← Book details Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 87

Sashe 37

Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Gyaran falon tayi cike da rashin kwarin jiki,bawai don gajiya ba,eh to akwai gajiyar ma amman kuma zuwan Abdoul wajenta shine dalilin dayasa jikinta duk ya mace murus.
Turaren wuta ta saka ta kuma kunna tsintsiyar kamshi,saida hayajin ya gama bud'e dakin sannan ta dauko freshner ta sake sawa,ta gyra labulbulun falon yayi lum gwanin sha,awa ga hasken kwan nefa farin haske da blue sai red green dake haskawa.fitowa tayi ta iske su cikin falon uncle yana rike da little fiyah suna hira da Anty.
"Kishiga ki tanadar masu abunda zasu ci ko hakanan xasu zo sutai."
Ya mutsa fuska tayi tace"Anty ruwa ma kadai ya ishesu"
Harararta tayi uncle yace"haba dai fiyah,bakonka annabin ka jeki falona akwai snacks din da muka rage dazun da friends dina suka zo,basu ci daya wa ba sai ahada masu da lemo ko"
Ba yadda ta iya haka ta juya taje ta dauko taje kitchen ta zuba su cikin wasu bowls,Anty tace akwai ferfesun yan ciki data saka akai mata dazun,tace ta dibar masu .
Kamar zatai kuka tace"wai Anty saikace wani shugaban kasa ne zai zo"
Kallon banza tayi mata tace"dalla banson sakarci,mutun baitaba zuwa inda kake ba yau zaizo kuma sai bazaka tarbeshi da kayan motsa baki ba,ni indan tanine wlh bamson zuwansa,don inajin kamar da biyu zaizo yana iya amshe ma muhseen kunerarsa.
"Anty wai ance maki muhseen dinma wani sonshi nake,nifa wlh kawai don ba yadda zanyi dashine,nifa ba yanzu zanyi aure ba"
Dungure mata kai tayi tana wucewa tabara.
Bayan ta gama shirya masu abun da zasu bukata ta koma daki,samun kanta tayi da yin wanka hasana tace"bako zakiyi ne fiyah"
Shafa take yi cikin mutuwar jiki "Wanda ya kadeni rannan zaizo dubani"
"Kice daya kadeki sai kuma yayi wuf da xuciyarki"
Murmushi tayi tace"waye yace maki,shi baya soyayya ai"
Dariya hasana tayi tace" naga waliyyi,karewar baya soyayya bari dai mugani ni nasan badubiya kawai zaizo ba harda banruwa zaiyiwa flower sa."
Dariyar da bata shirya ba tayi tam cigaba da abu da take.
Uncle ne yafita jin karar mota gaisawa sukai sosai da Alfah da malik,sun jima a harabar gidan kafin yyi masu iso.hira suke da malik kamar sun saba,indai malik ne badai iya hira ba koya kahadu dashi zakaga ya jaka ajiki dandanan zaku saba baida bakunta.
Anty ta wuce can ciki.
har cikin falon ya sauke su suka cigaba da hirar,sai daga baya ya fito don kiran safiyyan.
Simple make up tayi powder da lipstick sai kwalli,tasaka rigarta coffee brown da zanen milk color ajikin rigar,sai tayi rolling da milk din gyale tana fesa turare.
"Safiyya kifito haka nan sun iso,hasana ki rakota saiku gaisa ko"
"To uncle insha Allah"
Kasa motsawa tayi ita wai dawace fuskar zata tarbi wannan mutumen,kuma ma dame yazo ne wai.
"Kika zauna kuma ko gabanki yake faduwa ne?"
"Kice bashi kadai ya kamu ba ace kema yayi carab dake,"
Murmushi tayi tana mikewa tace "muje"
Chapter 37 · 0% Book details