← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 100

Sashe 98

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba ta son rakiyar sai dai taga kamar ko ma ina zai je ba dadewa zai yi ba, sannan kuma ba zata iya yi masa musu ba saboda yanda tayi kewarsa kuma bata son ta bata masa rai don ta kula yana tare da damuwa. Don haka ta amsa ya sakata a gaba suka fito.

Suna fitowa daga office din yace ta bar motarta a nan idan sun dawo sai ta dauka, don haka suka shiga motarsa suka wuce.

Yana tuki suna hira, nan da nan suka iso BON hotels, Kano. Ya shiga ciki yayi parking yayinda take binsa da kallo mai cike da tambayoyi. Yayi murmushi yace

'Fito muje, wani zan gani sai mu zo mu tafi.’

'To ka je mana sai na jiraka a nan.’

'No, fitowa zakiyi mu je.’

Ya fito yayinda itama ta fito ya rufe motar suka shiga hotel din.

Daga baya-baya ta tsaya don haka bata ji abinda yake fada ba a reception, ya gama aka bashi wani kati ya juyo ya ja hannunta suka shige ciki.

Binsa kawai takeyi tana mamaki; to wanda zai gani kuma a daki zasu hadu?

Kafin ta gama tunanin sun tsaya a bakin kofar wani daki, nan da nan yayi amfani da katin da ya karba a reception ya bude kofar dakin. Ya shige ciki yayinda ita kuma ta dan noke, ya juyo ya jata ciki ya rufe kofar. Ta zazzare ido tana fadin

'Kuma sai na shigarwa mutum daki?’

Yayi dariya

'Babu kowa a ciki to.’

Sai da suka zo tsakiyar dakin ya saketa, ya karasa ya ajiye mukullan motarsa da waya a kan mudubi, ya juyo ya dawo ya tsaya a gabanta ya kama hannuwanta yana fadin

'Bari muyi sallah ko?’

Ta marairaice tace

‘Don Allah me zamu yi a nan kuma?’

Ya dan kara matsawa daf da ita yanda yana jin dumin numfashinta, ya saki hannunta daya ya dago habarta suka hada ido. Ta sunkuyar da idonta. Ya sumbaci lebenta sannan ya kai bakinsa daidai kunnenta yace

'Ki kwantar da hankalinki, ko yanzun kuma ni kike tsoro?’

Ta dan ji kunya don bata zata tsoron da take ji ya bayyana a fuskarta ba, yayi murmushi yace

'Aisha na gaji ne da yawa kuma da zan iya samun hutu ni kadai da ba zaki ganni haka ba har ki dinga tambayata ko bani da lafiya. 2 hours kawai zaki bani zaki ga na warke. Ai zaki iya ko?’
Ba zata iya ce masa a'a ba saboda yanda yake mata maganar da salo na magiya da lallashi, sannan kuma ita kanta tayi kewarsa kuma ga hakkinsa na aure a kanta wanda ta san dole ta saukeshi. Don haka tayi murmushi ta daga masa kai alamar eh.

Cike da farin ciki yace

'Good! Bari muyi Sallah tunda lokacinta yayi.’

Ya shige bandaki ya barta tana karewa dakin kallo.

Ta gama kallon dakin sannan ta zauna a gefen gadon, ta zaro waya ta kirawo Anti Uwani ta sanar da ita kada suga ta dade bata dawo ba sun fita da Abban Sadik. Kafin ta ajiye wayar aka buga dakin aka ce room service ne. Ta mike ta bude kofar a hankali, ma’aikatan hotel din su biyu suka turo dan teburin nan mai taya da abinci kala-kala a kai suka ajiye mata suka fice. Abban yana fitowa itama ta shiga tayo alwala. Sai da suka idar da sallah sanna suka zauna suka ci abincin suna ci suna hira cike da walwala. Yanda yake cin abincin yasa ta dube shi da tausayi tace

'Wai ba kayi breakfast bane?’

Ya dubeta yace

'Hmm! Nayi breakfast. Kawai dai na dade rabon da na ci abinci a nutse kuma naci na koshi shi yasa yunwa tayi min yawa. Yanzu kuwa inaa ci kina min hira ai dole na ci na koshi.’

Tayi dariya.

Bayan sun gama cin abincin ta tashi ta wuce bandaki ta wanko hannu, tana tashi shima ya bita. Suka wanko hannu a tare suka fito.

Suna fitowa ta nufi gefen gadon zata zauna, ya karaso kafin ta zauna ya sha gabanta. Ya kama gefen laffayar da take jikinta wadda ta ki cirewa tunda suka shigo yana fadin

'Ai sai ki cire wannan nadin ki huta tunda ba yanzu zamu tafi ba ko, nifa bacci ma zan yi kuma dai ai kya tayani ko?’

Tana ji tana gani ya warware laffayar, yana ajiyeta a gefen gadon ya kare mata kallo daga ita sai straight skirt na atamfa da kuma bakar riga irin fitted dinnan mai kamar roba ta bi jikinta duk ta kwanta. Kamar a can kasan makoshinsa yace

'Nace ki daina fita da wannan fitnanniyar rigar fa, ai gara ma da hijab kika sa.’

Kafin ta bashi amsa ya fara sumbatar wuyanta.

Haka ta biye masa yayi yanda yake so, sai da ya dauki lokaci ya gamsu sannan ya gyara kwanciya ya jata jikinsa ya rungumeta. Kafin tayi wani yunkuri bacci ya kwasheshi, ta duba agogon wayarta sannan ta dan gyara kwanciya ta lumshe ido itama bacci yayi gaba da ita.

