← Book details Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 87

Sashe 30

Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wajene ta tanadar masu Mai tsananin kyau da burgewa,kuma wajen is save zasuyi maganarsu cikin sirri babu Wanda zaijisu ko yasa musu ido.
Zama fiyah tayi tana ajiye jikkarta agefe,ta tsurama zakiyya ido tana kallo tana sake karantarta tsaf.
Zakiyya zaman tayi itama Amman gabaki daya fuskarta ta canza babu wannan walwalar da tazo da ita afarko.
Hannu tasa tana dafeda fuskarta natsayin wani lokaci kafin ta iya dagowa tana cewa cikin sanyin murya.
"Bari akawo maki a bun ta'bawa ko."
Cikin kulawa tace"Aa zakiyya,kibarshi har nakoma gida ban bukaci wani abunba,yanzu dai ga pos dinki duba kiga komi dakika San yana ciki yana nan yadda yake."
Murmushin karfin hali tayi tana cewa"bama sai na duba ba nayarda dake gani nafarko dake,nasan bazaki cuceni ba."
Murmushi fiyah tayi tace"karkiyi saurin yarda dani taya kikasan bazan cutar dake bah."
Ajiyar xuciya zakiyya taja tace"nasan ki ai,sunanki ne kurin ban rikeba Amman yadda nasan gidan dakika fito ya tabbatar mun bazaki cuceni ba,duk da ganin danayi maki baiwuce uku ba."
Cikin mamaki fiyah "inakika sanni."
Dariya tayi tace"nikinga banzanyi mamaki ba da kika sanni,dafarko nayi lokacin dakika kirani,Amman ganina dake yasa mamakin yafita,don unguwa daya ba wasa bace gidanku yana opposite danamu kohar yanzun kina mamaki."
Jinjina Kai tayi tace "nabar mamakin yanzu ai"
Shiru sukai fiyah tana jinjina halin kirki da rashin wulakanta mutane irin na zakiyya,Sam batayi Kama da yangidan masu kudin dasuke wulakanta Wanda sukasan kasansu Yakeba.
"Kince zamuyi magana dake,tundaga ranar hankalina baisake kwanciyaba har yanxu,sonake naji abunda kikeson muyi magana akai."
Sadda Kai fiyah tayi tace"inhar kinyi amanna dani cewar bazan cucekiba, zakiyya kiyimun alkawarin cewar duk abunda nake da bukata zaki fadamun gaskiya."
Kallonta take tana nazarinta kafin ta iyacewa"mezai hana,ai koda kingujeman gidanku bazai gujemun ba,balle nasan ba zaki yi abunda zasakani cikin damuwa bah."
"Karkiyi saurin cawa haka zakiyya,don kuwa abunda nazo dashi zaijefaki cikin damuwar da wata kila kinyi bikin binneta cikin ranki,abunda nazo dashi zaifama maki wani ciwo da kikatabaji cikin ranki,Amman Ina maitabbatar maki yadda na fama makishi haka insha Allah zanwarkar maki dashi ki bani yardarki da kuma amanarki."
Cikin dokantuwa dason jin abunda fiyah tazo dashi zakiyya tace"kin sakamun kwadayin jin wannan lamarin,koma miye nayi maki alkawarin baki yardata dakuma amanata,nabarmaki wuka da naman,don nayi imanin kinfini sanin yadda zakiyi dani."
Gyara zama fiya tayi tace" I know kinsan *ABDOULNASSER MUAZZAM CANJI*"
wata irin razana da gigita ce tashiga zakiyya,yayinda dandanan kwalwarta tashiga yomata tariyar duk abubuwan dasuka wuce abaya,tsawon shekara shidda kenan.
Dandanan idonta yawanke fuskarta DA ruwan hawaye,zuba kawai sukeyi babu kakkautawa........har lokacin idonta yana kan fiyah hannunta tasaka tana rufe bakinta,Wanda kukan dake tahowa zai iyajawo hankalin mutanen wajen Kansu.
Fiyah batayi yukurin dakatar da ita ba don so take ta yi kukan tagama sannan sucigaba da maganar.
Kwantar da kanta tayi bisa table din wajen tana kuka sosai maitaba zuciya,magana take cikin kukan ta na cewa"Ina kikasansa?Ina kikasan indayake rayuwa don Allah,hakika yau kin tayarmun da mikin da kullum nake dannesa cikin raina,Abdoulnasser shine duk wani farincikina shine duk wani burina,Zan iyace maki magabaki daya shine jigon rayuwata............Amman rana guda lokaci guda komi yawargaje komi yalalace,yabarni nabarsa alokacin damuke tsakada tsananin dokin juna da bukatar juna.
Abdoul shine haskena dake haskaka duniyata,shine Wanda idan inacikin duhu yake haskakamun gabana.Amman nawayi gari babushi banajin muryarsa,ba ganinsa wani abunma dazai tuna mun dashi Ana kokarin ganin annesantani dashi........kiyiwa Allah da manzonsa kigayaman wajen Da ABDOUL yake.inason sa hargobe bazan iya daina sonsa ba.koda naman jikina za,ayanka zuciyata bazata dakata daga tunaninsa ba,shiyasa sukayanke mun hukincin da ko inso kobana so dole zanbar Abdoul...........kuka yaci karfinta.
gabaki daya jikin fiyah yayi Mata wani mugun sanyi,kwalla sukacika idonta natausayi. Zakiyya Ashe ba tamanta dashiba,hargobe tana nan tana dokon kaunarsa,tana renon soyayyarsa taya ni Safiyya Zan iyaceto da wadannan masoyan masu tsananin begen juna.
Na tabbata yadda zakiyya take cikin wannan yanayin na shauki da begensa haka shima yanajin wannan feeling's din,saidai taurin xuciyarsa da kafewa bazai barshi asan DA haka ba.
