← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 100

Sashe 75

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta san yace mata sun tafi party don haka bata sa rai zai dawo kafin karfe goma na dare ba, don haka wajen tara da rabi ta kulle gidan ta turawa Saddiku message cewa idan ya dawo yayi mata waya tunda ba ciki zai shigo ba a boys quarters dakinsa yake.

Tunda ta kintsa ta kwanta bata farka ba sai karfe biyu na dare; agogonta ta fara dubawa a wayarta taga lokaci.

Nan take ta dannawa Saddiku kira, har wayar ta tsinke bai dauka ba sai kawai tayi zaton ya dawo bacci ne ya kwasheshi tunda ya kwaso gajiya don haka itama sai ta gyara kwanciyarta ta cigaba da bacci.
__

Tana idar da sallar asuba ta sauko ta bude kofa ta leko tsakar gidan, so takeyi ta tabbatar Saddiku ya dawo gidan jiya. Ga mamakinta babu motarta a tsakar gidan wanda hakan yake nufin Saddiku bai kwana a gidan ba. Ta fito ta tsaya a kan baranda ta kwalawa Malam Sado kira, da gudu ya taho yana rike da carbinsa da yake wiridi. Bayan ya gaisheta ta amsa tace masa

‘Malam Sado Saddiku bai dawo gidan nan ba jiya da daddare?’

Ya shafa kai yace

‘Bai dawo ba Hajiya sai dai ko nan gaba.’

Ta koma cikin gidan jikinta a sanyaye.

A kan dining table din kasan ta zauna ta lalubo lambarsa a waya ta sake kira, ringing kawai wayar take yi Amma ba a dauka ba. Hankalinta ya kai kololuwar tashi da ta tuno haka yayi mata wancan lokacin da yayi accident. Nan da nan idanuwanta suka cicciko da kwalla; da sauri ta fara laluben lambar wayar Abbansa. Sai da ta zo kan lambar tasa sai kuma ta tsaya ta kasa kiransa; to yanzu idan ta kirawo shi me zata ce masa? Ce mata yayi idan goma tayi Saddiku bai dawo ba ta kirawoshi amma bata yi hakan ba sai yanzu da safe ta kirawoshi tace masa me? To idan fa accident Saddikun ya sake yi
‘Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun.’

Ta fada a fili yayinda idonta ya cicciko da kwalla. Gashi bata san abokansa ba don haka ma bata da lambar ko daya daga cikinsu. Ta tashi jikinta babu kwari ta koma saman, ta zo daidai kofar dakin su Yusra taji motsinsu. Nan dabara ta fado mata; ta karasa ta tura kofar ta kirawo Yusra. A dakin Yusran ta sameta, bayan ta amsa gaisuwar ta tace

‘Yusra yayanki bai dawo gidan nan ba jiya gashi kuma ina ta kiran wayarsa bai dauka ba, ko kina da lambar abokansa da suke party din tare na kirawosu muji?’

Da mamaki Yusran tace

‘Mommy party sukeyi?’

Itama mommy din mamakinta ya karu

‘Au baki sani ba? Yace min end of year party zasu yi shi da ‘yan ajinsu jiya da daddare.’

‘To gaskiya Mommy ni ban sani ba, kuma a abokansa mutum daya nake da lambarsa. Bari na kirawo shi muji.’

Nan ta koma daki ta dauko wayarta ta dawo wajen Mommy din. Ta lalubo lambar Babs wanda dan ajin su Saddiku ne, shima ta sami lambarsa ne saboda yana sonta duk da ita din bata sauraronsa.

Sai da ta zauna a kusa da Mommy sannan ta danna masa kira ta sa wayar a loudspeaker. Yana dauka yace

‘Today is going to be a good day tunda ke kika fara kirana Babe, to ya kike?’

Tace

‘Uhm! Lafiya. Ka san wani abu? Ya Sadik nake nema ka san tun jiya da daddare bai dawo gida ba yace wai ‘yan class dinku suna end of year party shine nake son naji me ya hanashi dawowa gashi Mommy tana nemansa.’

Da mamaki a muryarsa yace

‘Party? Gaskiya ba dai ‘yan class din mu ba sai dai ko wasu friends din nasa, don gaskiya duk mun koma gida ko nima kin ganni a KD.’

Sukayi shiru na dan lokaci, jima kadan yace

‘Amma bari na tambayar miki su Bigi duk da dai na san ba da su bane amma dai idan har guys din mu ne suka shirya party din to lallai Bigi zai sani.’

Sukayi sallama bayan ya sanar da ita idan ya ji wani abu zai kirawota.

Ta dubi Mommy tace

‘Kin ji Mommy!’

Cike da damuwa tace

‘Hmm! Na ji Yusra. Ni haka yace min da 'yan class dinsu don sai da na bashi 20k sannan kuma ya zagaya ya karbe kudin da aka sayar da garwar tsohuwar motata ba tare da ya gaya min ba kuma cewa yayi duk a kan party din ne. To ina ya tafi?’

Jimawa kadan ta sallami Yusran don taje ta shirya mata yara su tafi tahfiz.

Haka tayi ta faman jan kafa cikin matsananciyar damuwa har wajen karfe goma saura.

Wajen karfe goma Abban ya shigo don ya dubasu ita da Yaran. Bayan ya amsa gaisuwar Yusra a falon kasa ya haye saman. A dakinta ya sameta tana kashingide a gefen gado, bayan sun gaisa ya zauna a gefen gadon kusa da kafafunta yace

‘Ya dai? Jikin ko garin na ganki a kwance.’

Ta tashi ta gyara zama sannan ta bashi amsa

‘Uhm, babu ko daya. Hutawa dai nake yi kafin ‘yan gidan su dawo.’