Itace ta fara farkawa wajen karfe uku da da rabi, ta yunkura zata zare jikinta ya riketa yana dariya

'Ina zaki je?’

Ta koma ta langabe tana fadin

'La'asar fa ta kusa, ai gara muyi wanka mu tafi.’

'Um.'

Ya rufe bakinta da nashi bakin yayinda ta fara kokarin ture shi, sai dai kafin ta samu ta kwace ya ci karfinta haka ta sake biye masa.

Sai da hudu ta gota sannan suka tashi suka kintsa sukayi Sallah suka kamo hanya. Suka koma office din sa don ta dauki motarta. Ya karbi mukullin motar ya bawa Malam Sule yace ya kai mata gidansu suma zasu hadu a can, ita kuma yace ta zauna shi zai kaita ya gaida Hajiya.

…………

Yana ajiye Aisha a gida magriba ta kusa don haka kai tsaye ya wuce gidan Yaya Bello. A can ya tarar da su Yusra gaba dayansu don tun tuni Malam Ali ya kawosu.

Bayan sun gaisa Yaya Bello ya dubeshi yace

'A'ah! Ashe ba alhinin mutuwa ne ya sa ka fita hayyacinka ba tsoron kada ka rasa Aisha ne, daga jiya mun je an ce zata dawo shine har kayi kiba kana sheki haka?’

Yayi dariya yace

'Haba dai wallahi ba haka bane Yaya.'

'Ai kuwa ko ka ki ko ka so hakane. Inaga dai nima auren nan zan kara ko na danyi kyan gani.’

Umman Muhammad da take jiyosu daga kitchen ta yiwo gyaran murya. Suka tuntsire da dariya. Abba yace

'Ai ki barshi Umma babu wadda zata aureshi sai ke, daga ke sai shi har Aljanna.’

Daga can tace

‘Ina dai jinku.’

Suka cigaba da hirarrakinsu.

Ana yin kiran Magriba Abban yayi musu sallama suka wuce masallaci da Yayan inda daga can yayi masa sallama ya koma gida.

_

Ranar Talata da safe ma'aikata suka zo, nan aka fito da kayan cikin gidan gaba daya har kujerun Abba yace a fito da su a hada da gadon dakin Zahra a sayar a rabawa magada kudin. Duk wasu gyare-gyare da zasu yi masa ya nuna musu, har kofa yasa ayi masa daga dakinsa wadda kai tsaye zata kaishi dakin Aishan.
A gyara bandakuna da kitchen din gidan duka biyun sannan a sakewa gidan gaba daya fenti. Nan da nan aka fara kwaso kayan ana fitowa da su tsakar gidan.

………

A zaune yake a office yana aikinsa, sai ya tuna ya kamata ya kirawo Amina don ya tambayeta ko akwai wadanda suke bin Zahra bashi kuma yayi mata maganar kudin da yaga Zahran ta tura mata.

Nan take ya ajiye biron da yake hannunsa ya janyo waya, ya lalubo lambar Aminan wadda ya kwafa a wayar Zahra. Bugu daya ta dauki wayar tare da yin sallama; bayan sun gaisa yayi mata bayanin kansa. Ta sake yi masa gaisuwa sannan ta tambayi yaran. Ya tambayeta ko akwai wadanda suke bin Zahra bashi a kawayensu, ta tabbatar masa babu wanda yake binta bashi. Sannan ya tambayeta bayanin kudin da Zahran ta tura mata har naira dubu dari biyu da saba'in. Ta dan diririce sannan a hankali ta janyo nutsuwarta tace

'A'a daman wasu kayane fa da ta siya, kuma ta riga ta karbi kayan tun kafin ta rasu don tana turo min kudin ma na turawa mai kayan.’

Ya amsa suka yi sallama ya ajiye wayar yana mamakin ta.

Daga jin bayanin da tayi ya san karya takeyi sai dai kawai ya kyaleta saboda baya sha'awar ya daga zancen balle wani yaji kudin na menene aka tura.

—-----

Duk yanda ya so a gama aikin gidan nan a sati biyu abun bai yiwu ba, domin ko fitar da kayan ma sai da aka dauki kusan sati ana yi.

Don haka lokacin da sati biyu ya cika da kansa yaje har gidan Baffa ya sanar da shi ba'a gama aiki ba sannan ya je ya sanarwa Hajiya ma.

_

Sai da aka dauki sati hudu ana aikin gidan nan sannan aka kammala. Don haka a farkon sati na hudun ranar asabar da safe Abba yaje gidansu Aisha don ya dauketa su je su yi sayayyar furniture.

Tun kafin ya karasa kofar gidan yayi mata waya don haka kafin ma ya gama tsayar da motar ta fito. Ta bude kofa ta zauna a gaban motar, tana rufe kofar motar kuma ta fara gatsina fuska yayinda yake kokarin jan motar. Da hannu ta fara yi masa alamar ya tsaya ta bude kofar motar ta zuro kanta sai amai. Ya dafe bayanta yana yi mata sannu, ya dauki ruwan roba a gefensa ya mika mata. Bayan ta dauraye bakin ta dubeshi tace

'Bana jin dadi kamar ma nace mu bari sai gobe.’

'Me yake damunki?’

'Malaria ne. Na ma fara shan maganinsa tun jiya da daddare, to kasan maganin ma ba dadi gareshi ba.’

Ya mika hannu ya rufo kofar tata ya karya kan mota yana fadin

'Bari dai muje asibiti a duba ki.’

'A duba me kuma? Ai da ka bari idan na shanye maganin ban warke ba sai naje.’

'Kiyi hakuri muje.’

Ta kwantar da kanta a jikin kujerar motar tayi masa shiru suka nufi asibiti.
Chapter 98 · 0% Book details