Kukan yayi kasa sosai tana shashshekar kukan kasa kasa,
Wannan lokacinne fiyah ta Fara magana cikin natsuwa da furta kalma dalla dalla.
"Sunana safiyyah kabir El-ladan wadda mutane sukafi kira da fiyah...........ta zayyane Mata tas tushiya mafarin dawa,daga lokacin da ta hadu dashi sanda akaban keshi tatasho makaramta,zuwa sanda sukai rigima da feea da mafarin shigarta rayuwarsa komi ta zayya nema zakiyya,wadda kukanta yadawo sabo jin halinda masoyinta abun kaunarta yake ciki.
"Nasha wuya,konace inacikin shan wuyar akan lamarin Alfah.don yadda yake da xuciya tunkararsa wani tashin hanakine,badan Allah yakiyayeni ba zakiyya Abdul karya kafafuna zai tas.Amman nima inada tawa kafiyar idan nasa kaina Abu,shiyasa duk abunda yakemun nake shanyewa,tunda har malik yajure abunda yake yi nima naji Zan jure.saida nafetsare idona na fitsare kafafuna sannan lamarin Abdoul Allah da ikonsa yafara dawowa cikin natsuwarsa,Amman har yanzu da saura.zakiyya banda wani buri daya wuce na maido ma mami d'anta,na dawo maki da masoyinki na dawoma Da ABBI dansa.Wanda malik yaban labarin rayuwarku dana soyayyarku,amman haryau basu san farin wannan tashin hankali ba.......da nazauna nayi tunani nayi dogon nazari naga cewar,babu Wanda Zan iyatunkara da wannan maganar na tsira saike dubada tsarin soyayyarku da kuma yadda abun yazo kema bada son rankiba."
Tana kuka tace"wlh fiyah bada son raina ba,Allah shike ganin xukatan bayin sa na tabbata yaga tawa xuciyar ban so ba.........."
Katseta fiyah tayi tace"nayarda zakiyya bada son rankiba Amman da saninki,kinsan komai duk wata kullallaiya da kunshe kunshe kinsani kuma dake akai,anyi anfani da karfin iko an jaki ciki kuma kin aikatan."
Tana kuka sosai tace"fiyah,wlh duk hasashenki haka yake ba aikin kowa bane sai na mahaifiyata umma da yaranta,saboda kiyayyar da sukewa Abdul da mahaifiyarsa............."ya isa naji wannan zakiyya,Amman yanzu matsayin ki na masoyiya wadda Abdoul yaso soyayya Mai inganci,wace irin gudunmawa zaki bashi kasancewarsa cikin wannan halin,sannan nasan kece wadda Abban su feea zai Aura watau Alh kwangila,kuma basai na tambaye ki ba nasan bakison wanan auren akwai dalilin kullashi ko nayi karya."
Share kwallarta tayi tace"bakiyi ba fiyah,tabbas aurena da Alhaji kwangila duk shirinsune shida umma ta........muryarta tayi rauni sosai tace"wlh safiyyah Ina bakincikin halin da umma tajefa kanta kuma tajefa mu,Alh kwangila dadiron umma ne Abdoul ne ya tab'a ganinsu sau daya,mafarin suka Fara shirya masa tuggu.daman ga kiyayyar da suke mashi sai a bun ya zame ma shi biyu.Zan sanar dake komi Safiyya don kuwa nasan zaki taimaka mun,kuma bazaki Bari Abdoul ya wulakanta ba,Amman Zan so kiban lokaci zuwa jibi sai musake haduwa zanzo da abun recording kidauki duk hirarmu,koda bayan raina nasan Abdoul ya wanku mutanen dake masa kalon dan iska mashayi zasuzo suna dasun Sani."
Cikin jin tausayinta tace"zakiyya mezai tsayar damu har jibin,karki manta aurenki fa sake matsowa yake."
Tace"haka ne,inason binciko wasu abubuwane,domin ahalin yanzu umma a bun tsoroce safiyyah.akwai abunda suke shiryawa ita da yaranta zuwairat DA Ameenah DA haulat.
Khadija ce kurin shiryayya,itama bayan barin abdoul Naringa janta da nasiha da kwatanci har nayi nasarar jawota jikina,yanzu so nake nasan mesuke shirya wa Wanda zan recording komi nabaki ajiye."
Jinjina Kai safiyya tayi tace"wannan ma dubara ce,Amman inajin tsoron kar suganeki suyi maki wani abu."
"Ai yanzu sun dauka na mance da komi,nashiga cikinsu,ganin na anshi auren hannu biyu ban nuna kiyayyata dashi ba,ina anso masu kudi wajen Alh sunayin yadda sukeso.
Daman nashirya daukar recording komi naje naba mami mahaifiyar Abdoul.don nayi alkawarin Ana gobe daurin aure Zan gudu inshiga duniya."
Sai gashi Allah ya turo Mani ke,naji dadin hakan kuma naimaki alkawarin baki hadin Kai dari bisa dari,koda Abdoul bai auran ba nayi abunda ya dace."
Fiyah tace"balle ma insha Allah nadauki nauyin wanan cikar burin naki zakiyya."
Kallon agogo fiyah tayi tace"inason naje na ga malik,inkoma gida da wuri kome kenan zakiyya zamuringa waya kafin jibin.
Rungume juna sukai suka nufi motar zakiyar wata dankareriya tace"Alh kwangila yasiya mun,saboda farin cikin zan auresa mafarin fa yasaki matarsa uwarsu rafeea."
Fiyah tace"ta gaya mun shiyasa ai na zage insha Allah aniyarsu zata koma masu."
"Muje na kaiki gidan inma zansamu ganinsa."
Murmushi fiyah tayi tace"zakigansa harma saikin ringa korarsa"
Dariya tayi tana tukin ta na cewa"Allah ya nuna man wannan rana."
Fiyah tace"Amen summa Amen tanajin wani abu yana yin raga ragada zuciyarta da ruhinta.

