← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 100

Sashe 49

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda Abba ya kirawo Malam Ali direba yazo yayi aikin Sallah Malama Sule ya sami damar gujewa gidan; cikin dabara ya tsara Abban a kan a bar Malam Ali ya cigaba da kai yara makaranta yana daukosu. Don haka tun safe Abba ya sanar masa ya zama cikin shiri jirgin su Mommy ana sa rana saukarsa karfe biyar na yamma.

Lokacin yana yi Sadiku ya shige gaban mota Aliko ya ja suka kama hanyar airport.
………..

Alhaji Salihi Bello abokin Abban ne tun na kuruciya, tun cikin azumi aka yi masa ministan lafiya. Tun lokacin ya so shirya walima amma bai sami dama ba, sai ranar hudu ga watan Sallah shine ranar da aka ware domin yin wannan walimar ta taya shi murna a hotel din Bristol dake Kano.

An gayyaci Abba wannan taro kuma ya gama shiri shi da Aisha zasu je, hakan nema dalilin da yasa ya ce wa Mommy ba zai je daukota ba don yana so ya biya ta gidan Hajiya ya kai Aishan tayi mata gaisuwar Sallah sannan kuma su biya gidan Yaya Bello inda daga can idan sukayi Sallar Magriba sai su wuce wajen taron.

Bata taba shiga cikin abokansa da matansu ba, don a abokansa ma bai fi mutum biyu ba wadanda ta sani; duk sai sunayensu da take ji. Da farkon aurenta ya kai ta gidan mutum biyu sai dai tun a lokacin ta fahimci matansu duka kawayen Zahra ne don haka ta ja jikinta.

Sai da tayi alwala sannan ta tsantsara kwalliyarta cikin farar atamfa mai ratsin shudi, ta kawo luffaya mai kalar shudi wadda ta sha ado da fulawowi farare da duwatsu masu kyalli ta nade jikinta da ita.

Kunshin sallarta yana nan radau don haka ya kara fito da yatsunta da ta sakawa zobe me ruwan tasa sannan ta daura agogonta Fendi. Ta kawo takalminta mai matsakaicin tudu wanda ake kira wedge ta saka da jakarta Yar karama wadda ta dace da shigar. Goge fuskarta kawai tayi sannan ta dora jan janbakinta wanda yake karawa labbanta kyau, ta fito falo ta sameshi inda yake zaune sanye da farar shadda dinkin doguwar riga da wando da jar dara kamar yanda ya saba.

‘Na gama.’

Ta fada tana daga tsaye a bayan kujera, ya juyo ya dubeta ya mike yana murmushi yana fadin

‘Wannan kwalliyar ai sai ki sa a zata ni aka yiwa minister din.’

Tayi murmushin da ya kara mata kyau, ta sunkuyar da kai tana fadin

‘Allah Amin.’

Ya dubi agogon bangon dake falon yaga karfe biyar harda rabi, yazagayo yana fadin
‘Mu tafi.’

Motarsa tana bakin gate don haka har nan suka fita.

Dai-dai lokacin da suka fito daga gate din suna hirarraki a lokacin Yusra ta fito daga gidan commissioner tare da yarinyar gidan Rafi’a wadda kawarta ce. Tar ta hangosu ta kawar da kai; a ranta tace dama shi yasa ya cewa Mommy zai fita ba zai je daukanta a airport ba. Tabbasa tana dawowa sai ta gaya mata.

Suka shiga mota ya ja suka bar unguwar.

Ko minti talatin basuyi da tafiya ba Malam Ali ya dawo da Mommy.

Nan da nan gida ya rude yara suka hau sowa da tsalle ana ta oyoyo. A falon kasa ta zauna duk yaran da Jummai da Rahama suka gaisheta suna mata maraba; tuni Sumayya ta makale mata. Tana nan zaune a falon ta bawa Yusra da Rukayya mukullin dakinta ta bude ta share ta canza zanin gado sannan suka haye saman ita da yara.
Bata jima da zama ba akayi kiran sallar Magriba, ta lallaba Sumayya ta zauna a wajen Yusra taje ta yiwo alwala.

