← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 100

Sashe 8

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya dago ya dubeta, ta cigaba

‘Dakin kasa za a gyarawa amaryar mu fara kwashe kayanmu ko kuwa wani dakin za ayi mata.’

Ya ajiye kofin shayin da yake hannunsa yana murmushi yace

‘Saurin me kikeyi ne? Ko har kin fi ni zumidin kanwar taki ta zo.’

Tayi murmushin yake saboda yanda taga kamar maganar ta saka shi nishadi, ta juya kai ta amsa

‘A’a! Wai saboda na fara kwashe shirgina daga dakin a hankali ba sai an tsaya a kaina ba.’

‘To ki kwantar da hankalinki ki kara baje shirginki ba nan zata zauna ba, ina dai duba wani gidan a nan kusa wanda zan saya sai ta zauna a can.’

Mamaki ya bayyana a fuskarta.

‘Au! Amma dai ba wata matsala bace ta sa za kayi hakan ba ko? Tunda ka ga nan din ma da zai ishemu kuma ni ka san bani da matsala da hakan.’

Ya ajiye kofin shayin a kan teburin gabansa bayan ya kurbe shayin sannan ya bata amsa

‘Babu wata matsala, kawai dai ita din ta fi son haka ko kuma akalla ta sami complete apartment nata wato daki, bandaki, falo da kitchen; kin ga kuma idan ta zauna a nan daki kawai zata samu sauran duka hadaka ne.’

‘Um, lallai! Ai ko dai da ka hade mun ko babu komai kaji motsin mutum ma rahama ne. Da nan zata zauna ai ko mu sai mun fi samun natsuwa tunda ko dai ba kwanana ba kana cikin gida tare da iyalanka gaba daya.’

‘Wallahi, nima hakan naso amma dai ita bata son hakan sai dai ko zuwa nan gaba kafin ayi auren mu gani.’
‘Um.’

Sukayi shiru yayinda Abban Sadik ya cigaba da duba wayarsa da take hannunsa, Zahra ta gyara kwanciya ta rufe ido kamar mai bacci saboda bata son ya sake yi mata magana don ya gama bata haushi; tun kafin ma yayi auren har ya fara sauraron yarinyar da zai aura tana tsara masa yanda za ayi, yarinyar ma da yace bazawara ce ba budurwa ba.

Ita bata son ya raba musu gida; in dai har dole sai ya kara aure to ta fi so ya ajiye su gida daya da duk matar da zai aura. Gani takeyi kamar idan aka raba gida cutarta za a dinga yi, a kaiwa amarya abinda ba a kawo mata ba. Ta fi so su zauna tare ta dinga kula da motsin mijinta. Duk da ta san auren ba zai yiwu ba kamar yanda Mallam ya gaya mata, amma dole ta shirya don idan auren ya yiwu gaskiya dole ya hadesu don bazata sallamawa wata bazawara miji ba.
Haka har bacci ya kwasheta.
…….

Yau saura sati biyu daurin auren Aisha da Yusuf, tuni ake ta shirin biki ana sayayya a gidan su Aishan. Sai dai a yawancin lokuta bata bada hadin kai, don haka Zainab, Zuwaira da Hajiya sune suke ta shirinsu. Ta dai zabi gado mai matukar kyau da yake Baffa ne ya turo hotunan yace ta zaba, amma daga wannan duk abinda aka tambayeta sai dai kawai tace ayi; ta dauki ATM card dinta ta bawa Zainab ta gaya mata password saboda sayayyar.

Haka su Zainab suka gama sayayyar gidan amarya ba tare da amarya ba.

Yau ma Yaya Zainab ce da Zuwaira suka tafi kasuwa domin sayo carpets, babu yanda basuyi ba su tafi da ita amma taki. Tace sune suka siyo labule don haka su siyo carpets din da yayi matching. Don haka suka tafi suka barta a gida inda daga baya Zahida ta zo suka hadu sukayi zamansu.

A zaune suke a dakin Aisha, ita Aishan tana kashingide a kan gadonta yayinda Zahida take zaune a gefen gadon suna hira. Ta dubi Aishan wadda take ta faman danna waya tace

‘Yaya Aisha sai ana maganar aurenki sai kiyi ta basarwa, wai ko bakya son mutumin nan ne.’

Ta dire wayar a kan ruwan cikinta tana 'yar dariya tace

‘To wa ma ya sani ne? Amma fa he’s ok sosai ma, duk wani quality na miji yana da shi. Gashi ba sai na gaya miki ba ke kanki kin san yana so na. Kawai dai ina jin Mustafa ya tafi da rabin zuciyata shi ya sa nake ji kamar na bar muku garin wallahi.’

Ta harareta tace

‘Umm! To in sha Allah sai mun kai ki, komai zai tafi daidai. Allah ya ji kan Abban Abdallah amma babu yanda bawa zai yi da ikon Allah duk yanda kika ga Allah yayi da bawa daidai ne.’

‘Hakane.’

Haka suka cigaba da hirarrakinsu Zahida tana cigaba da kwantarwa Aisha hankali game da auren tunda duk wanda ya sansu da Yusuf ya san yana sonta kuma itama tana sonshi sai dai kawai gaddama irin ta Aishan.

Sai can wajen shabiyu da rabi tayi musu sallama don zata dauko yaranta Nur da Hafsa a makaranta sannan su wuce gida.

UWAR SADDIKU

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

7

Saura kwana goma auren Aisha da Yusuf aka buga kati, da kansa ya kawo mata katin hade da na wuni wanda zatayi a nan gidan Umma sanna yaje ya kaiwa Baffa nasa kuma ya kaiwa Yaya Abubakar ma.

