← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 100

Sashe 78

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta share hawayenta yayinda ta mike ta fice daga dakin, wayarta zata dauko ta kirawo Yaya Murja ta sanar da ita. A falo ta zauna a kan kujera ta dauki wayar tata, har ta budo lambar Yaya Murja sai kuma ta tuna cewa bata shirya sanar da Yaya Murja cewa Saddiku shaye-shaye yakeyi ba. Musamman da yake taba yiwa Yaya Murja korafin yanda mutane suke faman gaya mata cewa Saddiku yana shaye-shaye. Tun a lokacin Yaya Murja tace mata ta bincika sosai kuma ta sanar da Abbansa, har ma ta ce ta tura mata shi domin idan ta gan shi ko zata iya fuskantar wani abu a tattare dashi. Ko maganar bata yi masa ba balle ta bincikeshi don a lokacin gani take kawai kiyayya ce da hassada tasa ake mata haka. Sai daga baya ta samu ta tsara Yaya Murja.

To yanzu idan ta kirawota me zata ce mata? Nan ta ajiye wayar ta kifa kanta a kan kujerar ta sake fashewa da sabon kuka.

Haka ta kwana cikin matsananciyar damuwa; tunaninta daya hannu aka saka mata a al’amuranta take ta shiga matsala kuma ko wanene sai ta rama.

Mutum biyu take zargi; Aisha wadda dama duk itace silar rikita mata gidan aurenta wanda a baya yake cike da kwanciyar hankali da kauna, sai kuma Yaya Bello wanda sosai take zarginsa a kan al’amarin Saddiku tunda ta kula yana bakin cikin yanda yaransa basu da gata kamar yanda Abban yake kulawa da yaranta, tunda shi baya iya bawa nasa yaran gata kamar yanda Abban yake bawa nasa.

Tabbas sai ta rama; tunda daman yanzu account dinta ya fara nauyi. Sarkar Rukayya ta gwal kawai zata bayar aje a sayar shikenan da zarar Amina ta sami dama sai suje wajen malamin da ta samo musu tunda itama a halin yanzun tana da tata matsalar.
…………

Ko da gari ya waye ranar aiki ce don haka Abba ya shirya daga gidan Aisha suka fice gaba daya ba tare da ya je gidan Zahra ba. Ya riga ya san babu abinda suke bukata kuma ya yi waya da Malam Ali ya riga ya kai masa yara makaranta.

Babu yanda Aisha bata yi ba ya barta ta rakashi asibitin itama ya hanata, sai dai ta hada breakfast inda ta soya dankalin bature da sauce din kaza sannan ta zuba musu ruwan zafi a flask ta bashi ya kai musu. Yana fitowa ya sayi kayan shayi ya wuce asibitin.
Da sallama ya tura kofar dakin ya shiga.

Muhammadu yana zaune a kan tabarmar da ya shimfida yana kokarin hada musu shayi da ragowar ruwan da ya zo da shi jiya. Ya ajiye kofunan da suke hannunsa ya tari Abban ya karbi kayan hannunsa ya ajiye. Bayan Abban ya amsa gaisuwar sa yace

‘Likitan ya zo ne Muhammadu?’

Yace

‘Bai zo ba, nurse din ce ta shigo tace yaci abinci zata dawo ta bashi magani.’

‘To ga abinci nan ka zuba muku ku ci, bari naje na sami nurse din.’

Yana fita ya sami waje ya zauna, basu dama yayi suci abinci sannan ya samu yayi magana da Saddikun kafin likitan ya shigo.

Sai da ya basu kusan awa guda sannan ya dawo dakin, lokacin sun gama cin abincin har nurse din ta bawa Sadik maganinsa. Sun gama cin abincin, Saddiku yana zaune a kan gadon yayinda Muhammadu yake zaune a kan tabarmar yana karatu. Bayan Abban ya amsa sannu da zuwansu yace

‘Kana da lecture ne yau Muhammadu?’

Yace

‘A’a, sai gobe ne zamu yi test shi yasa nake karatu. Yau ba zan shiga makaranta ba.’

‘Allah ya bada sa a.’

Ya karasa ya zauna a gefen gadon Saddikun.
Muhammadu ya dauki litattafansa ya mike yana fadin

‘Abba bari na zauna a nan waje na cigaba da karatun, idan ana nemena Ina nan.’

‘Ok to kada kayi nisa don yanzu zan tafi.'

Ya ji dadin hakan don dama so yake yayi magana da Saddikun, wanda tun bayan da ya cewa Abban Ina kwana ya sunkuyar da kai bai sake dagowa ba.
Sukayi shiru na dan lokaci babu mai magana, shi Abban yana kallon Saddikun yayinda shi kuma ya sunkuyar da kai ya kasa hada ido da Abban nasa. Jimawa kadan Abban yayi gyaran murya yace

‘Sadik me yasa kake son ka kashe kanka?’

Ya dago kai idonsa cike da kwalla, suna hada ido da Abban yace

‘Kayi hakuri Abba.’

Ya sake sunkuyar da kansa yana share hawaye.

Abban ya jijjiga kai yace

‘Likitane ya duba ka Saddiku, nurse din da ta shigo ta baka magani bata wuce sa’arka ba sai dai ko ta baka shekaru biyu zuwa uku, kalli yayanka Muhammadu yana karatu don ya zama dan jarida, ni da na haifeka public administration na karanta shi yasa kaga na kai matsayin da na kai. Amma kai Saddiku ka zabi zama dan kwaya, ka tara kayan maye ka sha ka fita daga hayyacinka shi kenan abinda kake so Saddiku.’

Cikin kuka yace

‘A’a Abba kayi hakuri.’

