← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 100

Sashe 73

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har bacci ya fara kwasarta fitsari ya takura mararta, don haka ta tashi ta shiga bandakin don yin fitsari. Tana sabule pant din da yake jikinta ta ga jini, nan da nan hankalinta ya tashi. Tayi fitsarin ta fito tana kokarin fita daga dakin kuma mararta ta kara tsanantawa da ciwo don haka ta koma ta durkusa a gefen gado.

Ta lalubo wayarta daga kan gadon ta kirawo Abban Sadik wanda yake office dinsa. Bayan ta sanar da shi halin da ake ciki yace ta shirya ya zo su je asibiti domin Malam Ali ya fita dauko Sumayya da Ummi daga makaranta.

Nan ya sameta a gefen gado tana faman dagewa saboda ciwo, ya kamata ta saka hijabi sannan ya rikota suka sauko. Jummai bata san halin da ake ciki ba sai da suka sauko; tayi mata sannu da fatan samun lafiya suka wuce asibiti.

Suna zuwa asibiti aka samu likita ya dubata saboda yanayi halin da take ciki. Scanning likita ya turasu wanda da kyar Abba ya riketa suka je dakin da akayi mata, aka bashi takardar ya rikota suka koma wajen likitan.
Cikin hanzari likitan ya karbi takardar ya fara dubawa, bayan ya gama dubawa ya kalli Abban yace

‘Alhaji sai dai ayi hakuri, yaro ne a cikinta namiji amma Allah yayi masa rasuwa shi yasa take bleeding. Yanzu zamu dubata mu taimaka mata ta haifeshi sai ayi masa sutura.’

Abban ya goge fuska yace

‘Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun, ikon Allah.’

Nan take ita kuma ta fashe da kuka yayinda mararta take kara kartawa. Nan da nan likita ya kirawo ma’aikatan jinya yace su saka ta a dakin labour room. Shi da Abban suka bi bayansu.

Aka shige da ita yayinda Abban ya tsaya, jimawa kadan ya lalubo waya ya kirawo Yaya Murja ya sanar da ita sannan ya kirawo Aisha da Yaya Bello ya sanar da suma halin da ake ciki.

Ba tare da bata lokaci ba Yaya Murja ta iso asibitin,nan suka tsaya ita da Abban suna ta jira. Sai wajen karfe uku na yamma sannan aka samu ta haifi yaron babu rai.

Likita ya dauki yaron ya mika mata yace

‘Sannu Hajiya, kin ganshi ko. Allah ya kawo wasu masu albarka.’

Ta share hawaye tace

‘To likita me ya kashe shi?’

Ya mayar da gawar ya ajiye ya dubeta yace

‘Allah ne ya kashe kayansa kinga kuwa sai muce Allah ya kawo masu albarka. Kar ki damu Hajiya wannan ba wani bakin abu bane a wajen mace mai haihuwa tunda ma ke kina da wasu yaran wannan ba zai zama matsala ba.’

Nan ya barta da ma’aikatan suna gyarata ya fito waje.

Bayan an gama shiryata aka fito da ita aka bata daki inda likita yace zasu riketa zuwa gobe saboda jininta ya dan hau. Aka nade gawar yaron aka bawa Abba. Bayan ya tabbatar an bata daki sun zauna ita da Yaya Murja ya sanar da ita zai je ya kaiwa Yaya Bello gawar ayi mata sutura sannan ya karbo musu abinci a gida.

Abba yana fita Yaya Murja ta matsa kusa da Zahra tace

‘Kiyi hakuri ki share wannan hawayen, in da rabo sai kiga kin haifi wani amma kina ta kuka sai kace karamar yarinya.’

Cikin shesshekar kuka tace

‘Yaya ya za ayi yaron da bai fi sati biyu ba aka duba aka tabbatar min kalau yake kuma yanzu ace ya mutu?’

Da mamaki Yaya Murja take kallonta tace

‘Hmm! Saboda ke baki taba yin bari bane shi yasa kike cewa haka. Ya za ayi ba zai mutu ba tunda rayuwarsa tana hannun Allah. Ki kwantar da hankalinki wannan ba wani abu bane, ke da kike da yara shida ai sai dai kawai ki cigaba da godiya ga Allah da fatan Allah ya sa wahala ta zama kaffara.’

Ta janyo flask din da tazo da shi ta had a mata shayi mai kauri ta sakata a gaba saida ta shanye. Jimawa kadan likita ya shigo yayi mata allura, kafin ya fita bacci ya fara fuzgarta don haka ta hakura ta kwanta ba da son ranta ba. Yaya Murja ta zauna a kan kujera tana jiran zuwan Suwaiba wadda tace zata biya ta taho da Rahma saboda jinya.

UWAR SADDIKU

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

37

Tun kafin Suwaiba ta fito daga gida ta kirawo Rahama, sai dai bata dauka ba. Don haka ta kirawo Innar su Rahman don ta sanar da ita zata zo sai ta dauki Rahma su wuce.

Rahama tana daki a kwance tana kallon wayarta da taga Suwaiba ce taki dauka, haka kawai jikinta ya bata gidan Zahra zasu ce taje ita kuma tayi alkawarin ba zata sake komawa wannan gidan ba.

Tana jiyo Inna ta fara magana da Suwaiba a waya tayi tsalle ta fito tsakar gidan, bayan Inna ta ajiye waya tace

‘Inna na gaya miki ba zan sake zuwa gidan nan ba, wallahi duk wani mutunci da kika ga tana yi idan mutum bai taba yaranta bane. Ni dai gaskiya bana son zuwa gidan nan.’

