← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 100

Sashe 47

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya dauki wayarsa ya duba lokaci, tabbas idan bai yi da gaske ba zai makara. Nan da nan ya kintsa ya fito falon. Tana zaune tare da su Rukayya suna cin abinci; suka hada baki suka gaisheshi bayan ya amsa ya wuce dining table ya zauna ya fara cin abincinsa.

Yana ci yana jiyo Aisha tana ta hira da yara suna dariya; tabbas ya san fushi takeyi da shi.

Ya san yana da aiki domin Aisha sarauniya ce, dole ya lallabata su shirya.

Kafin ya gama sahur sun gama ita da yaran, ta shiga dakinta ta dauko wayarta da kayan sawarta. Yana nan zaune ta wuceshi ta koma dakin yaran.

Tana shiga ita da yaran suka fara Sallah. Dama haka suke da sun gama sahur ragowar lokacin sai suyita ibadarsu har asuba tayi.

Haka ya gama cin abincinsa ya koma daki, da aka yi assalatu ya shirya ya wuce masallaci.
__

Tunda Rahma ta tabbatarwa Yusra cewa Abbansu ya tafi wajen amarya ta kasa nutsuwa, so take ta gayawa Mommy amma kuma bata da waya. Dama wayar Abban suke kiranta da ita kuma ya fita da kayarsa, shi kuma Saddiku yana bq balle ta ari tashi, ba ta so ta ari ta Rahma don kada ta zargi wani abun. Haka ta hakura ta kwanta da shawarar idan sun tashi sahur sai ta ari wayar Rahma ta kirawo Mommy din, tunda ko flashing tayi mata ta san zata kirawo.

Wajen karfe uku na dare suka tashi sahur, Yusra da Nana suka daga dakinsu. A nan falo Nana ta zauna yayinda Yusra ta wuce kichin inda ta jiyo motsin Rahma.

Bayan ta gaisheta tace

‘Anti Rahma don Allah ki bani aron wayarki na yiwa Mommy message.’

‘Tana daki ki dauka, amma don Allah ki shiga dakin a hankali kada ki tayarin da Sumayya.’

‘To Anti Rahma, ba zan tasheta ba.’

Tana daukan wayar ta haye sama ta shige dakinsu, credit din wayar ta fara dubawa taga naira dari da ashirin. Ta san ba zai isheta waya ba amma ta san zai isa ta cewa Mommy din ta kirawota.

Nan da nan ta dannan lambar Mommy ta Saudiya, ringing daya Mommy ta dauko kafin tayi magana Yusra tace

‘Mommy Yusra ce, ki kirawo ni.’

Saida gabanta ya fadi, jikinta har rawa yakeyi lokacin da take kokarin kiran lambar Rahman. To me ya faru Yusra take nemanta a wannan lokacin? Allah ya sa dai ba wani abun ne ya faru da gidan ba.

Muryar Yusra ce ta katse mata tunaninta, ta amsa gaisuwar Yusran sannan tace

‘Ya akayi Yusra?’

‘Mommy kin san jiya tun wajen sha daya na dare Abba ya fita, wai ya tafi gidan matarsa kuma a chan zai kwana.’

Da tsananin mamaki tace

‘Kwana Yusra?’

‘Wallahi Mommy, har yanzu ma yana can don bai dawo nan ba.’

‘Um, ba zama ta barshi ya dinga kwana inda kuke ba tunda ba na nan, shine ta janye shi ta barku ku kadai? Ai shike nan.’

‘Wallahi Mommy, yana can abunshi.’

‘Babu komai, ki cigaba da kular min da gidan kiga zuwa lokacin da zai dawo. Duk wani abu da yayi zuwa na dawo ki kular min. Zan kirawo ki da safe.’

Suka yi sallama suka ajiye wayar.

Yusra ta sauko ta mayarwa Rahma wayarta suka cigaba da sahur dinsu.

Duk da Rahma bata san menene dalilin da ya sa Yusran ta kirawo Mommy ba amma ta zargi cewa zata gaya mata ne yau Abbansu ba a nan ya kwana ba; domin tana sane da yanda duk wani motsi da akayi a gidan Yusra sai ta sanar da uwarta.


Sallah takeyi a lokacin da ta sallame ta amsa kiran Yusra, sai dai zuwa lokacin da suka gama waya da Yusran ta ma manta me takeyi. Abinda Yusran ta gaya mata ya girgizata sosai.

Ya za ayi ace Abban ya tafi kwana gidan Aisha? Ita da a gaban idonta ta ga cewa ya kasa shiga gidan. Kuma yaron Malam ya tabbatar mata muddin wannan abun da ya bata yana binne a gidan Aishan to Abban ba zai taba iya shiga gidan ba, to yanzu me ya faru? Zuciyarta ta kara harbawa da sauri a daidai lokacin da tayi tunanin watakila fa Aishan ta saka an hake abun nan; lallai yarinyar nan hatsabibiya ce kamar yanda yaron Malam ya fada. Yanzu kenan Abban yana can wajen Aishan ya bar mata yaran yana jin dadi; anya kuwa Aisha ba so take ta raba Abba da iyalansa ba? Ai kuwa doke ta dauki duk wani mataki da ya dace don ba zata zauna wata banza tazo ta rabata da mijinta uban ‘yayanta ba.
Ta dauki wayarta ta fara laluben lambar yaron Malam, sai dai ta tuna a babbar wayarta kawai take da lambarsa wadda kuma a gida ta barta ta taho da karamar duk saboda kada tazo da babbar wayar ta hanata ibada yanda ya kamata.

