← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 100

Sashe 92

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har ya saka mukulli zai bude kofar sai yaga idan ya shiga ma babu abinda zai yi don haka ya juya ya fice daga gidan ya nufi gidan Yaya Bello yana san ra duk ma inda taje kafin ya dawo ta dawo in ya so sai yaji.

A farfajiyar gidan ya sami Yaya Bellon yana zaune yana shan fura da ‘yar autarsa Minal wadda zazzabi ya hanata zuwa islamiyya. Bayan Minal ta gaisheshi ta shiga gidan ta karbo masa kofi don ya sha furar, tana ajiyewa ta koma cikin gidan.

Bayan Abban sun gaisa da Yaya Bello suka cigaba da hirarrakinsu. Yaya Bello ya dubeshi yace

'Ya yaran? Aishan ta koma wajen nasu?’

Cikin yanayi na damuwa yace

'Wallahi Yaya bata koma ba, sai wasu dokoki da ta kafa na shirme. Ni gaba daya ma na kasa fahimtar ta. Wai ita bazata rike yaran duka ba sai dai dole na cire Yusra da Nana su bazata iya zama da su ba.’

'Ah, kamar Yaya? Wannan ai zancen banza ne ma. To su Yusran da Nana gidan marayu zaka kai su kenan ko ya take so kayi dasu?’

'Wallahi Yaya nima dai na kasa fahimta.’

'To kuma bata baka wani dalili ba?’

'To basa dai jituwa da Yusra, ita kuma Nana zaka iya cewa ko uwarsu bata kai Yusran iko da ita ba. Kuma da Zahran ma ai basu sami wata jituwa ba tunda ka ga abinda ya faru har na shekara ban shiga gidan Aishan ba ko ba a fada mata ba Zahran take zargi kamar yanda kowa ma ita yake zargi. Da wasu abubuwa dai na cutarwar da rashin kunya da tace ana aika Yusran tana yi mata. Don haka tace ma wai Yusran ta tareta bayan rasuwar Zahran ta gaya mata ba zata barta ta maye gurbin uwarta ba.’

Ya daga hannuwa ya yarfe kamar mai Shirin fada yace

'Ai ka ji! Duk shirme ne nasu na mata. Nawa Yusran take da Aishan zata ce ta rasa yanda zata yi da ita? Wanna ma ai ba wani abu bane, idan ka koma sai ka hadasu ka jawa yaran kunne a gabanta. Kuma in ta dawo nan din ma ai ba kyalewa zaka yi ba, duk wanda yayi ba dai-dai ba sai ka dau mataki kuma gidan ma sai ka sa ido tunda yanzu babu irin muguntar fa da mata basa yiwa dan kishiya.’

'Hakane. Sai na koma gidan yanzu zan saka ta a gaba mu koma can din.’

'Gara haka, Kai ma ka huta da biyan kudin hayar. Amma idan kace zaka biye ta tata sai ta tarwatsa maka iyalin don haka ma kada ka saurara mata. Idan ba zata zauna maka da wadannan marayun yaran ba yanzu kam bata da wani amfani a wajenka.’
Suka cigaba da hirarrakinsu Yayan yana kara karfafa masa gwiwa lallai kada ya kyale Aishan dole ta koma ta kula masa da yaran.

Sai wajen karfe biyar na yamma sannan Abba yayi masa sallama ya kama hanyar gidan. Yana shiga unguwar ana kiran sallar Magriba don haka kai tsaye masallaci ya wuce. Sai da aka idar da sallar Magriba sannan ya wuce gidan Aishan. Kamar dazu haka ya tarar da gidan a rufe, cikin tsananin mamakin inda Aishan ta tafi ya sa mukullinsa ya bude kwadon ya shiga falon. Dakinta ya fara shiga inda ya hangi akwatunanta na saman wardrobe babu guda uku a cikinsu, ya karasa ya bude wardrobe din ya tarar ta kwashe mafi yawancin kayan sawarta. Yayi murmushi yana tunani yanzu haka ta riga shi dawowa ta hada kayanta ta koma can gidan, don haka cikin kwarin gwiwa ya fito ya nufi gidan.

