← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 100

Sashe 20

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta gane sakon don haka nan da nan ta dauka ta fice.

A falo ta sami Aishan tana zaune tana kallon TV tana shan zobo da cake. Bayan ta sake gaisheta ta mika mata kwanukan tace

‘Wai gashi inji Mommy.’

Bata zata nama bane a tunaninta ko abinci ne don haka tace da Rukayyan ta ajiye a kan dining table. Bayan ta ajiye ta kuma ce mata

‘Ki debo zobo a fridge ki sha, ga cake nan a kan dining table ki dauka.’

Ta shiga ta debo zobon ta fito ta dauki cake din ta wuce ta zauna a kujerar zaman mutum daya. Ta kurbi zobon sannan tace

‘Anti kikayi cake din bana nan, ina so fa na koya Anti.’

‘Kada ki damu in dai cake ne next time in zaki tayani kwana sai mu bi dare mu yi miki na zuwa a school ko? Sai dai fa ina tsoronki a kicin kin yi kankanta fa. Shekarunki sha daya fa, bar ganin kinyi tsawo.’

‘Kai Anti, Allah zan iya. Ai dai kema kin ce ina da natsuwa don haka kin san ba zan yi barna ba ko?’

‘Tabbas kina da natsuwa Rukayya, in sha Allah za muyi cake mai dadin gaske kuwa.’

Saida ta shanye zobon nan suna hira sannan ta tuna da gargadin da akayi mata ta tashi ta fice ta koma gidan.

Bata dade da fita ba Aisha ta tashi ta bude kwanukan, ta bude baki tana mamaki; kada dai ace duk naman nan da aka soya wannan ne rabonta, ko kuwa dai daga makota aka aiko da wannan din.

‘Ikon Allah.’

Ta fada a fili tana mamaki da dariya. A yanka sa guda kato da rago amma a sammata wannan, ai ko su Jummai ta san sun cancanci kason da yafi wannan. Amma dai zata jira tunda yau maigidan a nan zai kwana taji bayani.
Ta mayar da kwanukan ta rufe ta barsu a wajen.
……..

Sai bayan sallar isha’i ya shigo gidan, kamar yanda ya tsira ‘yan kwanakin nan haka ya mike a kan kujerar zaman mutum uku ya fara gyangyadi. Har ta gama jera masa abincin dare ta zo ta tsaya a kusa dashi bai ji motsinta ba; ta rasa gane wannan yawan gyangyadi da baccin da yake mata ‘yan kwanakin nan, sai kace wanda yake kokawa da zaki a office din. Tabbas da ace shine matar da zata ce ciki ne da shi. Tayi gyaran murya ta zauna a hannun kujerar tace

‘Habibi abincin daren fa, ko har kaci a mafarki?’

Ya tashi zaune ya dungure mata kai yana fadin

‘Sai dai idan mafarkinki nakeyi kika bani abincin a mafarki, ba dama mutum ya kashingida sai kice yana gyangyadi.’

Tayi dariya

‘Uhm, to a dai taso aci abinci kafin na cinye abuna.’

Saida suka gama cin abinci suna hira sannan yace mata

‘Dan debo min naman nan mana, Zahra tace ta raba an kawo miki naki ko?’

Ta kalleshi da mamaki tace

‘Au wai wannan shine rabon nawa?’

Kafin ya amsa ta mike ta dauko kwanukan nama ta ajiye ta zauna tace

‘Kaga fa abinda Rukayya ta kawo, wallahi na zata ma daga makota ne.’

Mamaki ya bayyana a fuskarsa yana buda kwanon da robar, yace

‘Wannan din shine rabon naki?’

‘To ni dai shi aka bani. Shiyasa nima na zata daga makota aka kawo. Wannan nama ai ko su Jummai kason su ai ya kamata yafi wannan balle ni, duk da ban san yanda tsarin yake ba.’

Yayi shiru yana mamakin wannan rabo na Zahra, domin ko yanzu da zai fito ya ga nama zai kai fanteka biyar a falon sama kuma ya san akwai wani ma a kicin.

‘Bari idan naje yi musu sallama maji yanda aka yi.’

Nan ya sa naman a gaba, kafin wani lokaci ya ci rabi.
……..

Sai wajen goman dare sannan ya tafi wajen Zahra don yayi musu sai da safe. Babu kowa a falon sai Sadik yana kallon TV yana cin nama da burodi. Bayan yayiwa Abban sannu da zuwa ya amsa ya wuce sama.

A dakinta ya sameta tana kwance a kan gado sai dai ba bacci takeyi ba, bayan ya amsa sannu da zuwanta ya karasa ya zauna a gefen gadon yayinda ta nade kafarta don ya sami wajen zama.

Yace

‘Gajiya ce ta sa kika kwanta da wuri yau?’

‘Wallahi kuwa, duk jikina ciwo yakeyi.’

‘Sannunku da kokari, Allah ya maimaita mana.’

Suka yi shiru na dan lokaci, jim kadan yace

‘Kika ce min an raba nama an bawa Aisha nata?’

Da mamaki ta amsa

‘Eh, Rukayya ta kai mata, sai dai idan shirme tayi.’

‘Bana jin, na dai ga naman ne a ‘yar Samira don ko kafin na fito ma na cinye rabinsa. Duk wannan naman ya za ayi kuma ace wannan ne rabonta, ko ba ke kika zuba bane.’

