← Book details Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 87

Sashe 66

Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fiyah na jinsu duk abunda ya wakana saitaji yabata tausayi,kuma ya burgeta hakika tana taya yar uwarta murnan zamun namiji irin muhseen,Allah ya samashi soyayyarta fiye da wadda yesmin take mashi.
Kallonta tai ta dunkule waje guda tana raba ido,dariya ta kwashe da ita tace"to mrs love tashi ankashe maki boss din saiki bani ladata"
Boye fuskarta tai tana dariya tace"nidai Adda kibari don Allah bana so"
Cikin tsokana tace"ehyy bakiso meye bakiso muhseen din kuma yanzu shine bakiso,innalillahi bari inje insanar da baba to ashe hasashena karyane........Wlh Adda ba haka nake nufi ba kiyi hkr"
Rike bakitai tana dariya tana kallonta,saida fada kuma kunya ta kamata ta soke kai tana dariya
"Adda don Allah kibari kunya kike bani"
"To nabari yar qanwata Allah ya tabbatar da alkairi yakuma kara kauna"
Kin ansawa tai da amin din.

💞💞💞💞💞

Umma dai direct gidan mahaukata aka kaita,saboda hauka take tuburan idan kasake kaje inda take saidai akwasheka ayi asibiti dakai,yaranta banda kuka babu abunda sukeyi Abbi kuma ya sakasu daki ya kulle yasa wani soja yayi masu dukan tsiya,har saida xuwairat da haulat suka suma.Amina ce kurin bata suma ba,khadija kuwa Allah yasota bata ciki ta ruga ma wajen mami abunta,xindir haka aka fitar da umma daga gidan don duk kayan da aka saka mata saita yagasu tayima su fatafata,gashi duk tajima jikinta ciwo ta yayyage fatarta,sai ihu take tana tona ma kanra asiri wani abunma babu wanda yasan tayi,sai lokacin akeji ashe tun sanda tasan mami na da cikin Alfah taso atura mata aljanu su sace cikin,kuma su hanata daukar wani amman dayake Allah yace sai Alfah da ni,ima sunzo duniya Allah baibata iko ba.
Haka aka kwasheta mutane sai Allah wadarai suke da ita,anan wau sukasan sharri akaima Alfah bai akaita abunda mutane suke zargiba.

Alhaji kwangila kuwa yana tsaka da hira cikin iyalinsa don duk yinin ranar kin fita yayi,tsoro yakeji kar shima asirinsa ya tonu akamashi don ya tabbata Alh muazzam bazai kyalesa ba,shiyasa duk atsorace yake dayaji karar get zai zabura yace waye.saiyaga ba yan sanda bane ko sojoji saiya natsu.
Ya sadakar kila yatsira wajen karfe takwas na dare kurin saiga sojoji mutun hudu yansanda mutun hudu,babu ma wani dogon bayani sukai sama dashi suka sashi motarsu aka dankara mashi unka,kiraya ke kubarni nayi magana da lawyer na nifa karya akemun wlh sharrine"
Tunda wani bajimin soja ya makamai bakin bindiga baisake magana ba,don hakorinsa uku saida suka fito.
Ranar momi da su rafeea sunga tashin hankali,jin rade raden cewa ai matar Alh muazzam yake zuwa dadiro wajenta.saboda kidima da tashin hankali saida momin rafeea ta suma,daker ta farfado suka hau kuka kamar Alhajinne ya mutu.

