← Book details Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 87

Sashe 6

Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*wlh saboda ku yau banci abincin rana ba sai la,asar kuyi manage pls,sannan inhar banga comment 70% ba gaskiya zan dakata da typing,don haka na nuna bakwa jin dadinsa.*

Mrs Bb
Mom muhseen. Lov u all masoyana😘😉
[9/17, 3:35 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

🅿️.........6

Runtse idonta tayi ta bud'e tace"Aa mamana,babu abunda nake boye maki kawai dai banjin dadi ne kwata-kwata."
Yesmin duk ta koma kalar tausayi don jin halin da yayarta ke ciki.
Wayar maman ce tayi kara yesmin ta dauko ta tana cewa"wlh Anty ce ai daman nasan tunda kikace bakije ba wlh saita kira."
Mika ma maman wayar tayi tana zama kusada Addarta.
Daukar wayar maman tayi tare da sallama.
"Mama ina fiyah,wlh ranta sai yayi mugun b'aci yesmin bata gaya mata sakona ba."
Shiru maman tayi har saida ta gama sannan tace"sallama ta ma bazaki ansa ba jamila zaki hau yimun sababi,ko nice sofiyyar ne ban sani ba."
Cikin tausasa murya tace"Aa mama ba haka bane kiyi hkr."
Itama cikin d'an fad'a tace"aikin tambayi dalilin rashin zuwanta bawai kihau yin fad'a ba,."
Sake kwantar da murya tayi tace"to mama kiyi hkr don Allah,meyasame ta ina take ban ita."
Fiyah na kwance har lokacin kan cinyar mamar idonta lumshe eyelashes dinta sun wani kwanta gwanin sha,awa tunani take ta yadda zata shiga rayuwar *ALFAH* taji waya kan kunnenta maman ta aza mata.
Cikin cool voice dinta tace"Anty ina wuni."
Daga can ita ma face"lafiya lau fiyah,lafiyarki kuwa naji muryarki tayi sanyi sosai."
Gyara kwanciyar ta tayi tace"Anti kiyi hkr wlh nataso banda isassar lafiya,kaina naciwo ga gajiya shiyasa ban biyo ba,amman insha Allah gobe ina nan zuwa."

Ajiyar xuciya ta sauke tace"daman muhseen ne yake son kuyi bankwana zai koma spain,yama tafi aman yabar sak'o abaki."
Haushi taji ya kamata yadda Antyn ta matsa mata akan wani muhseen,itafa bata ra,ayin wannan guy din mai shegen yangar tsiya kamar mace,ta gode Allah ma daya tafin.
"Toba ma saina zo ba kenan."
Cikin fad'a tace"ban son iskanci bacin kinji nace maki yabar sak'o,to mezanyi dashi in baki zo kin ansa ba."
Dariya tayi k'asa k'asa tace"to zanzo goben insha Allah agaida man uncle da onborn baby."
Ta fad'a tana dariya.
Tace"marar kunya kawai zakizo ki saman."
Tana dariya ta kashe wayar.
Antynsu akwai zafi itada yayansu jalal,ga saurin hagula,dan danan zaka bata masu rai amman dan danan zasu sauko,daga mamansu har baban su babu mai tsananin su,suma wajen kakanni suka gado.
Itada yesmin kuwa sanyin su har yakusan yawa,amman ita fiyah akwai lokutan da takeda zafi,zafinma sosai amman tana daukar lokaci baka ganta cikin irin wanan yanayin ba.