‘Ka daina bani hakuri Saddiku, baka yi min laifi ba. Kanka ka yiwa laifi kuma kayiwa Allah laifi. Ya baka rayuwa kuma ya baka dama ka zama abun alfahari ga al’umma amma ka zabi shaye-shaye.’

Sukayi shiru na dan lokaci, Abban yace

‘Wa ya baka kudin zuwa party?’

‘Mommy.’

‘Tun yaushe kake shan kwaya?’

Ya sunkuyar da kai yayi shiru na dan lokaci, jim kadan yace

‘Tun ina SS 2.’

‘Ka san yanzu jikinka ya saba ba zaka iya rayuwa babu kwayoyin da kake sha ba saboda ka zama addicted ko?'

Bai iya amsawa ba kai kawai ya daga don ya san hakan ne.

‘Ina son ka Saddiku, ina son kayi rayuwa a hayyacinka kaima wataran ka zama wani ka tara naka family din cikin nutsuwa. Akwai makarantar da zasu taimaka maka ka daina shan kwaya amma fa makarantar kwana ce, idan likita ya sallameka daga nan can zamu wuce. Idan Allah ya sa ka rabu da addiction din a wata shida sai ka fito ka cigaba da karatunka.’

Kai kawai ya dagawa Abban saboda yanda kuka yaci karfinsa.
Suka zauna sukayi shiru har sai da ya daina kukan, Abban yace

‘Yanzu ina ne yake maka ciwo?’

‘Babu ko ina, jikina ne kawai yake ciwo.’

Jimawa kadan Abban yayi masa sallama ya fito ya tura masa Muhammadu sanna ya wuce office zuciyarsa cike da damuwa.

Yana tausayin Saddikun sanna kuma yana ganin laifinsa ne da yayi sakaci a kan Saddikun, yana fatan Allah ya bashi ikon ceto Saddikun.

Kafin ya isa office din yayiwa Aisha waya ya sanar da ita ta dafawa Sadik abincin rana idan ta dawo daga aiki idan ta gama ta yiwa Malam Ali waya ya zo ya karba ya kai.
…………

Tun safe take jiran shigowar Abban don ta gama shirin zuwa asibiti wajen Saddiku amma har wajen karfe tara bai shigo ba. Wajen karfe tara da rabi ta sa Yusra taje ta dubo gidan Aisha ta kirawo Abban, sai dai bata dade da fita ba ta dawo ta sanar da ita babu kowa a gidan.
Zuciyarta ta kara tafasa saboda ta gaji da abinda Abban yake mata, ita da danta a hanata zuwa ta dubo shi.

Ta dauki wayarta ta shiga daki sannan ta danna masa kira, sai dai har ta gaji da kira bai amsa wayar ba. Ji take kamar ta rusa ihu saboda takaici, ta rasa ma wanda zata gayawa taji dadi. Ta zauna a gefen gadonta ta lalubo lambar Yaya Murja wadda tun jiya take kiran Zahran ita kuma ta ki dauka saboda tana kunyar abinda zata fada mata.

Tana dauka tace

‘Zahra ina kika shiga ne ? Tun dare nake faman kiranki. Yusra dai ta ce min kina nan amma me yasa ba kya daukan waya. Kin gan ni a tsaye gidan naki zan taho ko kina asibitin?’

Cikin shesshekar kuka tace

‘Ina gida. Abbansu ya hanani zuwa asibitin kuma ya ki ya gaya min me ake ciki.’

Cikin muryar lallashi tace

‘To kinga gani nan zuwa gidan yanzu.’

Ta katse wayar ta ajiye.

Wajen sha daya saura Yaya Murja ta shiga gidan, a daki ta sami Zahran ta ci kuka ta koshi. Nan ta bata labarin irin wulakancin da Abban yakeyi mata tun lokacin da aka kwantar da Saddikun a asibiti, gashi ya ma ki ya barta koda ta ji muryar Saddikun. Sai dai duk cikin bayanan da take yi bata gaya mata ainahin abinda ya sa Abban ya ke mata hakan ba.

A iya sanin Murja ta san akwai fahimtar juna tsakanin Zahra da Abban Sadik; duk da a baya bayan nan Zahran tana kokarin ta fahimtar da yayar tata cewa tunda Abban Sadik din ya auri Aisha ya canza mata.

Gaba daya dai ta kasa gane bayanin da Zahran take yi mata a halin yanzu; amma ko ma menene ya za ayi ace mace ta haifi danta kuma ace mata bashi da lafiya amma an hanata ta ganshi kuma an ki ayi mata bayanin halin da yake ciki.

Sai da ta samu Zahran ta tsagaita da kukan sannan ta zaro wayarta daga jaka ta lalubi lambar Abban Sadik din ta kirawoshi.

Cikin girmamawa da mutuntawa suka gaisa ta tambayeshi jikin Saddiku sannan ta sanar da shi tana gidansa, ta nemi yayi mata kwatancen inda Saddikun yake a asibitin tana son zuwa ta duba shi. Bai yi mata wani musu ba domin ya san dama za ayi hakan; sai dai ko da ta nemin izini zasu taho da Zahran ya sanar da ita kada su taho da ita idan ya zo zai kaita da kanshi.

Don haka nan take ta tashi kai tsaye ta fito daga gidan ta hau motar haya ta nufi asibitin Malam. Kafin ta isa asibitin Abban ya isa don haka a farfajiyar wajen ta sameshi bayan yayi mata kwatancen wajen.

A zaune yake a kan irin kujerar nan ta dutse don haka itama Yaya Murja sai ta zauna, bayan sun sake gaisawa sukayi shiru tana jiran yace su tashi ya kaita dakin da Saddikun yake. Madadin hakan sai yace

‘Ta gaya miki abun da ya sami Saddikun?’

Cikin zakuwa tace
Chapter 78 · 0% Book details