Duka yaran suna zaune a falon kasa; kafin ya karasa shiga ciki Sumayya ta taso da gudu tayi masa oyoyo. Bayan ya shiga ya zauna sannan ya dubi Jummai wadda take tsaye da leda a hannunta tana jira ya dawo ta tafi gida yace

'Jummai zaki tafi ko?’

'Eh Alhaji dama jira nake ka shigo sai na tafi tunda Yayansu ma bai dawo ba tukunna.’

'To babu laifi. Aisha bata shigo bane?’

'Eh gaskiya bata zo nan ba.’

Mamakinsa ya bayyana, yayi sauri ya wayance ya sallami Jummai ta fice bayan ta yiwa yaran sallama shi kuma ya haye sama yana ta mamakin inda Aisha zata tafi harda kwashe kaya haka ba tare da ta sanar da shi ba.

Ya zauna a gefen gado ya zaro wayarsa daga aljihunsa, ba tare da bata lokaci ba ya lalubo lambar Aishan ya danna mata kira. Har aka fara kiran sallar isha'i yana nan zaune yana faman kiran wayar amma ba a dagawa, haka wayar zata kari ringing har ta katse. Cikin kosawa da damuwa ya mike ya shiga bandaki yayi alwala ya fito ya nufi masallaci yana ta tunani kala-kala; to ina Aishan ta tafi? Me ya hanata daukan wayars?

Yana daf da shiga masallacin dabara ta fado masa, don haka ya tsaya ya lalubo lambar Zahida ya kirawota. Bayan sun gaisa ya tambayeta yayarta. Nan take ta sanar da shi Aisha tana gidan Hajiya, yayi mata sallama ya ajiye wayar.

Ya mayar da wayar aljihunsa yana murmushin yake; wato Aisha gidansu ta tafi kenan saboda ba zata rike masa yara ba? To wannan wacce kalar fitna ce? Wai dama haka Aishan take ko kuwa wani ne yake zugata? To idan ma don yaranta ne ai yace ta kwasosu su dawo gidan tare? Shi dai bai taba ganin inda mutum yana da mata taki rike masa yara ba, ko da kuwa shegu ne balle yaran da aka san uwarsu. Yana nan tsaye yana mamaki ba tare da ya sami amsar tambayoyinsa ba aka tayar da Sallah, don haka ya mayar da wayar aljihunsa ya karasa masallacin ya shiga sahu cike da damuwa.

Ana idar da sallah ya koma gidan, a nan ya tarar Saddiku ya dawo don haka yayi musu sallama ya shiga mota ya nufi gidan su Aishan. Duk da bai san me zai je yayi ba amma dai yana jin gara yayiwa iyayenta bayani don yana kyauta zaton zasu goya masa baya.
UWAR SADDIKU

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

44

Tun a wannan daren Hajiya ta kirawo Abubakar ta sanar da shi ga Aisha a gida don haka gobe yazo da safe don a sami mafita. Suna ajiye waya ta kirawo Baffa, bayan tayi masa bayani yace to shima da safen zai zo don bai kamata a bari ta sake kwana ba ba tare an bi diddigin abun ba.

Ko da gari ya waye da yake Baffa ya saba sammako tun kafin su gama karin kumallo ya iso gidan, Anti Uwani ta zubo masa dafadukan taliya da kunun tsamiya. Ya sanar da ita ya riga ya ci abinci kafin ya fito sai kunun kawai ya debi rabin kofin ya zauna a falon yana sha yana jiran isowar Abubakar don yace ya fi so ayi a gabansa.