💞💞💞💞💞💞💞

Tun da suka shiga cikin gidan Alfah ya zube cikin falon yana wani irin huci na ban tsoro,malik ya rasa gaba d'aya natsuwarsa duk ya gigice yana jin wani tsananin tausayinsa yana cika zuciyarsa,bai wuce abunda ya faru tsayin shekaru ba yake dawo mashi sabo,saboda aduk sanda akai wani abu daya tuno mashi abun,ko yaga wani nashi ko wanda abun ya shafa,to fah wannan halin yake kasancewa cikinsa,koma fiye da haka........tunaninsa ya katse jin sautin kukan sa kallonsa yayi cikin tausayawa jin yadda yake kukan cikin bayyana tsananin kuncin da zuciyarsa take ciki,duk da yana tsoron tun kararsa ahaka cikin wannan yanayin nasa. zuciyarsa takasa hkr ya nufesa shima kwallar cike da idonsa.
Durk'usawa yayi gabansa yadafa kafad'arsa yace"kayi hkr Alfah Allah yana sane dakai............cikin wani irin yanayi na zuciya da fushi ya watsa malik gefe muryarsa har lokacin bata fita sosai yace"hkr,hkr fa kace inyi. bazan ba bazan tab'ayin hkr ba malik,antozartani anci mutuncina an goge duk wani kallon kima da mutunci da masoyana kemun,an yayatani ga media........cikin sarewa ya silale k'asa cikin shashshekar kuka kamar ransa zai fita ya cigaba da magana wadda ba sosai kakejin taba muryar ta dishe sosai cikin kuka da tarin kunci yace.
"Suka Koran,sun aibatani sun zagan sun wulakantani sun lalata man carria,sun lalata sunana duk inda na shiga k'yamata ake aibatani ake,zagina ake babu maisona........malik babu maisona duniya ta tsaneni duniya na mun kallon fasik'i,wlh malik niba fasik'i bane ban fab'a ba bazan tab'a ba kayarda niba d'an iska bane kamaryadda sukace ko,?kayarda ni mutumen kirkine ko?"
Malik kuka yaci karfinsa isowa inda yake yayi ya rungumeshi yana kuka iyakar karfinsa shima ya matseshi kamar zai ballashi tare suke kukan kamar yanzu abubuwan ke faruwa.
Cikin kuka malik yace"kai mutumen kirkine,kai ba dan iska bane kai ba fasik'i bane ABDOUL-NASSER kamilin matashine,natsatstse mai addini mai girmama nagaba dashi,burinsa shine ya tallafawa masu karamin karfi,mai biyayya g iyyensa..........yaja numfashi yanajinsa yana ajiyar xuciya bugun zuciyarsa yana raguwa cigaba yayi da cewa"sharrin macene yaja maka duk wannan Alfah,kaddarsrka tazone ta wajenta karka zargi iyayenka abunda suka gani dashi zasuyi anfani.........fincikoshi yayi daga jikinsa idon nan babu kyan gani yatura shi kan kujera kamar ba shine yanzu yayi sanyi ba.
"Karkasake mun maganarsu,natsanesu ban sonsu har abadan bazan sosu ba."
Malik na hawaye yace"Alfah kagane mana...........bazan tab'a gane wa ba,kafita anan ban son ganin kowa karka sake zuwa inda nake,nagane cewar kaima munafukine baka kaunata nace kafita!!! Yafada cikin ihu da har gagi.
Malik na kuka ya fita ya barshi.
table din glass dake tsakiyar falon Alfah ya dunga duka har saida ya tarwatse,ya dunga boll da duk wasu kaya dake cikin falon,masu fashewa nayi masu watsewa nayi.hankalin malik inyayi dubu ya tashi kuka yake yaciro wayarsa yana kokarin kiran Daddy,tsotsai yasa wajen sauri wayar ta silale ta fad'i aikuwa fuskar wayar ta fashe,..........cikin haushi da takaici ya zube kasa yana dora hannu saman kai.
"Wannan wace irin rayuwace haka,har sai yaushe abubuwa zasuyi sauki,cikin kuka da magiya yake rokonsa,Alfah karka raunata kanka,inbaka son rayuwarka ni inasonta kayiwa girman Allah kadai na."
Amman Alfah baijin ma komi malik yake fad'a saida ya hauka ta falon yajiwa kanshi raunika sosai.
ya zube yana kuka mai cin Xuciya,yanajin wani irin ciwo cikin zuciyarsa jiyake kamar yacirota ya jefar ko zai daina jin wannan ciwon amman kamar tira mashi ciwon ake frig ya nufa ya dauko kwalaben giyarsa ya cire masu hanci yadunga bulbulawa cikinsa,daya shanye sai ya dauko wata itama ya gama mata aiki,atakaice saida Alfah yasha kwalba biyar,amman baiji koda kadan cikin ciwon daya keji yaragu ba,a haukae ya dauko kwalbar daya shanye giyar ya buga ta da kasa ta fashe,ya dauki b'allin kwalbar ya saita jijiyar hannunsa zai yanke yaga hakan bai mashi ba,ya jefar da kwalbar yafasa wata irin kara yabuga kanshi ga bango sai gashi ya xube kasa babu numfashi.