Inna ta jijjiga kai

‘Hakuri zakiyi, ko iya asibitin ne kije ki zauna da ita in ya so da an sallameta sai ki dawo. Tunda dai kin ga suna kallonki kina yiwa yayyenki irin wannan hidimar, hakuri zakiyi, yanzu Suwaiban zata karaso.’

Haka Inna ta sakata a gaba tana bata baki, ba tare da bata lokaci ba Suwaiba ta zo suka wuce asibitin.

Nan suka zauna a asibitin har magriba.
Ana idar da sallar Magriba Abban ya shigo, ya kawo musu abincin dare sannan kuma ya tahowa Zahra da wayarta wadda ta bari a gida lokacin da suka taho asibiti. Suna gaisawa Yaya Murja da Suwaiba sukayi musu sallama suka tafi. Jimawa kadan Abba ya yiwa Rahma sallama ya tafi ya barta da Zahra wadda take ta bacci saboda alluran da ta sha.

Sai da yayi magana da likita kafin ya bar asibitin inda likitan ya tabbatar masa zasu sallameta da zarar blood pressure dinta ya dawo dai-dai kuma ta daina ciwon kai wanda take ta korafinsa tun bayan da ta haihu.
…………

Tun a daren Abba ya sanar da Aisha, tayi maganar abincin safe ya sanar da ita Yaya Murja tace za a kai musu don haka ta bari idan yamma tayi sai ta dafa musu abincin dare suje tare su dubota; idan ba a sallameta ba zuwa lokacin.

Ta sanar da mutanen gidansu wanda kafin wani lokaci Hajiyanta ta yiwa Hajiyan Abban waya ta jajanta mata sannan kuma suka sa cewa gobe zasu je asibitin su dubota.

Suma su Yusra tunda Abban ya dawo gida suke ta tambayar labarin Mommy, don haka yayi musu alkawarin gobe ko bai je da su duka ba zai je da wasunsu idan dai ba a sallameta ba.
----------

Sai wajen karfe biyu Abba ya kirawo Aisha ya sanar da ita ta dafa wa Zahra abinci zai zo da anyi sallar la’asar su wuce asibiti. Nan da nan ta fada kicin ta dafa farfesun kaza sannan ta dafa shinkafa ta dafa macaroni tayi miyar dage-dage wadda ta sha nama sannan ta hada coleslaw. Ta sami flask ta cika musu da ruwan zafi saboda shan shayi.

Bayan ya fito daga office ne ya kirawo Yusra ya sanar da ita cewa su shirya ita da kannenta in ya dawo zasu je asibiti, tunda ranar Juma’a ce babu islamiyya. Nan da nan Jummai ta tayasu suka shirya ta tambayesu ko za a dafa wani abun Yusran tace Abba yace Anti Murja ce take kaiwa.
---------

Sai da ya tsaya a wajen Aisha ya ci abinci sannan Aisha ta shirya cikin abayarta mai kyau ta rufe kanta da mayafi mai kalar olive green ta dauki 'yar jakarta sannan suka fito. Suna fitowa ta zare mukullan motar daga aljihunsa tana dariya tana fadin

‘Ka gaji da yawa, bari na tukamu.’

Yayi dariya yace

‘Za dai ayi min wayo a more min mota.’

Itama tayi da dariya.

Suka karaso gaban motar ya bude booth yana fadin

‘Zuba abincin a nan da yara zamu je sai su zauna bayan motar.’

Suka zuba abincin ya zauna a gaban motar ta ja suka fito daga gidan.

Tayi parking a kofar gidan Zahra, Abban ya fita ya shiga don ya fito da yaran.

Gaba daya su sun riga sun shirya don haka yana shiga suka fito yana dauke da Sumayya yayinda yake rike da hannun Ummi ragowar suna biye da shi. Sai da Yusra tayi turus da ta hango Aisha a motar Abba tana tukawa, ya karaso da su duk suka shiga bayan motar.

Rukayya ce ta fara gaida Aisha wadda ta juya tana amsawa, suka suka gaisheta har Yusra saboda Abban ya riga ya shiga motar. Ta ja motar suka kama hanya.
Sai da suka kamo hanya sosai yacewa Aishan idan sun zo kan tin gidan gwamna ta tsaya zasu sayi fruit. Don haka suna zuwa ‘yar kasuwar nan da take kusa da Yahuza suya ta tsaya; da hannu ya yafito mai fruit din wanda ya taho da guda. Yayi masa lissafin lemon, ayaba da kuma apple na kusan dubu bakwai yace a saka a leda kuma ya taho da POS machine ya karbi kudin.

Nan da nan mutumin ya juya da hanzari ya dauki leda ya fara cikawa yayinda shi kuma Abban ya gyara zama ya fara laluben aljihunsa don dauko wallet dinsa wadda ATM card dinsa suke ciki. Sai dai ga mamakinsa babu komai a cikin aljihun; ya dan yi tunani yana rike da aljihun ya kalli Aisha wadda take kallonsa yace

‘Kin san na baro wallet din a falo!’

Tayi murmushi tana dubansa, cikin rada tace

‘Kanata santin shinkafata.’

Yayi dariya yayinda ta mika hannu inda kafarsa take ta dauko jakarta, ta zaro ATM card dinta ta mikawa Abban a daidai lokacin da mai fruits din ya karaso dauke da manyan ledodi guda biyu.

Abban ya fita ya karbi kayan ya saka a booth yayi amfani da katin Aisha ya biya kudin sannan ya dawo ya zauna, ta ja motar suka wuce.
Chapter 73 · 0% Book details