← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 100

Sashe 57

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

‘To ai na ga kamar baki ji dadin dawowata bane shi yasa da zan dan koma na baki waje ko.’

Ta murgude bake zatayi magana, kafin ta bude baki ya sumbaci lebenta yayi dariya

‘Allah ya nuna min ranar da za a daina murgude min bakin nan na rashin kunya.’

Ta zumburo baki, ya sa hannu ya kara janyota jikinsa. Duk wata tsiwa da ta haddace zatayi ya goge mata haddarta, haushinsa take ji amma ta kasa ture shi. Yace

‘Na san dai kinyi kewata da yawa, to ba gani na dawo ba kuma shikenan sai a tare ni da murguda baki sai kace wani wanda bashi da galihu. Ai dole na koma tunda dama jakata a kulle take idan kika shirya sai na dawo.’

Shiru kawai tayi ta kwanta a kirjinsa ya rungumeta yana shafa bayanta. Tayi kewarsa kamar yanda shima yayi kewarta. Suna nan a tsaye suka ji motsin hawowa saman wanda kana ji ka san Ummi ne da Sumayya. Tayi gyaran murya ta dan ja baya don ta tabbatar shi ba sakinta zaiyi ba, tace

‘Yara fa suna nan.’

Ya ja baya ya koma ya zauna.

Nan ya zauna suka cigaba da hirarrakinsu shi da ita da Yara.

Jimawa kadan ya mike zai shiga daki, yace

‘Ayi abinci da ni fa a nan zan kwana.’

Ya shige dakin bayan ta amsa; yana so yace tayi abinci da Aisha amma yana tsoron fitna, don ya kula duk lokacin da yayi mata maganar Aisha to da fada suke rabuwa don haka ya hakura.
…………

Bayan sallar la’asar ne suna zaune gaba dayansu a falon a kasa ana ta hira, ya duba agogo lokacin karfe biyar da kwata. Ya san dai zuwa yanzu Aisha ta dan huta don haka ya dubi Mommy yace

‘Bari muje da yara mu yiwa Anti sannu da zuwa, yanzu zamu dawo.’

Ya dauki Sumayya ya tasa yaran gaba daya har Saddiku suka nufi gidan Aisha; domin ya san idan ba haka yayi ba bazasu je ba, shi kuma baya jin dadin wannan zaman da sukeyi kamar suna gaba da juna.

A zaune take a falo tana hutawa lokacin da suka shiga; cikin fara’a dalwala ta karbesu.

Bayan ta amsa gaisuwar kowa taki amsa gaisuwar Rukayya don haka bayan kowa ya gama magana Rukayyan ta sake cewa

‘Anti sannu da zuwa.’

Ta harareta tace

‘Bazan amsa ba Rukayya, sai yanzu kika zo inata nemanki.’

‘La Anti wallahi aiki nakewa Mommy shi yasa.’

Ummi tayi caraf tace

‘Abba kaga Anti tayi fushi da Yaya Rukayya.’

‘Shikenan sai muyi ta dariya.’

Aisha tace tana rungumo kafadar Rukayyan

‘To mun shirya, dama ba fada bane.’

Sukayi dariya gaba daya. Saddiku ne kawai bai saka musu baki a hirarsu ba yana zaune da hannusa wanda bai gama warkewa ba a rungume yana ta muzurai.

Ta tashi ta shiga daki, jimawa kadan ta fito da kaya ta ajiye ta koma ta sake dauko wasu ta fito ta ajiye sannan ta zauna. Ta janyo hannun Sumayya wadda take kan cinyar Abbanta, ta noke alamar ba zata zo ba. Ta dauko ‘yar tsana daga leda ta mika mata sannan ta mika mata alawa a 'yar karamar roba. Ta mika mata hannu tace
‘To zo mu shirya.’

Ta sake nokewa, tayi dariya tace

‘Sumayya kiwa.’

Ta bawa Saddiku takalmi sau ciki, Yusra da Nana da Ummi kuma kowa ta bashi abaya da agogo.