Bai san yanda Zahra zata dauki maganar ba don ya ce mata da sauran lokaci, kuma yayi sa’a Yaya Bello ya bashi hadin kai ko daya zancen bai fito ba. Tun saura sati uku bikin ya kama hayar wani karamin gida wanda gida daya ne tsakanin sa da gidansa da Zahra take, bashi ya kama gidan da kansa ba abokinsa Jafar ne ya kama shi yasa ma ko masu gidan basu san wa aka bawa ba. Da fari ma so yayi ya saya sai suka ki sayarwa sukace na marayu ne haya zasu bayar, don haka aka gama magana Jafar ya biya kudin haya na shekara biyu. Nan da nan aka shiga aikin gayara; ko da wasa bai je gidan ba, Jafar ne a kan komai don amininsa ne tun na yarinta.

Yau da wuri ya taso daga office, yana tuki yana tunanin yanda zasu kwashe da Zahra idan taga katin nan. Baya jin zata bashi matsala tunda wancan karon ma bata bashi matsala ba duk da ta san yana neman aure tunda suka hadu da yarinyar, har aka saka rana bata yi masa wata fitna ba. Abinda bai gane ba har yanzu shine dalilin da yasa ya fasa auren waccan yarinyar.

Har ya karaso gidan yana wannan tunanin da bai samo amsar ba, me gadi ya bude masa gate ya shigar da motarsa ya ajiye a gareji sannan ya shiga gidan. Ita da yaran duka suna zaune a falon kasa suna kallon TV, suka tashi gaba daya kowa yayi masa sannu da zuwa bayan ya amsa ya haye dakinsa dake sama.

Sai da ta dauko ruwa daga kicin sannan tabi bayansa, bayan tayi masa sannu da zuwa ta nemi waje ta zauna.

Ya saba zuwa gidan da envelop don haka ma bata damu ba da taga ya shigo da envelop, kafin ta shigo dakin ya boye envelope din don haka da bata gani ba sai ta cigaba da harkarta.

Saida yaci abinci ya huta, yana kashingide a falonsa na sama yana kallon tashar BBC ita kuma tana zauna a gefensa suna hira ya mike yana fadin

‘Ina zuwa.’

Kafin ta amsa ya shige daki, jimawa kadan ya fito rike da katin daurin aure kamar guda goma a hannunsa. Ya dawo inda ya tashi ya zauna ya jingina da doguwar kujera, ya ajiye katin a gefensa ya dubeta yace

‘Dama so nake na cemiki kanwar taki fa nan da kwana tara za a daura auren.’

Dauke wuta tayi saboda yanda taji kamar ya buga mata guduma a ka, ta yi kokari ta rike nutsuwarta tana yake

‘Wace kanwar tawa kenan?’

‘Ah, ba nace miki zan kara aure ba? To ita nake nufi.’

Ta danyi gyaran murya da mamaki a fuskarta

‘Ikon Allah! Kace zai kai wata shida ko ma fiye?’

Ya dan diririce saboda bai sa ran zata tambaya ba kuma da yanda yaga kamar ta dan shiga damuwa

‘Eh, daman babanta ne zai yi tafiya saboda bashi da lafiya zasu je Egypt ayi masa aiki, shine yace idan na shirya sunaso a daura auren kafin ya tafi.’

Ta kau da kai

‘Um, Allah Sarki! Allah ya bashi lafiya.’

Sukayi shiru na dan lokaci kowa da abinda yake tunani, ya dauko katunan gayyatar da ya ajiye ya mika mata

‘Ga wannan saboda mutanen gidanku, Yaya Muhammad ma dazu na kai masa office.’

Ta karba jiki a sanyaye, ta kalli sunan da kwanan watan ta yi lissafi nan da nan ta gano saura ma kwana taran kamar yanda ya fada. Ta bude baki da kyar ta ce

‘Allah ya sanya alkhairi.’

Ya washe baki yana wani murmushi da yake kara bata haushi

‘Amin ya Allah Uwargida sarautar mata.’

Ta hadiye malolon da ya tokare mata makogoro saboda takaici; wato har ya mayar da sunanta Uwargida ma kenan?

‘To kuma tarewa zatayi ko har sai Baban nata ya dawo zata tare?’

‘A’a, ranar da aka daura zata tare, ai wannan gidan na jikin gidan Bashir na kama hayarsa ina jin ma har an gama gyarawa idan dai ba Jafar yayi min shiririta ba kin san shi na dora a kan neman gidan.’

Wani abu ya tokare mata zuciya a dai dai lokacin da duk wata dama da take da ita ta kwace mata.
A da har ta fara tunanin suna da lokaci Malam ya gama aikinsa ta yanda ko an daura bazata tare ba amma yanzu da yace mata a ranar zata tare tana jin kamar za a sami matsala saboda jiya Malam yace mata akwai aikin da za ayi amma wanda zai yi aikin ya tafi umra sai sati mai zuwa zai dawo sannan ayi aikin.

Da sauri zuciyarta take harbawa; ya za ayi ta iya zama da kishiya bayan itace matar Yusuf ta rufin asiri, sai yanzu da yayi kudi yake jin zai auro wata. Gaskiya sai inda karfinta ya kare, gobe zata kirawo Malam idan babu hali ma zata nemi wani malamin. Ba za a zo gidanta a mayar da ita kalar kwatance ba.

‘Baki ce komai ba?’
Chapter 8 · 0% Book details