani yake tunaninta ma inyayi yacuci zuciyarsa,wani iri yakeji wanda bazai iya tantance meyakejin ba,amman shima da yana iyawa to tabbas kukan zaiyyi,don abun yafi karfi sa.
Inama Zai iya lallashinta yanzu inama zai iya ansar no dinta yayi kiranta,bazai iya ba mezai ce mata dawace kalmar zaifara.
Saiya tuna ranar da yake gidan yayarta fushin da yayi biyonsa da tai tana kwalla don ta bashi hkr,kenan ita bata camcanta dayayi mata hakan ba,dafe kansa yayi tare da saitin xuciyarsa don ciwo suke mashi.
Malik ne yafito yayi shirin zuwa company tunda yau shibazai iya fita ba,kallonsa yayi yaga yadda yake shafa kirjinsa da kanshi ya iso inda yake ya zauna yace"daka taimaka ma xuciyarka kabar tunanin tunda bata so,inkuma inbaka no dinta kakirata niba wahala bane wajena,inkai kana ganin hakan kamar da wuya,gata nan na saka maka ka kirata ko karka kirata ya rage naka.daka cire ma kanka wannan nauyin ka fuskanci reality da yafiye maka sauki Abdoul,amman nasan indan nafurta abun da yake damunka zaka karyani kuma zaka dauki zafi,don haka nidai karufa man asiri kacire damuwa,zanje company daga can zan biya store.likita zai dubaka anjima amman kafin nan zanje naga jikin zakiyya."
Uffan bai cemashi ba idonsa a kulle bai bude ba,har malik din yafita kallon wayarsa yayi yaga digit din numbers din daya kera mashi,daukar wayar yayi yana kallonsu na dan lokaci kafin yasa hannu ya goge su tas. Ya maida ya ajiye.

Kuyi hkr babu yawa wlh masassara nake. Daker idan zanyi sanyin idaniya plsss kumun uziri.

It's for sale if u need it meet me 09934722970
Don't share it plsss I beg
[9/17, 3:41 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

*ABDOUL-NASSER NA KUDINE,INKIKA KARANTA BAKI BIYA BA KEDA LILLAHI,GA MAI BUKATA ZAI IYA TUNTUBAR WANNAN NO DIN 09034722970.

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

🅿️.........34
Chapter 42 · 0% Book details