← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 100

Sashe 87

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'Hakane. To ni zaman nake ji; kin san fa duk labaran da muke ji a kanta ba masu dadi bane, kamar dai daga abubuwan da Zahran take fada matar tana da fitna ga sharri.’

Suwaiban ta dawo ta zauna kusa da ita a gefen gado ta fuskanceta tace

'To Yaya mu ya zamuyi? 'Yaya dai nashi ne don haka yanda yake so haka zai yi da su. Don kuwa kin san babu makawa ita zai bawa rikon yaran nan wanda hakan shine daidai.’

Cikin damuwa Yaya Murja tace

'Hakane. Ni da tunanina ko ayi masa magana idan ba damuwa ya auri Rahama, kinga dama ta saba zama da yaran shi kuma ya saba zama da mata biyu shikenan sai ta rike yaran ‘yar uwarta.’

Ta dan zaro ido

'Yaya kada fa ki manta shi ba dan uwanmu bane don haka bamu da uko da shi, kuma ita Rahman idan bata yarda ba fa?’

'Ai ba mu zamu yi masa magana ba, idan muka kaiwa Baffa shawara su sai su shawarceshi. Ita kuma Rahma ni bana ma jinta; ya za ayi taki yarda ma? Kalli fa shekarun da ta dauka babu aure, ai ina ga ko musu ba zata yi ba tunda ko babu komai ta san ba zata je gidan Zahra ta sha wahala ba.’

'Hmm! Kada dai ki ballo ruwa Yaya.'

Ta mike ta saka hijabinta tana fadin

'Mu tafi Yaya don ina son na dawo kafin ‘yan makaranta su dawo.’

Suka fice suka nufi gidan Zahra.

Lokacin da suka je gidan yaran duka suna makaranta sai Goggo da Jummai, suna nan zaune a falon kasa suna gaisawa Saddiku ya fito a shirye. Bayan sun gaisa suka dan taba hira sannan yayi musu sallama ya wuce wajen da yake koyon computer.

Nan suka zauna suka cigaba da hira.

Duk yanda Yaya Murja ta so taji yanda zamantakewa take tsakanin Aisha da yaran nan bata sami wani abun aibi ba. Duk da Jummai bata san wani abu game da Aisha ba saboda kwata-kwata Zahra bata bada damar hakan ba, amma dai abubuwan da ta sani game da ita duk alkhairi ne. Don haka basu sami wani abu da zasu iya kamawa ba.

Suna Shirin tafiya Yusra ta dawo, bayan ta ajiye kayanta ta zauna a wajensu suka cigaba da hira.

Daga bakin Yusran ne Yaya Murja ta dan ji wasu bayanai na karya wadanda suka kara tabbatar mata da cewa Aisha zata iya cutar da yaran nan idan an barta da su. Kafin azahar suka yi musu sallama suka tafi; Yaya Murja tana kara tabbatarwa da Suwaiba cewa gara idan an kwana biyu suje su sami Baffa a yiwa Abban magana ya auri Rahma.

__

Sai da aka yi sallar la'asar sannan Abban ya samu ya baro office, aiyuka sunyi masa yawa musamman da yake ya dauki tsawon sati bai je aikin ba. Yana shiga unguwar ya wuce wajen yaran, bayan ya dubasu ya tabbatar sun tafi islamiyya ya wuce gidan Aisha.

Sai da yaci abinci ya huta sannan ya sameta a falo tana kallo, bayan ya zauna yace

'Wai ya naga baki fara hada kayan bane, kin san fa ya kamata a ce yau kin koma saboda Goggo ma ta san ba su kadai za a barsu na.’

Ta kalleshi suka hada ido, tayi murmushin yake. Ta hada tafukan hannunta ta ta rufe tsakiyar fuskarta da su tana kallonsa ta gefen idonta.

Binta kawai yakeyi da ido yana mamakin kalaman da take son fada da suka yi mata nauyi haka, a lokaci guda kuma yana mamakin abinda ya hanata ta fara kokarin bin umarnin da ya bata.

Sai da tattaro duk wani karfin hali da take dashi ta bude baki a hankali tace

'Kayi hakuri gaskiya ba zan iya komawa can gidan ba.’

Kallon da yake binta da shi ya sa ta dakata da maganar ba don iya abinda ta so fada kenan ba.

Tsananin mamaki ya bayyana a fuskarsa, yace

'Ban gane ba. To ya za ayi da yaran? Kin san dai idan sun dawo nan dakunan ba zasu ishemu ba sannan kuma nan din gidan haya ne wancan shine nawa. Don haka kinga dole haka zaki koma can din. Idan ma akwai wani abu da kike so a gyara a gidan a hankali za a mayar miki da shi yanda kike so ai ko?’

Ta sake saita fuskarta ta dan jijjiga kai tana dubansa, suka dan yi jim suna kallon juna sannan tace
'Gaskiya ba wai gidan ne ba zan koma ba. Ka san dai raino abu ne mai wahala kuma mai nauyi, duk kwatancen da zan yi maka ba zaka gane ba. Gaskiya ba zan iya rike yaran bane ba wai gidan ne bai yi min ba.’

Ji yayi kamar ta buga masa guduma a ka, ya kalleta cike da tsananin mamaki wanda a hankali ya fara komawa fusata. Nan take itama ta bata rai ta kawar da kanta. Bayan ya gama kare mata kallo yace

'Ban fahimcekiba, kina nufin kice ba zaki zauna ki kular min da yara ba kenan? To ya kike so nayi da su? Haka za a barsu su cigaba da zaman kansu ke kuma gaki a nan a matsayin matata ko kuwa hakura zanyi da aikin na zauna na dinga kula da su?’

