← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 100

Sashe 80

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba karamin dadi taji ba lokacin da ta shiga gidan Yaya Murja ta tarar babu kowa a falon kasa; wanda falon amaryar Yaya Murja din ne. Kai tsaye ta haye sama, inda ta tarar da Yaya Murja zaune da yaranta suna hirarrakinsu. Cike da farin ciki yaran suka yi mata oyoyo, ta karasa ta zauna a kusa da yayarta. Gaba daya yaran suka matso suna gaisheta yayinda Yaya Murja ta umarci Hibba; yarinyarta ta uku wadda Yusra ta girmeta da shekara daya; ta debo ruwa ta kawowa antinta.

Bayan yaran sun gama gaisheta sannan ta fara gaisawa da Yaya Murja, a nan ta fahimci kanwar tata tana cikin damuwa don haka ta jata suka shige daki.

Suna zama a gefen gadon ta kifa kanta a kan cinyar Yaya Murja ta fashe da kuka. Bata hanata ba sai da tayi mai isarta tayi shiru don kanta, ta janyo tissue a kan durowar gefen gadon ta goge hawayen sannan Yaya Murja wadda take kallonta da mamaki tace

'Allah ya sa dai lafiya.’

Ta karasa face majinar da ta taru a hancinta ta ajiye tissue din a kasa sannan tace

'Yaya na rasa yanda zan yi da Abban Sadik, wallahi ji nake kamar an canza min shi.’

'To me kuma yayi?’

'Hmn! Yaya kin san har yanzu bai gaya min inda ya kai Saddiku ba? Gaba daya ma ko kula ni baya yi a cikin gidan harkar gabansa yake yi. Idan a kan abinda ya faru da Saddikun ne ai na bashi hakuri amma sai ya dinga faman share ni kuma ba zai gaya min inda ya kai min yaro ba, kashe ni yake so yayi tunda idan na mutu bashi da asara ya auri wata matar?’
Yaya Murja tayi murmushi ta kamo hannun Zahra ta rike a nata hannun tana kallon fuskarta a nutse, sai da suka dauki kusan minti daya a haka sannan tace

'Abinda nake so dake shine, kwata-kwata ki cire tunanin kishiyarki a ranki idan kikayi haka shine zaki iya fuskantar rayuwarki kiyi gyara a inda kike bukatar hakan. Kin ji ko?’

Ta gyada kai alamar ta fahimta, sannan Yaya Murja ta cigaba

'Abban Sadik mijinki ne kuma a halin yanzu laifi kika yi masa, ki sake kwantar da kai ki bashi hakuri. Ki sake janyo shi a jiki kamar yanda kuke da. Kuma ina son ki kwantar da hankalinki, Saddiku dansa ba zai taba cutar da shi ba don haka ki barshi ya nemawa yaronsa lafiya. Kada ki sake yi masa maganar Saddiku. Ki nuna masa duk yanda yayi da yaransa dai-dai ne, ke dai so kawai kike ku koma kamar yanda kuke a da. Ki kuma nuna masa duk wani laifi da kika yi masa da wanda kika sani da wanda baki sani ba ba zaki sake ba; domin kin san wani lokacin maza saboda mulki ba zasu gaya mana laifin ba sai dai muga sauyi a halayyarsu. Kuma kullum dare ki dinga tashi musamman ranakun da ba kwananki ba kina yin sallar dare kina addu'a, wallahi a hankali zaki ga komai ya dawo dai-dai.’

Ta gyada kai; ta sami natsuwa da wadannan kalaman duk da dai babu yanda za ayi ta cire kishiya daga lissafinta tunda ta san duk abubuwan da suke faruwa da ita sa hannu ne na kishiya. Amma dai tayi alkawarin zata gwada shawarwarin Yaya Murja.

'Shi Kuma Saddiku ki cigaba da yi masa addu'a amma don Allah ki bari a gina rayuwarsa. Kinga yaranki kamar mu suke, dukkansu mata sai shi kadai namiji. Idan ya bi hanyar lalacewa zasu taso basu da wani uba bayan ranmu. Kina kallo mu iyayenmu duka sun rasu yanzu Yaya Muhammad muke takama da shi; to da ya zama dan shaye-shaye ai da kinga bamu da sauran gata a duniya.’

Cikin sanyin murya tace

'Hakane.'

'Yauwa.'

Saida suka dauki lokaci Yaya Murja tana kwantar mata da hankali sannan da magriba ta fara kawo jiki tayi mata sallama ta kama hanya.

Duk yanda lokaci ya kure sai da ta tsaya a gidan Amina domin tana so ta samu tabbacin maganarsu tana nan ta zuwa wajen malamai.

Bayan a sun gaisa da Aminan ta rakata daki ta duba Ummansu wadda take kwance sannan suka dawo falon Aminan suka zauna.

A nan suka cigaba da kulla yanda da zarar Umma ta dan ji sauki zasu kai ziyara wajen malamansu don samarwa kansu mafita a aurarrakinsu wanda a halin yanzu suke cikin wani hali.

Sai bayan sun yi sallar Magriba sannan Zahra ta fito suka kama hanyar gida da Malam Ali.

—----

A ‘yan kwanakin nan jikin Hajiya kara rikicewa kawai yakeyi, duka da cewa Yaya Bello a tsaye yake a kanta. Kusan shekaru biyar kenan tana fama da hawan jini wanda daga baya ya hade mata da diabetes. Shi yasa ma kullum Yaya Bello yake zuwa yana bata abincin da kansa don ya tabbatar ta ci abinda ya dace. Sai dai duk da haka ‘yan kwanakin nan da an samu jininta ya sauka sai kuma diabetes din ya tashi, idan kuma ya yi sauki sai jinin ya sake hawa. Haka dai suke lallabawa.