Ta bata rai

‘Ikon Allah, na kula kai dai idan dai a kan Aisha ne ba zan taba burgeka ba. Gani nayi ita kadai ce a gidan nata, idan ta cinye wannan ba sai ta turo a kara mata ba? Kai kuma ai ga naka can na ajiye maka a dakinka kamar yanda muka saba. Nan fa mu shida ne ni da yara ga masu aiki, baki da danginka duk nan suke shigowa kuma a nan zasu ci ga makota ma duk a nan zan dibar musu. Naman Sallah kuma dama ina yaga wani auki da mutum zai zata zai samu da yawa?’

Binta kawai yake da kallo yana mamaki, so yake yayi mata fada amma ya rasa me ya hanashi.

Cikin sanyin murya ta shafe kwalla daga idonta tace

‘Kayi hakuri idan rabon da nayi bai yi maka ba, ka kwashi naman gashi can a falo ka kai mata ta raba in ya so ta aiko mana da kason mu.’

Ta sake share hawaye tana shirin kwantawa, yace

‘Wannan duk ba abun kuka bane, shikenan a barshi haka. Allah ya maimaita mana. Ni na tafi sai da safe.’

Kafin ta amsa ya tashi ya fice daga dakin, ta bi bayansa da kallo tana mamaki don ta zata fada zai yi kuma sai taga ya fice. Tayi murmushi da ta tuno da aikin da Hajja tayi mata; tabbas aikin ne ya fara ci da ta san baran-baran zasuyi don ba zata bashi naman ba.

Dama tana sane tace a nan za su soya naman don kawai Aishan tayi mata aiki ne don bata isa taci kamar rabonta ba.

UWAR SADDIKU

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

13

Tunda ya shigo gidan ta gane bashi da nutsuwa, bai yi mata maganar naman ba don haka itama sai kawai ta kyaleshi. A nan kan dining table a nan kwanukan da aka kawo naman suka kwana, har ta saka musu abincin safe suna nan bata dauke ba.

Kwai kawai ta soya suka hada da shayi da burodi suke karyawa, suna yi suna hirarsu cikin walwala. Ya dubi kwanon yace

‘Naman nan inaga in na fita zan bawa Malam Sule danyen nama ya kawo miki, sai ki soya ki barshi a nan kya yi amfani da shi tunda ko babu komai naman sallah ai ka bawa baki.’

Da mamaki ta dubeshi

‘Nama kuma, haba dai! Me yayi zafi?’

‘To duk sun rabe wancan naman, akwai dai danyen nama a babbar freezer a can idan zaki yi miya ki dinga turawa a karbo miki. Wanda za a kawo din kuma sai ki soya.’

‘Hakan ma yayi, amma ba sai an kawo wani danyen nama ba. Kasan na gaya maka nayi layya a gidan Umma ko? To wallahi ta ajiye min nama danye da soyayye, don nice ma nace su barshi a can idan naje na taho da shi da tuni an kawo shi.’

‘Zaki dai kwashewa Umma nama, bayan ga naki a nan.’

‘Ba haka bane, ka san fa raguna hudu aka yankawa Umma naman ma ai ya yi mata yawa; ga na Yaya Abubakar, ga nawa ga kuma na mijin Zahida sannan daga gidan Baffa ma cinyar sa aka kawo.’

Haka dai ya hakura da batun naman.

Sai bayan azahar ta shirya sukaje tare ya ajiyeta a gidan Umman, nan yara suka hadu akayi ta murna. Tayi matukar kewarsu don haka ta sanar da Umma duk ranar Juma’a zata dinga daukarsu daga makaranta su dinga yin weekend a wajenta, in ya so ranar Lahadi da yamma sai ta dawo da su.
_

Kamar yanda ta daukarwa kanta alkawarin ana sallacewa taje aka cire mata abun family planning din da ta saka, don haka ko al’ada batayi ba bayan an cire ta sami ciki. Shi kanshi Abban Sadik din bata sanar da shi da cikin ba ta bari sai ya kai kamar wata hudu; saboda bata so ta gaya masa ya gayawa Aisha kada ta cutar mata da ciki.

Duk wata tambaya da zata yiwa Rukayya a kan alamun ciki a tattare da Aishan Rukayyan ta tabbatar mata ba haka bane. Sai dai bata yarda da hakan ba; gani takeyi kamar Rukayyan ce bata gane ba. Don haka har saida cikin nan yayi wata uku sannan ta sanar da Abban Sadik wanda daman ya riga ya gane kyaleta kawai yayi.

Tunda ta san ta sanar da shi cikin nan kuma bata ji ya ce Aisha ma tana da ciki ba sai ta tsiri fitna; kullum akwai abinda zatace ya sa Aishan ta dafa mata daga karshe kuma idan an dafa bata ci sai ta san abinda tace bai yi mata ba. Da kanshi ya gane hakan ya daina biye mata.

Namiji take so ta haifa don haka sosai ta dage da addu’a Allah ya sa namiji ne a cikinta, sai da cikin ya kai wata biyar sannan taje aka yi mata hoto wato scanning inda aka tabbatar mata namijin ne.
--------

Kwanci tashi cikin Zahra har ya kai wata bakwai, ya riga ya fito sosai gashi da alama yaron da yake cikin nata yana da nauyi sosai. Dole yasa take hakura da kusantar Abban Sadik kamar yanda take so, ya zama sau daya a mafi yawancin dare wasu lokutan ma kuma idan yaga yanayinta haka yake lallabata suyi bacci ba ayi komai ba.
Chapter 20 · 0% Book details