Ta sunkuyar da kai cikin murya kasa-kasa tace

'Ban sani ba, amma dai na san abinda ba zan iya ba. Kayi hakuri ka fahimce ni.’’

Cikin daga murya yace

'Ya za ayi na fahimceki Aisha, kina gaya min ba zaki iya zama da ‘yayana ba? Me suka yi Miki? Ko kuma kishin mahaifiyarsu ne zaki koma yi da su da har kike kyamatarsu haka?’

Wata zazzafar kwallace ta fado kan fuskarta; dama ta san babu wanda zai fahimceta musamman shi da yake so a yita kula da shi da ‘yayansa. Batayi magana ba don haka ya cigaba.

'Daman shi yasa tun farko kika ki zama a cikin iyalina? Kina nufin ni kadai kike so ba kya son zuri'ata Aisha? Wannan ai ba so bane. A kan idonki yaran suka zama marayu amma kice ba zaki iya kula da su ba ke ko ladan rikon maraya ba kya so? To ya kike so nayi da su?’

Tayi murmushi tare da share kwallar idonta, ta mika hannu ta dafa hannunsa dake ajiye a kan kujera. Ya kalli hannun nata sannan ya zare hannunsa tare da jifa da nata hannun. Gaba daya tsoron da yake zuciyarta ya fice don ta kula so yake yayi mata wata fassara da ban. Ta gaji da share kwalla don haka ta bari hawaye ya fara bin fuskarta, ta bude baki a hankali tace

'Tun kafin su zama maraya nake rikon marayu don idan ba na manta karatun islamiyya ba to wanda ubansa ya mutu shine maraya amma wanda uwarsa ta mutu musulunci baya kiranshi maraya don uba shine karshen gata. Ban san yanda zakayi da su ba amma dai na san kana da zabi kamar yanda musulunci ya tanada idan an sami irin wannan dangin uwa zasu iya rike yara, idan kuma lallai matarka kake so ta rike su to ai kana da damar da zaka kara aure ka sa matar a gidan. Ni bani da matsala da hakan. K..’

'Ke yanzu a kan ki zauna da yaran kin gwammace na kara aure? To naji kema kina da marayu, ai wannan ba zai zama matsala ba sai ki dauko su su dawo nan mu zauna tare. Wannan ma da kin yi magana ai da tuni suna nan.’

Tayi yake tace

'Daga baya kenan!’

'To don Allah su su Yusran me yasa ba Zaki iya rike su ba, yaran ma da kusan kowa ya iya kula da kansa? Me suka yi miki ko me uwarsu tayi miki da ya shafe su kika tsane su haka?’

Ta kula bata da wata mafita idan bata gaya masa gaskiyar abinda yake ranta ba. Ta muskuta kadan tace

‘Ba wai ba zan iya rike maka yara bane, hasali ma ko dan shege ka kawo zan iya rike maka shi har bayan ranka. Amma gaskiya ba zan iya zama da Yusra da Nana ba, idan ka cire su biyu zan iya rike sauran yaran.’

Kan sa ya kara kullewa, binta kawai yake da kallo. Ya gyara zama cike da bacin ran wannan rainin hankalin da Aisha take masa yayi ‘yar dariyar takaici yace

'Ah! Aisha kina bani mamaki. Yusra da Nana su kadai kika tsana? To me sukayi miki da ba zaki iya zama da su ba?’

Ta share hawaye tace

'Allah ya sani ban tsane su ba amma cutarwar da mahaifiyarsu tayi min tana da matukar yawa duk da kai ma ka san wasu sai dai ka ki gayawa kanka gaskiya.’

Ya bude baki zai yi magana ta dakatar da shi da hannunta ta cigaba

'Duk wata cutarwar da Zahra tayi min da Yusra take amfani, ban iya kai kara ba shi yasa ban taba gaya maka ba musamman bayan ka nuna mini yaranka masu tarbiyya ne ba zaka dauki laifinsu ba. Idan baka manta ba akwai lokacin da ka dinga kasa cin abinci na saboda yanda dandanon yake canzawa, to a wannan lokacin Yusra ake aikowa ta zo ta saka min sabulu a abinci wanda sai da Allah ya toni asirin ta na gane.
Yanzu ma kuma ranar da aka kwana uku da rasuwar mahaifiyarta tayi min alkawarin ba zata taba bari na maye gurbin uwarta ba kuma na tabbatar da gaske take.’

Ya nuna ta a raine

'Yanzu ke Yusran kike biyewa? Gidanta ne ko nawa da zaki kama zancenta?’

‘Ban iya rigima da tashin hankali ba kuma na tabbatar in dai da Yusra zan zauna to a cikin haka zan rayu. Ba zan iya ba, amma sauran yaranka gaskiya bani da matsala da su zan iya rike su kamar ni na haifesu.’

Ya ja tsaki ya mike a fusace, ya nunata da yatsa yace

'Wannan duk maganar banza kikeyi! Idan dai zamana kike a wannan gidan to na baki umarni gobe ki koma wancan gidan an gyara miki daki, idan kuma zaman kanki kikeyi to sai ki yi yanda kike so.’

Ba tare da ya saurari amsarta ba ya fice daga gidan.
Chapter 87 · 0% Book details