Akwai keken dinki mai aiki da wutar NEPA dan matsakaici na dorawa a kan tebur, ta janyo kwalin ta mikawa Rukayya tace

‘Chief fashion designer, ga keke.’

Nan take tasa ihu, ta sunkuci kwalin ta mikawa Abba cikin murna tace

‘Abba ka ga.’

Kafin ya amsa ta juyo tace

‘Anti nagode, kayan sallarki zan fara dinkawa.’

Tana dariya tace

‘Umm! Wannan dai mayi magana daga baya idan kin dinka na ‘yar tsana dai mayi magana.’

Duk gaba dayansu sukayi mata godiya, har sun mike ta mikawa Rukayya Leda tace kin manta da taki abayar. Abba ya karbar mata duka yaran suka wuce suka barshi a nan yana dauke da Sumayya. Ya dubeta yace

‘Wannan ai ke baki sayowa kanki komai ba yara kika siyowa, na zata ma kanki kika siyowa keken dinki.’

Tayi dariya

‘Ai ni bana son dinki itace take so, tunda suka je gidan Zahida da sallah ta gano kekuna kuma Zahida tayi mata alkawarin zata koya mata dinki shikenan ta kasa nutsuwa kullum dinki.’

Yayi mata sallama ya bi yaran a baya.

Yana shiga gidan ya tarar da su a falo sun baje gaban Mommy.

Rukayya sai murna take ta kasa zama guri daya saboda keken nan wanda ta riga ta fitar da shi daga kwalinsa.

Ya ajiye Sumayya ya wuce sama, ya shiga dakinsa ya kwanta don ya huta.

Da sallama ta shiga dakin, bayan ya amsa sallamarta ta zauna a gefen gadon wajen kafarsa. Ya gyara kwanciyarsa yana kallonta alamar ita yake sauraro saboda ya san wannan zaman da magana.

‘Mun ga tsaraba yara suna ta godiya.’

‘To ma sha Allah.’

Ta sake hade fuska sannan tace

‘Kuma wannan keken da aka siyo guda daya ina na Yusra? Tunda ka san itace dai Babba. Idan dai ba hada fada ba da so a raba min yara ai biyu ya kamata a siyo. Kuma abayar ma ita Yusra sai aka siyo mata iri daya da Nana ita kuma Rukayya tata ta fi kyau gashi harda wata jaka da turare bayan agogon. Idan ba hadin fada ba ai jaka ma da turare Yusra ya kamata a bawa itace 'yan mata tunda ko a makaranta yanzu SS 3 take yayinda Rukayyan take JS 3. Irin wadannan abubuwan ai su suke raban kan ‘yan uwa, duk abinda za a yi ko dai ayi musu tare ko kuma a fara yiwa Yusran tunda itace babba.’

Tunda ta fara maganar yake binta da kallo yana mamaki, ya tashi zaune yana binta da kallo yana murmushin takaici yayinda ita kuma take kara shan kunu. Yayi gyaran murya yace

‘To yanzu dani kike wannan hayagagar ko kuwa Aishan zan kirawo kiyi mata?’

Ta kara kulewa tana harararsa

‘Au hayagaga ma nakeyi ko? Ka kasa yin adalci tsakanina da matarka kuma yaran naka ma bazaka yi musu adalci ba saboda ana zuga ka ko?’

Ya tsani tace baya adalci saboda shi ya san iya karfinsa yana kwatantawa, yayi tsaki

‘Zahra kada fa ki gaya min magana saboda kinga Ina sauraronki. Duk abinda kika gani sun zo da shi Aisha ce ta siyo musu da kudinta don ni ban ma kwance kayan ba kuma ba wannan korafin ya kamata kizo kina yi ba godiya ya kamata kije kiyi mata. Tunda idan ban manta ba da kika je Umra banda dabino na ganin idona babu abinda kika bata kuma har yau ban ji korafinta ba. Idan kuma tafi yiwa Rukayya tsaraba ina jin ba sai na gaya miki dalili ba kema kin san dalilin ko. Saboda haka ki fita ki bani waje so nake na huta ba wai surutunki nake son ji ba.’

