← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 100

Sashe 26

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun daga lokacin da Aisha ta kama Yusra tana zuba mata sabulu a abinci sai kuma ta samu saukin fitnar Zahra, sai dai ita Aishan ta kasa sakewa da yaran gaba daya har Rukayya. Ko da Rukayyan ta zo tayata kwana sai tayi ta kula da ita tana kula da motsinta musamman a kitchen.

Tun wannan lokacin kuma sai fitnar Zahra tayiwa Aishan sauki, duk da bata fasa aniyar raba Aisha da Yusuf ba ta dai bari ne kawai tana jira ta tara kudin da zata iya bawa Malam Hatimu yayi mata aiki. Sannan kuma tunda Hajja ta bata maganin nan ta boye a bayan wardrobe ta sami natsuwa tunda duk abinda take so yayi mata yana yi, sannan kuma ko fada zai mata a kan wani abu da zarar ta bata rai sai ya fasa.
-------

Kwanci tashi har shekara ta zagayo an fara lissafin azumi, tunda aka ce azumi saura sati hudu Abban Sadik ya fara maganar kayan Sallah.

Saida ya gama magana da Zahra tayi masa total gaba daya har na Aisha, ya tabbatar mata da anyi albashi zai saka mata kudin.

Yana zaune a falon Aisha ta tada kai da cinyarsa suna hira, ya mika hannu ya dauki wayarsa yace

‘Au, bari na turawa yayarki kudin kayan sallarku don na huta, sai kuma a shiga hidimar azumi.’

Ta dauke idonta daga kallon TV din da take kallo tace

‘Wai Mommy?’

‘Eh, kin san sallar ta matso.’

Ta tashi zaune ta sashi a gaba

‘Don Allah ni dai kada ka tura da nawa, ka turo min kudin zamu saya tare da su Zahida kaga waccan babbar sallar ma haka sukayi anko babu ni.’

Yayi ‘yar dariya

‘Yanzu ku kayan sallar ma sai kunyi anko? Mata masu gari. To gaya min lambar sai na tura miki naki ita sai na tura mata nata da yara.’

Tana gaya masa kuwa nan take ya tura mata dubu dari kudin kayan sallarta, sannan ya tura wa Mommy nata da na yaranta.

Bayan ya je gidan ne take tambayarsa taga kudi amma basu cika ba; yayi mata bayani cewa Aisha ta karbi nata zasu saya da ‘yan uwanta. Babu yanda ta iya haka ta hakura da shirin tsiyar da tayiwa Aisha domin duk mitar ta yace mata shi ya riga ya gama wannan maganar.
……..

Cikin azumi ya sanar da Mommy yana shirin zai je aikin Hajji kuma da ita zai je, a take ta fara murna. Tayi masa godiya sosai sannan tace

‘Amma wallahi da ma Umrar azumi ka biya min, ka ga zuwana Hajji biyu fa zan so zuwa Umra, musamman ta azumi. Kuma ka ga ma yanzu Sumayya bata isa yayeba.’

Ya danyi tunani yace

‘Hakane, to babu damuwa. Sai muje Hajin da Yaya Bello in ya so kafin karshen shekarar sai na biya miki Umrar ko ba zan je ba sai kuje da Sadiku. Ita kuma kanwarki badi sai muje Hajin da ita.’

Nan take ta sake cika da murna tunda taji yace zai biya mata suje ita da Sadik, tana ganin kamar ma idan ta saka shi a gaba da naci ya hada harda Yusra in ya so su tafi ita da yaranta. In ya so Hajin da yace zai je da Aisha kuma ta san yanda tayi a ka bar zancen don tana ji a jikinta kafin shekara war haka ma ta samu an yi mata aikin nan an kada mata Aishan.
……..

Saura kamar sati hudu tafiyar alhazai Aisha ta fara laulayi, amai da jiri babu sassauci. Suna zuwa asibiti aka tabbatar ciki ne da ita sati hudu, aka rubuta mata magunguna aka sallamesu.

Tun a hanya yake tsokanarta domin da ya fidda rai da yaga aurensu har ya haura shekara ko batan wata bata taba yi ba. Yana kaunar Aisha sosai don haka yake so ta haifa masa yara ko guda biyu ne, sannan ne zai tabbatar jininsa da tsokarsa ta gaurayu da ta Aisha.

Don haka suka dawo gida suka cigaba da rainon cikinsu; duk da bayan ta fara shan magungunan da aka bata laulayin yayi mata sauki tunda tana zuwa aiki kuma tana harkokinta sosai.

Sati biyu da zuwansu asibiti ya kama ranar da jirgin su Abba zai tashi.

Tsaf Abba ya gama shirinsa yayinda Malam Sule da Yaya Bello suke jiransa a mota, ya sa Rukayya a gaba ta hada kayanta, ya kaita gidan Aisha yace ta zauna a nan har sai ya dawo daga Saudiya sai ta koma wajen Mommy. Ya sanar da Mommy din kuma ta dinga duba masa Aisha don tana dauke da juna biyu. Yayi mata sallama ya fice suka kama hanya.
Yana fita ta mike ta fara zarya a falon, wato don ma raini ita yake gayawa yayiwa amaryarsa ciki ta kular masa kafin ya dawo? Tayi kwafa, in sha Allah wannan cikin sai ya bare kafin ya dawo.

A take ta dauki wayarta, har ta lalubo lambar Hajja zata kirawo sai kuma ta fasa, ta kirawo Malam Hatimu mai almajirai.

Bayan ta sanar da shi cewa wancan aikin fa tana nan tana hada kudinsa sannan ta dora da bayani

‘Malam yanzu ciki ne da ita amma gaskiya ina so ne a lalata cikin, kwata-kwata bana so ta haihu na fi so yanda ta shigo ita kadai ta fita ita kadai kawai.’