💞💞💞💞💞💞

Da dadare bayan sun gama cin abincin dare wanda har lokacin fiyah bata daidai taba,gata nan dai kadaran kada han ko baban su saida ya tambaya ko tana lafiya tace kanta ke ciwo amman tasha magani yayi sauki.
Bayan ya gama cin tuwonsa yafita waje wurin d'alha da radion sa ga hannu.
Hira suke cikin gidan yesmin ce keta ba mama labarin yadda jara barawar su ta gobe zata kasance masu,fiyah dai tayi lamo gefe tana sak'awa tana kwancewa tab'ota mama tayi tai firgigi ta juyo tana kallon maman.
"Sofiyya,kallan ninan bazaki iya boye mun damuwarki ba saboda yana yinki ya nuna cewar damuwar babbace,kuma tana damunki matuk'a don najima ban ganki cikin wannan yana yin ba,don haka maza gaya mun abunda ke damunki yanxu nan."
Raurau tayi da ido zatai kuka don bata san taya zata gaya ma mama abunda ya faruba,amman dole zata boye wani abun don tasan makamar abunyi.
Cikin dakoya da kokarin boye abunda ke ranta "tace mama bafa wani abu bane kawai dai wani abune daya faru yake daure man kai tunda abun yafaru duk nakejin babu dadi."
Duk natsuwa sukai suna saurarenta mama tace "inajinki meye ne Allah yasa ba akan karatunki bane."
Kwanciya tayi jikin yesmin dake gefenta tace"wanine yayi hadari bakin titi,yawwa mama inkin tuna rannan wanda nace maki ankasa tai makarshi."
Cikin kulawa da maida hankali kan abunda take cewar tace mata"eh natuna sofyna meyafaru bayan nan."
Ta sake mazewa yadda maman bazata gano komi ba tace"wlh mama abunne yaketa damuna tun rannan to yau naga mutumen kamar wani mahaukaci bakin titi yaci kwalar wani mutun daker aka kwaceshi,ni mama sai nake ganin kamar nasan shi wlh,kuma abunda yaban tausayi gareshi mutane sun zagayeshi sai duka suke ga wani Alhaji sai tijara yake yana zaginsa maganganu marasa dadi hada ce mai wai iyayensa ma sun gaza dashi balle wasu,abun dai babu dadin ji wlh harfa cemai yake dan iska fa mama.wlh yaban tausayi ya kira yan sanda suka tai dashi.
Naji mai taxi din daya taho damu nida wani yana cema wanda ya dauko mu tare wai kowa yasan shi dan iskane kuma da iyayensa masu hali akwai abunda yayi suka korai."

Shiru mama tayi tana jin abunda fiyah ke sanar da ita taso d'ago wanda take maganar kanshi amman bata tabbatar ba,cikin kulawa tace mata"dawa kikace yake maki kama."
Aranta tace yawwa anzo wajen don daman so take tasan dagaske dan gidanne kuma me ya fiddashi inhar dan gidanne.
"Mama yama sunan wancen mutumen mai kudin unguwar nan,uhmmmm yesmin yama ni wlh mance sunansa nake ma saboda mugun halinsa."
Tayi hakane don ma kar mamar tagane dagangan tayi haka........cikin sauri yesmin tace "nagano shi wlh,mu'azzam canji tabbas sunan kenan ko mama."
Wani irin kallo mama kewa Fiyah cike da tuhuma ganin haka yasa fiyah takiyarda su hada ido da maman don tabbas idan suka hada ido tasan zata gane karya tasheka mata do dai ta samu wani bayani.

More comment more typing.

Mrs bb ce
Mom muhseen.
[9/17, 3:35 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

🅿️.........7
Chapter 6 · 0% Book details