‘Saddiku har ya fice ko? Ai sun gama exam tunda ke bakya hawa motar yau in ya dawo ya bani mukullin motar ya huta yawon ya isa haka, da anyi magana yace zasu je lecture ko kuma zasu hadu suyi karatu.’

Ta dan muskuta

‘Um nima haka na gani, bari ya dawo sai na karbi mukullin motar na boye saboda in zan fita.’

Suka dan taba hira daga baya yayi mata sallama ya fita; yana mamakin Zahra! Tun tuni yake so ya karbe mukullin mota daga hannun Saddiku amma ta hanashi sai tace ita zata kwace kuma bata iyawa. Lokuta da dama yana mamakita, yanda har yanzu ta kasa gane cewa bata tarbiyyar Saddiku takeyi. Shi yasa har yanzu bai gayamata cewa ba zai biyawa Saddiku kudin registration ba sai ya je makarantar da kansa ya ga result dinsu.

Ta kasa gayawa Abba cewa bata ga Saddiku ba kuma ta rasa wanda zata gayawa gashi har sha biyu saura, ta dai yanke shawarar idan aka yi kiran azahar bata sameshi ba zata gayawa Abbansa.

Karfe Sha biyu da kwata wayarta tayi kara, ta dauki wayar kamar wadda aka yiwa dole sai kuma ta ga sunan Saddiku, sai da zuciyarta ta nemi tsayawa lokacin da ta kara wayar a kunnenta. Kafin tayi magana aka ce
‘Hello.’

Ba Saddiku bane yake magana, haka dai ta daure ta amsa. Bayan mai maganar ya gaisheta yace

‘Don Allah ina magana da mahaifiyar Sadik Yusuf ne?’

Cikin hanzari tace

‘Eh, ina Sadik din?’

‘Um gamu nan da su a asibitin Malam Aminu Kano emergency shi da abokansa, suma sukayi tun jiya a wajen party da suka sha kwaya, har yanzu basu farfado ba.’

‘To gamu nan zuwa.’

Ta saki wayar a kan cinyarta daidai lokacin da hawaye ya wanke mata fuska.

Saddiku ya sha kwaya tun jiya ya suma? Yanzu me zata cewa Abbansu, bayan ta gama gaya masa da safen nan Saddiku ya fita.

‘Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun!’

Ta mike tsaye, wayar da take ajiye a cinyarta ta subuce ta fadi kasa ta dauke wayar ta ajiye a kan gadon. Ta karasa gaban wardrobe tana share hawaye ta dauko hijabi ta saka sanna ta dauko jakarta a kan mudubi ta dawo ta dauki wayar ta jefa a ciki ta nufi ficewa daga dakin.

Har ta kama hannun kofar sai kuma ta tsaya ta kasa murdawa; to ina zata? Babu mota a gidan kuma Malam Ali baya nan, shi kuma Abban da yake ba a nan ya kwana ba bata ma san ko yana gida ko baya nan ba. Ta juyo cikin sanyin jiki ta koma kan gadon ta zauna ta zuba fuskarta a tafukan hannunta ta sake fashewa da kuka. Bata da wata mafita illa ta kirawo Abban Saddiku ta sanar da shi domin idan ma taje asibitin ita kadai a halin yanzu komai zai iya faruwa.

Ta kama gefen hijabin da yake jikinta ta goge hawayenta, tayi ajiyar zuciya ta laluba jakarta ta dauko wayarta. Ta lalubo lambar Abban Saddiku ta danna kira ta kara a kunnenta zuciyarta na dakan uku-uku.
…………

Fitowarsu kenan daga gidan Hajiya shi da Yaya Bello, suka shiga motar Abban suka kama hanyar gidan Yaya Bello inda a can zasu ci abincin rana. Yana zura mukullin motar kira ya shigo wayarsa wadda ajiyeta kenan a kusa da giyar motar; ya fasa tayar da motar ya amsa wayar ya kara a kunnensa. Ba tare da ta amsa sallamarsa tace

‘Abba Saddiku bashi da lafiya yana asibitin Malam a emergency, yanzu Yayan abokinsa da suke tare ya kirawoni ya sanar da ni.’

‘Subhanallah! Accident yayi ko me?’

‘Nima dai ban gane bayanin ba amma dai ba accident bane, nima yanzu zan sami motar haya na wuce asibitin idan kuma kana unguwar sai na shirya mu tafi.’

‘Ina gidan Yaya kiyi zamanki zan je na gani in ya so mayi waya.’

Ya ajiye wayar ba tare da ya saurari amsarta ba.
Ya dubi Yaya Bello da yake gefensa ya sanar da shi abinda ta gaya masa, nan yace su wuce asibitin kawai. Don haka Abban ya tayar da motar suka kama hanya.

Ita kuwa Zahra yana ajiye wayar ta dora hannu aka ta sake rushewa da kuka; shikenan a gaban Yaya Bello za a yi mata wannan tonon asirin, ya sami dalilin da zai shiga rayuwarsu ita da yaranta ya hanasu jin dadi.

Sai da tayi mai isarta sannan ta dauki wayarta ta kirawo Yaya Murja ta sanar da ita halin da ake ciki, duk da bata gaya mata cewa kwaya Saddikun ya sha ba.

Sukayi sallama a kan idan taji abinda ake ciki ta sanar da ita.
…………

Har suka isa asibitin Malam Aminu Kano babu wanda yace wa dan uwansa wani abu; shi Abba yana ta mamakin to Saddikun da aka ce masa dazu ya fita meye zai sameshi har a kaishi emergency kuma ace ba accident ba yayinda shi kuma Yaya Bello yake kallon hanya yana nashi nazarin.
Chapter 75 · 0% Book details