← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 100

Sashe 40

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A cikin daren ta kirawo Amina tace ta samo mata direba, ita dai ba komai ta damu da shi ba kawai tana son wanda zai yi duk abinda tace ba tare da ya kawo mata tangarda ba. Idan ya gama koya mata tuki sai kuma ya dinga kai yara makaranta da motar Malam Sule da za a bashi.

Haka ta kwana cikin walwala saboda burinta ya kusan cika, itama zata mallaki mota ta dinga fita a gari kowa yana kallonta.
………

Ya riga ya sanar da Malam Sule cewa sati mai zuwa zai koma office da aiki saboda za a kawowa Zahra mota da sabon direba. Ko daya Malam Sule bai nuna damuwa ba saboda wannan abune da yake ta jiran faruwarsa saboda abubuwan da suke faruwa ‘yan kwanakin nan.

Yana office aka kirawoshi aka sanar da shi ga motar da ya saya ya fadi inda za a kai masa, nan take yace a kai masa gida amma idan an kai a jirashi a bakin gate.

Kusan lokaci guda suka Isa gidan da yaron da ya kai motar, maigadi ya bude musu gate suka shiga gaba daya. Bai gaya mata yau za a kawo motar ba don haka bata sa rai ba, ko da taji shigowar mota biyu ma tayi zaton shi da Malam Sule ne suka dawo a lokaci guda. Sun gama magana da Abban yau Malam Sule zai bar aiki kuma bata so ya dameta da wata sallama don haka tayi zamanta a falo.

Basu gama gyarawa motocin tsayuwa ba Malam Sule shima ya iso, bayan ya gaida Abban ya mika masa mukulli yayi masa sallama a kan zasu hadu a office.

Malam Sule yana fita ya sallami daya yaron ya karbi mukullin motar.
A falon kasa ya sameta tana chatting a waya yayinda Sumayya take wasanninta a tsakar falon.

Bayan ya amsa sannu da zuwa ta ya mika mata mukullin motar yana fadin

‘Ga mota, Allah ya sa direban naki ya shirya ku fara fita gobe don na san kin matsu ki fara yawo a mota.’

Kafin ya rufe bakinsa tayi tsalle ta mike ta karbe mukullin dake hannunsa tana godiya. Ta fice ta barshi yana kokarin daukar Sumayya.

Tana hango motar jikinta yayi sanyi, taci birki kamar wadda aka tare. Ta sake karewa tsakar gidan kallo don ta tabbatar wannan itace kadai bakuwar mota.

Dukkan alamu sun nuna hakan ne; yanzu wannan ce motar da Abban Sadik zai bata don ta dinga tukawa? Ita da take son mota ta kece raini kamar ta Aisha ko kuma wadda tafi ta Aisha amma ya siyo mata wannan? Ta matsa kusa ta karewa motar kallo, Honda Civic ce kirar 2009, ba wai muni tayi ba ko tsufa da yawa don fes take amma dai tana ga babu girma ace ta hau wannan Aisha kuma ta hau dalleliyar Honda Accord kirar 2013. Ko babu komai yanzu a 2018 ake, ina ma laifi ya bata koda accord din ce itana kuma ta 2013 misali.

Ta juya ta kalli kofar falon ko zata ga ya biyota amma sai ta ga babu kowa, tayi kwafa a fili tace
‘Haba ai da kunya ma ya bani wannan yace ya bani mota.’

Ta wuce cikin gidan ta tafi nemansa.

A daki ta sameshi ya ajiye Sumayya a kan gado yana kokarin cire kaya, bayan ya amsa sallamarta tace

‘Naga motar, nagode Allah ya kara budi. Ni da na sa rai da wata dankareriyar mota, wannan ma ai ta Malam Sule ta fita kyan gani.’

‘To sai ki ajiyeta ki dauki ta Malam Sule, wannan din sai a dinga kai yara makaranta ko?’

So take tace motar bata ma kai ta Aisha ba amma bata son janyo matsala; 'yan kwanakin nan duk lokacin da tayi maganar Aisha to fa sai ta kwana biyu bata gane kansa ba, haka zai yi ta kunci yana muzurai. Don haka ta ja bakinta tayi shiru.

……….

Tana zaune a falon kasa yara suka dawo daga islamiyya, bayan sun yi mata sannu da gida Yusra tace

‘Mommy naga wata mota a waje.’

Ta tabe baki ta kawar da kai

‘Wai ita Abbanku ya siyo min.’

Ta dan zaro ido

‘Mommy gaskiya Abba ya raina ki wallahi, wannan motar fa ina jin '98 ce ko rabin kyan ta amaryarsa bata kai ba. Ya za ayi ace tana hawa wannan motar ke kuma kina hawa wannan. Shima dai Abba!’

Kafin ta rufe baki Rukayya ta karasa kusa da Mommy ta dafata tana fadin

‘Congrats Mommy! Wataran muma kya dinga zuwa daukarmu a makaranta ko na cewa kawayena Mommy ta zo yanda suke min. Bari naje na kara kallonta, wallahi Mommy ta min kyau ina son mota kalar silver.’

Kafin Mommy tace wani abu tayi waje da gudu, Ummi ta rufa mata baya sunata murna Mommy zata dinga kaisu school.
Yusra tayi tsaki tace

‘Ji ‘yar kauye Mommy.’

Ta tabe baki kawai ta kawar da kai, Yusra ta cigaba

‘Mommy ya fa kamata ma ki hannan wannan tayin kwanan da Rukayya take zuwa, ace kullum mutum yana faman yawo wajen kwana. Kawai kowa tashi ta fissheshi.’