A fusace tace

‘Dole ka koreni tunda ka kasa yi mana adalci, tafiya Dubai din ma ai ba haka aka tsara ba amma da yake abun duk shiri ne sai kuka wuce da matarka saboda kai kanka ka san ni ya kamata ka fara zuwa dani wata kasar ba ita ba. Yara kuma ai da kudin ubansu aka yi sayayya don haka sai ayi musu adalci ni din dai da aka raina sai a cigaba da murdewa hakki.’

Mamakinsa ya karu saboda ya kasa gane dalilin wadannan maganganun da take zubawa haka barkatai. Yayi tsaki yace
‘Zahra, Aisha ita ta biyawa kanta kudin zuwa Dubai kuma duk wata tsaraba da ta yiwo kudinta ta saka tayi, zabi ya rage naki ko ki yarda ko kada ki yarda. Idan dai wannan shine rashin adalci to an ki ayi miki adalcin idan kina da karfi ki shake ni nayi miki adalcin. Ki fice min daga daki so nake na huta bana son wannan hayaniyar.’

Ta hadiye malolon da ya tokare mata makogoro tace

‘Shikenan saboda ka auro fitinanniya ba zan gaya maka gaskiya ba sai ka dinga korata, to wallahi…'

A fusace ya mike ya dauki mukullansa da wayarsa ya fice ya barta ba tare da ya gama jin abinda zata fada ba.

Ta share zafafan hawayen da ya gangaro kan kumatunta; ya kasa yi mata adalci yanzu kuma zai raba mata kan yara. Ta tabbatar wanna shirin Aisha ne. Kuma saboda ita ya mayar da ita ‘yar matsiyata shikenan komai sai ya bawa Aishan kudi yace da kudinta takeyi bayan musamman ta sa aka tambayar mata albashin Malaman gwamnati. Ta tabbatar kudinsa ne Aishan take facaka da su haka, amma zata yiwa tufkar hanci.

Tayi kwafa ta fice daga dakin
………..

Yana fita ya kirawo Aliko suka fice, ya kaishi gidan Yaya Bello. Can ya zauna har dare, ya shiga gidan Hajiya inda ya zauna suka ci abinci sannan ya kamo hanya ya dawo.

Lokacin da ya shiga gidan babu kowa a falo sai Rukayya da take zaune bata komai yayinda Yusra take kan dining table tana yin homework. Bayan ya amsa sannu da zuwansu yace

‘Rukayya taso na raka ki ki taya antinki kwana ko?’

‘To Abba, bari na dauko kayana.’

Ta shige dakinsu na kasa inda nan suke ajiye tarkacensu shi kuma ya haye sama, bayan ta fito ta haye sama.

Yana zaune a falon yayinda Mommy take zaune itama tana kallon TV, bayan Mommy ta amsa sallamarta tace

‘Mommy Abba yace zan je na taya Anti kwana.’

Ta kara hade girar sama da kasa sannan tace

‘To.'

Ya mike suka fice tare da Rukayyan.

Yusra tana nan a inda suka barta, har sun kusa fita daga falon Rukayya cikin sanyin murya tace

‘Abba.’

Ya juyo yana sauraronta
‘Na dauko keken dinkina na tafi dashi, na gama holiday homework dina kuma kaga sai next week za a koma bani da aiki.’

‘To dauko muje.’

Ta ajiye jakar makarantar dake bayanta a kasa ta koma dakin kasa da gudu ta dauko keken a kwalinsa, yana jin lokacin da Yusra ta faki idonsa tayi tsaki yace

‘ba sabun ba..’

Tana zuwa kusa da shi ya karbar mata keken ita kuma ta dauki jakar suka fice.
Chapter 57 · 0% Book details