Wajen karfe takwas da kwata shima Abubakar din ya iso. Nan suka hadu a falon Hajiya da ita Hajiyan, Anti Uwani, Baffa da kuma Yaya Abubakar. Har Hajiya ta fara yiwo bayanin abinda ya kawo Aishan gidan Baffa yace

'Ai bari zakiyi Hajiya ta fito Aishatun muji daga bakinta, ta hakane idan ma bata da gaskiya da izinin Allah zan ganeta.’

Nan Anti Uwani ta mike ta shiga daki ta kirawo Aishan.

Ko Hajiya bata fito ta yiwa ina kwana ba saboda tsoron abinda zata cewa Hajiyan sai a lokacin ne ta gaisheta ta gaida su Baffa ma. Bayan ya amsa gaisuwarta yace

'Shatu ba fa na son rigima da rashin gaskiya. Me ya hadaku da mijinki har kika taho gida tun jiya, gashi ko sawunki bai biyo ba kinga da alama kenan akwai abinda kika yi masa?’

Ta sunkuyar da kai murya kasa-kasa tace

'Babu abinda nayi masa Baffa, shi yace idan na cigaba da zama zaman kaina nakeyi shine na taho.’

'Assha! Akwai abinda kika yi din kenan in ba haka ba me ya kawo wannan maganar?’

Tayi shiru tana tunanin ta inda zara fara. Jimawa kadan Yaya Abubakar yace

'Dake ake magana kina ji kin yiwa mutane shiru.’

Baffa ya daga masa hannu alamar yayi shiru, sannan ya dubi Aishan yace

'Ina sauraronki Aishatu, me ya kawo har yace miki zaman kanki kikeyi? Kuma me yasa baki bashi hakuri ba kika taho?’

Ta kasa bude bakinta don haka Anti Uwani ta karanto masa bayanin abinda Aishan ta gaya mata da ta zo. Kafin Baffan yace wani Abu Yaya Abubakar yace

'Ahaf! Ai wallahi na san akwai abinda tayi masa. Wannan shegen taurin kan nata ne ya tashi shi yasa take so ta kashe aurenta.’

Cikin muryar lallashi Baffa yace

'Aure kam ba zai mutu ba da izinin Allah, Aishatu me yasa ba zaki zauna masa da duka yaran ba? Wannan ai abu ne ma wanda ba sai kin jira ya nema ba. Haka aka saba ko rabuwar aure aka samu matar da take gidan ita take hada kan yaran ta rike, balle wadannan marayun. Kinga lada biyu zaki samu,ga ladan kula da marayu ga ladan biyayyar miji.’

Tayi gyaran murya ta korowa Baffa bayanin irin abubuwan da Yusran take yi mata tun daga farkon zamanta har zuwa maganganun data gaya mata ranar sadakar uku da kuma bangazarta da tayi a falon gidan. Tace

'Wallahi Baffa ba zata bari mu zauna lafiya da shi ba, duk wani abu da uwarta ta dinga yi min na cutarwa cigaba kawai zatayi kuma gashi nan ta fara. Shekararta kusan ashirin Baffa, ko ni na haifeta ta kai yanzu ba lallai tayi yanda nake so ba balle ta riga ta shirya cewa ni makiyarta ce. Ba wai ina tsoron abinda zata yi min bane amma ina tsoron kada ta kureni nima nace zan rama tunda yara da yawa da matan uba suke cutarwa wasu ai da akwai irin hakan a ciki don dai kawai ba za a sauraresu bane.’

Sukayi shiru gaba daya kowa da abinda yake tunani. Har Baffa ya bude baki zai yi magana Hajiya ta riga shi

'Kaji fa Baffa! Ka ga wannan ai abune wanda za a kirawo Yusufan in ya so ya tsawatarwa ‘yarsa ta bari a zauna lafiya tunda kuma ai shima yana cikin gidan.’

Cikin nutsuwa Baffan yace
Chapter 92 · 0% Book details