Tana fitowa daga alwala tace yaran duka suje suyi Sallah sai su zo ta basu dabino da bagaruwa wadanda ta zubo a jakar hannunta.

Nan da nan duka yaran suka ruga da gudu suka fice daga dakin, Yusra ce kawai tayi saura tana zaune a gefen gadon Mommy. Kafin Mommy tayi magana tace

‘Mommy wai Abba ya gaya miki inda suka tafi shi da matarsa?’

Da mamaki ta dubeta

‘Aisha? Ce min kawai yayi zai fita, ina yace miki sun tafi?’

'Nima bai gaya min ba, kawai dai naga lokacin da suka fita dab da ki dawo. Kinga kuwa yanda taci gayu kamar wata matar gonna, ina jin ma dai dinner zasu je fa.’

Cikin tsananin bacin rai tace

‘Um.’

Sukayi shiru na dan lokaci, daga baya Mommy ta dubi Yusran tace

‘kije kiyi Sallah.

Ta fice ta barta tana kaiwa da kawowa a dakin.

Wai yaushe Yusuf ya zama munafiki ne? Ba zai ma gaya mata zai fita da Aisha ba sai yace mata kawai zai fita? Har yanzu bata daina mamakin yanda akayi ya koma wajen Aisha ba.

Tana nan tsaye ba tare da tayi sallar ba yara suka shigo da murnarsu sunyi tasu sallar a basu dabino da bagaruwa.

Ta bude jakarta ta bawa kowa nashi sannan ta basu wani a leda tace su kaiwa Rahma daga nan sai su zauna a can tayi sallah.

Suna fita ta bude wardrobe ta lalubi wayarta wadda ta bari a gida, ta kunna wayar sannan ta sayi data. Ta kunna data din sannan ta ajiye wayar a kan gadon ta tayar da Sallah, ta san kafin ta idar da sallah sakonninta sun gama shigowa.

Tana idar da sallar ta mika hannu ta dauko wayar tana daga zaune a kan daddumar, nan da nan ta bude wayar ta fara duba sakonninta.

Sakon Hajiya Sharifa ne a sama wanda da alama ma yanzu yake shigowa; Sharifa matar abokin Abba ce wato Alhaji Jibrin Muhammad Minjibir; suna aminci sosai da Mommy, don ko da zata tafi Umra ma musamman tayi mata waya sukayi sallama.
Tana ganin sakon Sharifa tayi murmushi; yanzu haka har ta sami labarin dawowarta shine take mata maraba. Ba tare da bata lokaci ba ta danna sakon ya bude:

“Hajiyata ya ibada? Na san dai yanzu kun hado kaya ko ma kuna hanya.”

“Kina jin dadin kasa mai tsarki kin bar maigidan a hannun yara.”

“Ai gamu nan muna kallon soyayya shi da kanwarki, naga ta goge fes da ita.”

Sai hoto ya biyo baya, yana budewa taci karo da hoton Aisha da Abban Sadiku. Bata san me ya basu dariya ba don dariya suke a hoton sosai, ta kalli laffayan dake jikin Aishan; wato da yake bata nan shine ya sayowa Aishan wannan dandatsetsen laffayan. Ita kuwa ko da tayi maganar kayan Sallah cewa yayi banda ita tunda an kwashe kudi an biya mata Umra, idan taje ta saya a guzurinta.

Wai yaushe ma Abban ya rainata haka? Tayi kwafa.

Ta sake karanta sakonnin sannan ta bada amsa kamar haka

“Bikin wa akeyi ne haka?”

Shiru babu amsa ga dukkan alamu Hajiya Sharifa ta sauka daga online don haka ta fita daga sakonnin Sharifan.