Abdoul bai tashi daga office ba sai bayan isha,i don yau yayi ayyuka sosai daya kwana biyu baiba.
Sanda yake kokarin tafiya dady ya kirasa awaya,bazai iya tuna ranar da dady ya nemai ba,awaya dai kamar haka komi yake neman sani akanshi zai nemi malik,amman yau dady dakanshi anya ba akwai wani abuba.
"Hello ina wuni"
Abdoul yafada daga can daddy yace"gobe wajen karfe goma na safe kazo gidana na maitama ina son ganin ka"
Wata irin faduwar gaba ce ta sameshi "gidanka na maitama?"ya maimaita dadyn cikin bada umurni yace"eh shi ake nufi hakan ka manta address din na turo maka,kokuma xuwane bazakai ba ka nuna man har yau ba,a isa dakai ba"
"Aa daddy ba haka bane kayi hkr zanzo amman awannan time din inada aiki office kodai na sameka office dinka idan narage aiki"
Yafada yanason xillewa daga xuwa maitamar don inyaje ciwon dake kirjinsa zai fama.
"Karfe goma nace ina son ganinka a maitama idan kuma ya zarta haka nidakai ne"
"Afuwa daddy zanzo kayi hrk"
Yaja tsaki yakashe wayar sauke tashi yayi yana jan numfashi,mezayyo maitama shifa ko kallon get din ma ayanxu baiso,aduk unguwar bakda wani masoyi bayan mami da ni,ima suma wataran yasan zasu hadu amman ba cikin unguwarba,babansa bai sonsa yan uwansa basa sonsa,yarinyar daya kwallafa rai da samunta tace bata sonsa tome yarage mashi amaitama?jiyai ma zai hada ma kanshi tension yayi saurin kawar da tunaninta yana shiga motarsa yabar company.

Wajen masu suyar balango da kaji ya tsaya idan bazai manta ba tana masifar son balango,da fruits sai fresh milk.
Murmushi yayi yau inason shiryawa dake dole zan nemi abunda zan faranta maki dashi kiyya.
Fitayai yasiyo balangon shikuma ya siyar masu gasassar kaza shida malik,yakara gaba yasai fruits ayaba apple abarba da inibi.yasai fresh milk din Katan guda mai sanyi sannan yadauki hanyar gida.
[10/3, 9:09 PM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSEER*
*(ALFAH)*

WRITTEN BY

MRS BB
MOM MUHSEEN

FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970

🅿️.............54

Suna falo yau da malik suna kallo news,babu laifi yaga canji daga zakiyyar yau amman bai tambayeta dalili ba yasan can tsakaninsu ne.
Sanda ya shigo duk suka xuba mashi ido har ya karaso cikin falon,yana xubewa cikin kushin.
Ya na furta "washhhh"
Malik yace"sannu yallabai,daman nasan za,ai haka katara ayyuka dayawa dole zaka ringa over stres din kanka"
"Wlh kuwa,don jinake gobe kamar karnaje nasan kuma hakan kara tara wasu zanyi"
Zakiyya na shan lemon fata bata tsoma masu baki ba,idonta nakan news din da,aketa nunawa da hoton Alh kwangila ajiki ankamashi da cin amanar Alh muazzam canji,wanda hakan ya jawo an dauresa gidan yari daurin rai da rai........wani dadi taji yadirar mata koba komi dai asirinsu ya tonu izuwa yanxu tasan Abbi yaji komi ya koma ga Mami,kuma ba jimawa xai nemo dansa tilo kamar rai yanemi afuwarsa,koda Abdoul bai aureta ba wannan nasarar tafi komi dadi wajenta.

Daga shi har malik kallon tv suke shi malik daman yasan hakan xata faru,amman Abdoul mamaki ya kasheshi meya hadoshi da Abbi,to kodai ya gano cewar baida laifi abunda duk ya faru?
Kallon fuskar malik yayi yaga babu wani mamaki ko wani al,ajabi haka zakiyya saima murmushi da take abunta.
"Malik meyafaru acan,nasan kana da masaniya"
Kafada yafaga yace"i don't know yadda ka gani nima haka"
Murmushi yayi yana mikewa"hakan ma ya sake tabbatar mun kasa komi,uhmm rike saninka Abdoulmalik."
Har ya juya yakai bakin hanyar dakinsa ya jiyo yana kalonta yace"kiyya"
Kamar bata so haka ta jiyo tabisa da kallo,lumshe mata idonsa yayi da suke cike da gajiya yace"wadancan ledojin kije dasu kitchen,naman asake gasashi fruits asasu frig plss."
Lauya kai kurin tayi batace komi ba,shikuma ya shige don watsa ruwa ya kuma sauke sallolin dake kanshi don baiyyi magruba ba.