Tayi tsaki a fili, Falmata wadda suke daki daya tace

‘Hajiya Zahra ya dai, lafiya dai yaran suke ko? Naga kina gama waya da Yusran kin shiga damuwa.’

‘Tsewww! Wata ‘yar matsala ce amma in Sha Allah babu damuwa.’

‘To ki barwa Allah, ai idan kana nan baka da matsala sai kawai kiyi ta roka kafin kije gidan komai ya daidaita.’

‘Umm.’

A nan Falmata ta barta ta wuce bandaki don tayo alwala ta wuce masallaci inda ragowar ‘yan dakin nasu a can suka kwana suna ibada.
__
Bayan ya dawo daga sallar asuba ya jiyo motsinsu ita da yara a kicin, bai leka ba ya wuce dakinsa ya kwanta. Bacci ne me nauyi ya kwasheshi saboda yanda ya kwana ba tare da yayi bacci ba.

Kafin karfe bakwai sun gama gyara gidan sun shirya tsaf ita da su Amira.

Bata ji motsinsa ba don haka ta san bacci yakeyi, ta dauki wayarta ta shiga kicin ta kirawo shi. Bugu daya ya dauki wayar, tana jin muryarsa ta san bacci yakeyi, tace

‘Sorry, na tasheka. Zamu je kitso ni da yara kada ka tashi kaga bama nan.’

‘Oh, to ku dan jirani ina zuwa.’

Suka tsaya a falon cikin shirinsu.

Baifi minti biyu ba ya fito falon, bayan ya amsa gaisuwar su yace

‘Kuma da sassafe zaku je kitson haka? Yanzu fa karfe bakwai tayi.’

‘Ka san na Sallah ne akwai layi, yanzu ma kada kayi mamaki mu sami wasu a wajen. Kuma sai an wanke kan an yi kitso sannan ayi kunshi, idan bamu tafi yanzu ba a can zamu sha ruwa.’

‘To sai kun dawo. Ai ban bayar da kudin kitson ba ma ko?’

Su Rukayya suka fice suka barsu. Tace

‘Babu komai dama na tanadi kudin kitson ai.’
‘To ku tafi, amma dai zan turo da kudin kitson yanzu.’

Tayi masa sallama ta wuce suka kama hanya yayinda shi kuma ya koma ya cigaba da baccinsa.

Kafin su isa wajen kitson sako ya shigo wayarta, tana dubawa taga shine ya turo mata naira dubu ashirin kudin kitsonsu ita da yaran.

Bai fi mutum biyu suka samu a wajen ba don haka nan da nan suka fara tunda sun riga sunyi booking. A da tace ba zata yi gyaran jiki ba sai bayan Sallah amma tunda taga ya turo kudi har dubu ashirin haka ta sa saida aka yi mata gyaran jiki sannan aka gyara gashin aka dandasa mata kunshi. Suma Rukayya da Amira kowacce an dandasa mata kunshi da kitso.

Sai wajen karfe hudu saura suka gama, suna fitowa suka biya ta gidan kawarta inda ta kai musu dinkinsu; leshi ne mai kyau ta siya yadi goma ta kai a dinkawa Amira, Rukayya da kuma Farha, a nan wajen kawar tata da ta bayar da dinki ta saya musu kowa jaka da takalmi sannan da mayafi. Bayan sun karba suka wuce gidan Hajiya suka ajiyewa Farha nata kayan.

Farha taso tayi bori a kan sai ta bi Mama, domin da Rukayyan da Amiran duk ta saba da su; cikin dabara Aisha ta lallabata a kan jibi ne sallah idan tayi kallon sarki ta gama Baba Abba zai zo ya kawota wajen Mommy.
Har sun zauna a mota Rukayya tace

‘Anti da ma mun taho da Farha.’

‘No, za mu bar wa Hajiya gidan ba hayaniyar Sallah. Bayan Sallah dai zasu zo in Sha Allah.’

Bayan sallar la’asar suka shiga gidan; Abba yana zaune a falo yana kallon TV tunda ranar Lahadi ce babu aiki duk da yaje gidan Zahra don ya dubo yaran sai dai bai dade ba ya dawo nan din ya zauna.

Bayan ya amsa gaisuwar su Amira suka shige dakinsu ita kuma Aisha ta shige nata dakin. Suna wucewa ya bi bayan Aisha.

Ta riga ta shiga bandakin don haka ya zauna a gefen gado yana jiranta. Bai dade da zama ba ta fito daga bandakin da alwalarta. Tana fitowa dakin ya mike tsaye

‘Aisha.’

Ta amsa yayinda ta dauki hijabinta ta fara kokarin sakawa.

‘Aisha fushi kikeyi da ni ko?’

Ya fada yayinda ya sha gabanta.

Tayi dan gajeran murmushi tace

‘A’a, ni ba fushi nake ba. Amma dai yanzu kaga ban yi la’asar ba gashi kuma an kusa shan ruwa ban dora komai ba.’

Ya bi fuskarta da kallo yayinda yanayin fuskarsa ya canza zuwa na damuwa.
Maganarta gaskiya ne, kuma ya san idan ya takura zai iya karya musu azumin ma don haka ya ja baya yana fadin

‘Hakane. Nima a nan zan sha ruwa ki ajiye min abinci na.’

‘To.’

Ya wuce ya koma dakinsa.

Nan da nan ta idar da sallah ta fito suka shiga kicin ita da su Rukayya.
……….

Duk yanda ya zata zai samu ganawa da Aisha abun ya ci tura, idan ta zuba abinci to sai ta zauna cikin yara ta ci nata. Da daddare kuma idan ya fita sallar tarawih duk saurinsa kafin ya dawo ta zuba yara a daki sun kwanta har ita.
Chapter 47 · 0% Book details