Nan da nan ta lalubi lambar Yaron Malam don dama shine abinda take nema, ta budo ta fara yi mishi sako na murya wato voice note:
“Yaron Malam duk wani aiki ya rushe wallahi, don yanzu haka maganar da nake maka ya san zan dawo amma ya dauketa suka fice. Sati biyu kawai nayi da ‘yan kwanaki amma duk wani aiki da kayi min sun lalata shi wallahi. Gaskiya na gaji da zama da yarinyar nan yaron Malam, ban taba tunanin akwai matar da zata iya kasa min hankalin miji kamar yanda yarinyar nan takeyi ba. Ya kamata dai a tumbuketa daga rayuwarmu ni da mijina Malam.”

Kamar daman jira yake tayi magana nan take taga alamar yana kokarin turo da amsa, don haka ta dan saurara kadan. Nan da nan sakonshi ya shigo shima ta voice note kamar yanda ta tura masa:

“Hajiya ai na gaya miki yarinyar nan hatsabibiya ce, kuma wasu lokutan bata tabuwa don haka kinga dole sai mun bi lamarinta a hankali. Idan kika sami lokaci ki shigo sai kiji cikakken bayanin yanda za ayi. Amma nayi miki alkawarin ko ta karya komai kwarjinin da na baki in dai kin masa amfani da shi yana nan don ba zata iya karya wannan ba sai dai idan shi da kansa ne zai karya. Ki kwantar da hankalinki. Sai kin shigo din.”

Ta dan sami natsuwa bayan ta saurari wannan sakon don ta san ko da akwai wani dalilin da zai sa Abban yace zai mata wata tijara to ba zai iya ba saboda kwarjinin yana aiki.

A nan ta kirawo Amina ta sanar da ita dawowarta da kumma halin da ake ciki sannan daga baya ta kirawo su Yaya Murja da sauran dangi ta sanar da su dawowarta.
……….

Sai wajen goman na dare saura sannan Abban ya shiga gidan, tana jiyoshi ta tashi daga falon saman ta shige dakinta ta turo kofar. Bata dade da mike kafa a kan gadon ba ya tura mata kofa ya shiga da sallama; yana dauke da Sumayya yayinda Ummi take biye da shi tana surutu.

Ya karasa ya zauna a kan gadon, ya dubeta yana murmushi

‘Hajjaju mutan maka. Kun dawo lafiya ko?’

Tayi murmushi tace

‘Lafiya kalau, mun sameku lafiya?’

‘Alhamdulillah duk gamu nan lafiya kalau. Ummi tace an bawa kowa dabino da chocolate nima a bani nawa '.

Tayi dariya tace

‘Au harda kai ma.’

Suka dan taba hira kadan, tayi kamar bata san daga gidan Aisha yake ba. Daga karshe tace

‘Ga abinci can a dining table an dora, naga dare yanayi baka ci abinci ba.’

Yayi dariya yace

‘Haba Hajiya, daga dawowa sai ki sa mana baki a harkar gida ke da zaki huta. Ai Rahaman ta san ba a nan zan ci abinci ba, don na ma riga na ci abincin dare na.’

‘Um! Dama ni nace ta ajiye maka.’

‘To nagode amma na koshi.’

Sukayi shiru na dan lokaci, jimawa kadan yace

‘Bari naje, ina gidan kanwarki a can zan kwana in ya so gobe sai a fara rabon kwanan daga nan kafin nan kin dan rage baccin gajiya ko?’

Ya mike ya jefa Sumayya dake kan cinyarsa sama ya cafeta ta kyalkyale da dariya, shima ya sa dariyar yana fadin

‘Sarkin tsalle-tsalle, muje na mayar dake inda na daukoki Mommy ta huta ko kafin gobe a kara mana dabino da chocolate.’

Ya dubeta yace

‘Sai da safe ko? Allah ya huta gajiya.’

A can kasan makoshinta ta amsa
Chapter 49 · 0% Book details