Damuwar duniya tataru xikin xuciyar fiyah,data dauko wayarta saitaga aibata da no dinsa,bala,in son jinsa take wata irin kewarsa take ji wadda bata taba jin irin haka ga wani da namiji ba,idan ta tuna abunda yasa yayi fushi har kwalla take.yesmin ta lura tana cikin damuwa ta tambayeta.
"Nikau Adda kamar wani abu yana damunki,don Allah ki gaya mun idan yafi karfina saina yi maki addua,kwanaki na dauka aka yaya muhseen ne to kuma naga maganar ta wuce still bakibar damu ba,kodai na gaya ma mama"
"Karkifara kuskuren gaya mata don bata wa zamuyi"
Cikin damuwa tace"amman Adda ni kina kokarin fitar dani cikin tawa damuwar taya kikeson zan jure ganin ki ahaka,kigaya mun ko shawara saina baki"
"Yesmin idan lokacin sanin yayi zan gaya maki amman kicigaba da man Addua Allah ya zabamun abunda yake alkairi ga rayuwata."
"To Adda insha Allah,amman kema ki dage kiyi tayi sannan ki rage saka damuwa bakiga yadda kika rame ba"
"Zan rage yesmin karki damu"

Tafita don kiran da mama ke mata,kalon wayarta take kamar xata ganshi aciki,wata xuciyar ce ta raya mata kila bazai rasa wannan sabon layin nata ba,don shine yayi mata register kila yayi saving no din.wannan yasata jin wani sanyi har cikin ranta,ta rarumo wayar da sauri amman saita rasa wace no din zata kira,idan tayi nazari xata iya tuno no din daya kirata atsohuwar wayarta amman daker idan daidai zata rubuta,haka ta fara sakawa sa bismillah tana adduar Allah yasa itace.
Hannunta har karkarwa yake idonta cike da kwalla,bata san girman soyayyarsa acikin ranta ba amman koma ya take tana masifar azabtar da xuciya da gangar jiki.
Kamar wasa taji tana ringing,wata zazzafar ajiyat xuciya taja harda lumshe ido.

Yana dakin dayake aikin sa wani dakine na musamman da yake zama yana rage ayukansa akan computer,yana rubuce rubucensa fa takaddu.suna tare da malik ma alokacin yana nashi aikin shima,yace"yallabai wayarka fa tana neman agaji"
Girgiza kai yayi yana saka biro ga bakinsa idonsa ga computer yace"bana jin zan iya waya aikina nake"
"Idan someone special ne fah"
Murmushi yayi yana kallon kofar shigowa don ya saka zakiyya ta hado mashi naman,da madarar daya shigo dasu ta kawoma malik nashi taje ta dauko na Abdoul din.daidai shigowarta yace"gata nan ai kaga kuwa duk wanda zai kira na musanman bayanta yake"
Mamaki ya kashe malik baidaice komi amman yasan tabbas akwai abunda ya faru tsakaninsa da safiyya,kuma zaiso yaji koma miye.

Jawo table tayi tana dora komi asama fuskarta kadaran kadahan,yana dan murmushi yace"bakiji ba hajiyata"
Jiyowa tai tana kallonsa yadaga girarsa yace"eh ban gama dake ba pls sit here"
Yana jawo dayar kujerar dake gefensa ya nuna mata,kallon malik tayi asace yayi kamar bai gansu ba,tadan jima kafin ta zauna.malik hakanan yaji abun bai mashi ba,ransa baimai dadi ba amman zaisan mezai.
Tashi yayi da tashi system din yana ficewa.

Rubda ciki tayi tana kuka mai sosa rai,hakika so masifa ne idan bakai dace da wanda kake son ba,tabbas kalar tata soyayyar idan banda wahala da ciwon xuciya babu abunda take haifarwa............amman tana so tasan dalilin yin fushinsa don kurin tace tana bata sonsa,bata ra,ayin auren kalarsa.duk da kalamanta sunyi tsauri tayine don ta gano ko yanajin makamancin halin da takejin kanta akanshi,ashe kwaba tayi bata sani ba.........hakika dole xai fushi saboda kalamanta amman ai yayi mata uxiri,tana mace ba kimarta bace furta tana son sa,hakan bai dace da ita ba.
Chapter 66 · 0% Book details