Ranar Juma'a ce don haka da wuri Abban Sadik ya tashi daga aiki. Ya je ya gaida Hajiya da safe amma duk da haka yaji yana so ya sake komawa, don haka ba tare da bata lokaci ba ya juya kan motarsa ya nufi gidan Hajiyan.

A kwance ya sameta a dakinta tana hutawa, ya shimfida dadduma a gaban gadon ya zauna. Ta rage yawan hira sosai don haka a mafi yawancin lokuta sai dai kawai su sakata a gaba su zauna. Bai dade da zama ba akayi kiran sallar Magriba, don haka ya tasheta ya rakata har kofar bandaki ta shiga ta yiwo alwala. Sai da ta zauna a kan daddumar ta inda zata yi Sallah sannan ya fito ya barta da Anisa ya nufi masallaci.

A masallacin suka hadu da Yaya Bello wanda shi kuma ya zo ne don ya duba Hajiyan ya bata abincin dare.

Tuwon alkama da miyar zogale Yaya Bello ya kawo mata; wanda shine abincin da ta fi so tun da aka hanata cin shinkafa. Anisa ce ta dauko musu plate ta kai musu daki don yau Hajiyan gaba daya ta ki fitowa falo. Haka suka saka ta a gaba ta dan ci tuwon kadan tace ta koshi, sai shayin goruba da aka hada mata ta shanye kofi guda.
Ta koma kan gadon ta kashingida ta barsu zaune suna ‘yan hirarrakinsu a tsakaninsu.

Sai da akayi sallar isha'i sannan suka yi mata sallama suka tafi suka barta da Anisa da mai aikinta kamar yanda suka saba.

………

Tun ranar da Zahra taje gidan Yaya Murja ta dawo ta aikata duk abinda yayan ta bata shawara; tunda ta fuskanci a halin yanzu bata da wata mafita da ta wuce hakan. Don haka babu laifi Abban Sadik din yana dan sauraronta duk da dai har yanzu bai ce mata komai a kan Saddiku ba.

Kwananta ne yau don haka yana dawowa daga gidan Hajiya ya tsaya a gidan Aisha yayi mata sallama sannan ya wuce gidan Zahra.

Kamar yanda suka saba karfe goma sun gama komai ya rufe gida, shi da ita ma sun yi shirin bacci.

Tana kwance idonta a rufe domin bacci ya fara daukanta yayinda shi kuma yake zaune a gefenta da computer dinsa a kan cinyarsa yana aiki. Karar wayarsa ce ta farkar da ita, ta gyara kwanciya yayinda ya kai hannu kan durowar gefen gadon ya dauki wayar. Lokaci ya fara dubawa ya ga karfe sha biyun dare har da minti goma; sai da gabansa ya fadi domin ya san ba lafiya ba tunda yaga Yaya Bello ya kirawoshi a wannan lokacin.

Yana kara wayar a kunnensa kafin yayi wata magana Yaya Bello wanda kana jin muryarsa zaka san kuka yake yace

'Yusufa Hajiya lokaci yayi, sai dai muyi hakuri.’

'Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun!’

Katse wayar kawai yayi ya ajiye computer dinsa ya mike a dai dai lokacin da itama Zahran ta tashi zaune tana tambayar abinda ya faru. Ya dubeta yana fitar da kwalla yace

'Hajiya ta rasu, yanzu zanje na gani.’

'Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun! Allah Sarki.'

Sukayi shiru na dan lokaci yayinda ya cigaba da kokarin saka kayansa. Ya dauki mukullin motarsa ya nufi kofa, ta mike tana fadin

'Allah yayi mata Rahama, Allah ya hada fuskokinmu a aljannah.'

'Amin.'

‘Zamu taho da safe ni da yaran.’

'Ku bari sai mun yi waya tukunna, zan turo Ali ya kai ku.’

Yayi mata sallama ya fice.

……..

Kafin gari ya waye labarin rasuwar Hajiya ya zagaya gari. Karfe tara na safe aka gama hadata aka kaita makwanci. Sai da aka dawo daga makabarta sannan Abba ya sanar da iyalansa su taho, don haka gaba dayansu suka taho. Itama Aisha saida ta biya ta dauko Amira sannan suka wuce saboda ko ba komai ta samu wadda zata debe mata kewa a gidan.

Kafin yamma gida ya cika da dangi da abokan arziki, domin Hajiya Balaraba mace ce mai mutane sosai. Allah bai bata haihuwa da yawa ba domin yara hudu kawai ta haifa, kuma da yake ita kadai ce matar mahaifinsu sai suka zama basu da ’yan uwa. Duk da haka tana da dangi da yawa, domin mahaifinta yayi aure-aure kuma ya tara yara su goma sha takwas. Lokacin da tana da jajayen sawunta yanuwanta da suke mafi yawansu mazauna Sumaila ne suna zumunci da ita sosai, sai dai daga baya bayan rasuwar mahaifinsu Yusuf din da dukiyar ta kare a hankali kowa ya janye jikinsa. Yanzu kuma da aka sami labarin rasuwarta kowa ya zo ana ta kuka ana tuna alkhairinta lokacin da tana da hali.

Duk yaranta suma sun hallara da ‘yayansu, Ummulkhairi ce kawai bata iso ba wadda a Lagos take zaune inda aure ya kaita. An riga an sanar da mijinta rasuwar wanda yayi alkawarin shi da ita zasu biyu jirgi kafin magriba zasu iso.

……..
Chapter 80 · 0% Book details