*plssss sorry kwana biyu kunji shiru wlh banda lfy ga ciwon ido I need ur prys*
Ina alfahari daku masoyan ABDOUL-NASSER ALFAH.

MRS BB CE
MOM MUHSEEN.
09034722970
[9/17, 3:38 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

_WANNAN PAGE DIN KYAUTANE GAREKU ALFAH FANS,KUYI YADDA KUKESO DASHI MALLAKIN KUNE SABODA IRIN KAUNAR DA NAKE MAKU_😊💞💞💃

🅿️.........26

Zakiyya ta sauke fiyah tajuya badan ranta ya so zata tai ba,saidan batasan mezata yiba kuma tafi bukatar indan komi ya bayyana sai su hadu alokacin zata gane cewar idan yana kan turban soyayyarta kobaya bisa,Amman yanzu tabbas idonsa yasauka akanta tashiga ukunta yadda taji fiyah tana gaya Mata yadda Abdoul yakoma yanzu saurin fushi dazafin xuciya.
Kwallarta tashare tafurta"kayi hkr masoyina bayadda na iya da mahaifiyata muddin nace zan Saba Mata ratuwata zata lalace,hakika nayi kuskure abaya da har bari akai anfani dani wajen lalata maka rayuwa Abdoul,Amman yanzu kam ko hakan zayyi sanadiyyar rayuwata wlh saina bayyana gaskiya domin maidomaka da hasken rsyuwarka daya disashe,Abbi yana cikin tashin hankalin rashinka Abdoul,bazai dai iya fitowa fili yanuna ba,don bala,in umma bazai barshiba.nayi imanin cewar duk randa kasan cewar abunda Abbi yayi maka bayacikin hayyacinsa zaka mashi uziri,zaka hucedaga kullatarsa dakai.insha Allah muddin Ina numfashi cikin ikon Allah komi zaizo ya warware."
Hawaye takeyi natausayin kanta DA shi kanshi abdoul din.
(Nikau nace bakisan YAN ALFAH FANS suna can suna kare maki tanadi😂😂)
Chapter 30 · 0% Book details