Yayi ‘yar dariya

‘Wannan karamin aiki ne, yara ma zasu iya yinsa. Akwai laya da za ayi aiki a ciki a baki ki samu ta tsuguna a kan layar nan, idan dai ta tsuguna to kafin awa daya cikin ya rabu da jikinta.’

‘To Malam yanda za ayi ta tsuguna din shine matsalar don ka ga ma ba gidan mu daya ba.’

‘Kada ki damu, ko yara ki bawa su jefa mata a masai. Na san masanku na tangaran ne layar kuma mai sulbi ce ana jefawa ko ba a kora ba zata wuce, idan dai ta tsuguna a kan wannan masan cikin nan sai ya fita daga jikinta.’

Tayi murmushin farin ciki, yayi mata bayanin kudi Naira dubu goma sha biyar. Nan take tana ajiye waya ta tura masa kudin da alkawarin washegari zai taso yaro ya kawo mata har gida ita kuma zata sallami yaron.

Cikin walwala ta karasa wunin ranar domin dama babban abinda yake firgita ta shine Aisha ta tarawa Yusuf wasu yaran. Ta ci alwashin ko sau nawa yarinyar nan zatayi ciki sai ta barar da shi muddin Malam Hatimu yana raye.
---------

Tunda Abban ya kaimata Rukayya Rukayyan take ta magiya don Allah suyi cake tunda gobe da akwai makaranta kuma yanzu ta dawo na ta huta da dafa abincin makaranta.

Haka Aisha ta tashi ta hada kayan cake, da yake ta koyawa Rukayyan ma kusan duk ita tayi aikin da yake ba Mai yawa bane. Ta gama ta zuba cake din a oven tanayi tana wanke wanke, kafin magriba ta gama.

Ana idar da sallar magriba ta sa Rukayyan ta dafa musu indomie da kwai suka juye a tray suna ci suna hira. Sun kusan cinyewa aka buga kofa, Aisha ta tsame hannunta tana fadin

‘Cinye ragowar bari naje na duba kofa.’

Saida ta zo daf da gate din tace

‘Waye.’

Cikin isa aka amsa mata

‘Mune.’

Ko bata ga mai maganar ba ta san Yusra ce don haka ta bude kofar tana Lahaula a zuciyarta saboda sharrin yaran ya fara bata tsoro.

Tana budewa suka shigo ita da Sadik, ya dubeta shekeke yace

‘Ina Rukayya, Mommy tana kiranta.’

Ta juya tana fadin

‘Ku shigo tana ciki.’

Suka biyo bayanta.

Suna shigowa falon Rukayya ta mike tsaye da kwanon abincin nasu a hannunta zata kai kicin tana tande baki saboda indomie din da yaji. Suna karasawa ciki Sadik yace

‘Kizo in ji Mommy.’

Ta kalleshi da mamaki

‘Yanzu?’

Yusra ta balla mata harara tace

‘A’a gobe?’

Aisha ta karasa tana fadin

‘Ce miki akayi fa Mommy na kiranki kike tambaya Rukayya, kai kwanon kicin ki sha ruwa ki zo kuje in ya so kya dawo.’

Ta wuce kicin din ta ajiye kwanon ta fito, ta dauki hijabinta wanda tayi sallar magriba da shi a falon ta saka tace

‘Sai na dawo Anti.’

Suka tasa ta a gaba kamar wata mai laifi suka wuce.

Ta riga ta san wannan kiran ba na Allah bane don haka ta mayar da kofarta ta rufe don ta san ba za a bar Rukayya ta dawo ba.

Haka kuwa akayi, tana shiga gidan Mommy tace an gama kwanan ba zata sake taya wannan matar kwana ba. Tayi maganar kayanta aka ce yayyenta zasu kwaso mata gobe amma ita kam ma idan aka sake ganinta a kofar gidan sai an karya kafarta. Haka ta kwana tana matse kwalla saboda takaici; ga cake dinta a gidan wanda ta san bata isa tayi maganarsa ba don ko an karbo ba za a bari ta ci ba.
……….

Haka da gari ya waye Aisha ta tashi ta gama shirin zuwa aiki, a al’ada bakwai da kwata Malam Sule yake buga mata kofa su tafi, idan ya jiyeta sai ya wuce da yaran tunda makarantar da take koyarwa ta fi kusa.
A shirye ta zauna a kan kujerar dining table tana jiransu, da taga da dan sauran lokaci ta kirawo Yaya Zainab a waya ta sanar da ita zata zo in an tashesu daga makaranta ta dauki Amira;’yar wajen Zainab din ce wadda shekarunta sun kai sha uku. Ta sanar da ita Abba ya tafi Hajji kuma Zahra ta hana ‘yar tayin kwanan tata, in ya so daga nan sai ta dinga kaita makaranta da safe suna dawowa tare tunda saura sati biyu a bayar da hutun Sallah kuma tana sa rai kafin a koma Abban ya dawo.

Suka gama waya ta ajiye ta cigaba da kallon agogo. Har karfe bakwai da rabi ta gota bata ji bugun Malam Sule ba, don haka ta kirawoshi a waya. Kafin ma tace wani abu ya fara magana cikin girmamawa

‘Afuwan Hajiya, wallahi Hajiya Babbace tace yara suna makara don haka na wuce na kaisu idan na ajiyesu na dawo na daukeki. Kin ganmu a hanya dana kaisu yanzu zan juyo in Sha Allah Hajiya ayi hakuri da ni.’

Tace

‘Babu komai Malam Sule, ba ma sai ka dawo ba yanzu zan wuce babu komai.’
Chapter 26 · 0% Book details