Sai yanzu tunanin ya fado mata, don da tayi wannan tunanin da tuni ta hana tunda yanzu duk abinda ta fada shi Abban yakeyi.

Jimawa kadan Yusran ta sake cewa

‘Mommy kika ce Malam Sule ya bar aiki, yaushe za a kawo Sabon direba?’

Ya ma zo dazu kun tahfiz, gobe shi zai zo ya kai ku makaranta. Sunansa Balele, sai goben za ki ganshi.
………..

Yana zaune a a falo shi da yaran gaba daya bayan sallar isha’i. Yusra tana zaune a dining table tana karatu su kuma Ummi da Nana suna zaune yana yi musu homework.

Rukayya ce ta fito daga daki dauke da jakar makarantarta, ta wuce kicin inda ta jiyo motsin Mommy. Bayan tayi mata sannu da aiki tace

‘Mommy sai da safe.’

Tana shirin juyawa tace

‘Ke na gaji da wannan tayin kwanan, koma ki ajiye jakarnan an gama daga yau. Ai naga itama a danginsu tana da ‘yaya don haka ta dauko mai tayata.’

Ta sunkuyar da kanta saboda damuwa, sai dai ta san babu yanda zatayi don haka ta ja kafa ta fice daga kicin din.

Daga inda yake zaune yana jiyo abinda take fada don da karfi tayi maganar, ba zai iya hanata ba don haka ya tashi ya tsallake yaran ya haye sama.

Bayan ta fito ta dubi Nana tace

‘Ina Abban kuma?’

‘Ya tafi sama, yace ki karasa mana homework din ko ke ko Yaya Rukayya.’

Tayi murmushi ta janyo littafin Ummi; ta san ya jiyo abinda ta fada ne kuma babu yanda zai yi da ita.
………

Bai iya yiwa Aisha waya ba sai dai text kawai yayi mata ya sanar da ita ta rufe kofa don Rukayya bazata zo ba yau.

Batayi mamaki ba don tuntuni take tsammanin hakan; ita din ma hakan ya fi mata nutsuwa don gani take kamar za a iya amfani da Rukayyan a cuceta. Don haka nan take ta tashi ta rufe gidan tayi kwanciyarta; ta bari sai nan da sati daya sai ta dauko Amira ta cigaba da tayata kwanan suga abinda hali zaiyi.
--------

Kamar yanda Yaya Zuwaira tayi alkawarin zata nemi shawara a wajen malamai hakan kuwa tayi. Ta sami Malama Halima wadda bayan ta ji duk wani bayani ta ja ta suka sami Malam Muhammad.
Yayi musu bayani sosai, ya tabbatar musu tsafi ne tunda daga karshe Aishan tace Abban yace kamar daga jikinta yake jin warin. Sai dai ya tabbatar musu idan aka cigaba da addu’a abun zai karye. Ya tunasar da ita azkar sannan kuma ya tuna mata addu’oin karya sihiri, ya sanar da ita ta dinga karanta surarul baqara kullum dare a gidan kuma ta dinga yawan sadaka da sallar dare.
Ya sanar dasu kada suce zasu rabata da shi domin don haka akayi wannan asirin, idan suka bari aka cigaba da addu’a komai zai wuce.

Tun da Zuwaira ta sanar da ita ta mayarwa kanta ka’ida kullum kafin ta kwanta bacci sai ta karanta suratul baqara, idan kuma ta kwanta karfe biyu da rabi na dare tana yi zata tashi tayi sallar dare sannan ta koma bacci.
…………

Ko da aka hana Rukayya zuwa sai tashi ya dan fara yi mata wahala kasancewar dama cikin da yake jikinta yana sakata bacci sosai sannan kuma idan ta tashi kasancewar ita kadai ce a gidan bata jin dadi sosai. Idan tana jin motsin Rukayya tafi natsuwa, ta dai tabbatarwa kanta lallai gobe zata dauko Amira tunda ma an gama jarrabawa hutun makaranta za ayi.

Yau ma kamar kullum karfe biyu da rabi na dare alarm din wayarta ya fara waka, ta lalubi wayar ta kashe alarm din sai dai ta kasa tashi. Wajen karfe uku saura kwata alarm din ya kara daukan kara; ta daure dai ta mike zaune bayan ta katse alrma din. Ta kunna fitlar wayarta ta ajiye a kan durowar gefen gadon saboda babu wuta a lokacin. Ta zauna tana hamma tana muttsike idanu tana kokarin ta wattsake ta tashi tayi sallah.

Haka kawai sai taji tsoro ya shiga ranta, nan take baccin ya bar kanta. Ta karewa dakin kallo duk da dai babu wuta amma tana iya ganin komai dake ciki dakin saboda fitilar wayarta da take kunne. A hankali sai ta fara jin kamar ba ita kadai ce a dakin ba, sai taji kamar akwai motsin mutum a dakin kuma motsin ma a nan kusa da ita inda take zaune a gefen gado. Ta duba har tana shafa gadon ta tabbatar babu kowa amma kuma kamar tana jin alamar da wani a kusa da ita.

Ta kasa tashi ta bar wajen kuma ta kasa aikata komai, har jikinta ya fara rawa a hankali saboda tsoro.

Ta dan muskuta kadan ta janyo abun rufar da ta rufe kafafunta da shi ta rufe kirjinta da shi ta kankame jiki.
Chapter 40 · 0% Book details