← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 100

Sashe 65

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

‘Eh, munyi magana da shi don nine ma nace masa ya barsu su fara a nan din idan sun fito da sakamakon mai kyau sai su tafi kasar waje karatun degree na biyu. Ina ganin kamar hakan zai fi tsari da tarbiyya musamman a wajen ita Yusra din. Kuma karatun ma na nan ai ba gagararsu zai yi ba kamar yaune zaki ga sun gama musamman da yake dukkansu suna da kokari sosai.’

‘Uhmm!’

Ta hadiye malolon da ya tokare mata makogoro.

Har yanzu ta kasa gane dalilin da yasa mutumin nan yake mata kwarjini, duk inda ka tsaya a gabansa sai ya sha gabanta ya cika maka ido. Yau din nan zuwa tayi ta kora masa jawabi amma gashi ta kasa, tayi zaton ma zata ga ya rage kwarjini saboda aikin da akayi a kansa amma sai taga kamar ma kara masa kwarjini aka yi.

Umman Muhammad tace

‘Hmmm! Ka san dai karatun a can yafi a nan nutsuwa da sauri Alhaji, sai dai kawai da yake kayi maganar taribiyya amma fa da banbanci.’

Yayi gajeriyar dariya yace

‘To ai komai lokacine, yaran da wataran ma da kansu zasu kai kansu duk inda suke so a duniya musamman shi Saddikun da yake namiji.’

Tayi gyaran murya tana murmushin yake

‘Bari na tafi don nayi sauri na koma.’

Suka mike kusan lokaci guda ita da Umman su Muhammad a dai-dai lokacin da Shukuriyya ta fito dauke da tray ta doro waina da kili_kuli.

Nan da nan Umman ta karba ta koma kicin din ta juyo a roba ta fito mata dashi sai dai kafin ta zo har ta ja mota ta tafi. Ta dubi Yaya Bello da yake tsaye a bakin kofar falon tace

‘Laa! Kuma sai ka barta ta tafi bata karbi wainar ba Alhaji ai abun marmari ne kuma mutum ya gani.’
Yayi murmushi

‘Bata so karba ba. Ba zuwa tayi muyi magana ba zuwa tayi ta yi min rashin kunya kuma bata isa ba. Ina jin ya gaya mata na hana ya kai yara waje karatu shine ta zo kuma bata sami yanda take so ba, ko baki kula da yanda take magana bane?’

‘A’a ina kula sai dai da yake ni tunda ya kara aure haka muke da ita, da kyar take kulani don haka ni bata ma damuna shi yasa yanzun ma na zata nice bata son gani ashe kai din ma ka shiga gonarta.’

Ya juyo ya dawo cikin falon ta biyoshi a baya tana mita

‘To kai kuwa Baba ka kyalesu mana, tunda yana da kudin.’

Ya zauna sannan ya bata amsa

‘Ba zan kyalesu ba! Yusufa ai danuwana ne kuma idan yaransa suka lalace dole abun ya shafi zuri’armu. Da ma wasu nutsattsun yara ne da sai ace, musamman shi Saddikun. Bari su gama a nan din tukunna muga hankalinsu.’

‘Ai shikenan, Allah ya bada sa’a.’

--------

Tunda ta dawo daga gidan Yaya Bello Abba yaga yanda take cika tana batsewa ya san bata sami yanda take so ba, don haka ya kawar da kai kamar bai ganta ba. Haka ta karasa wunin tana ta faman kunci, tunaninta ma yanda zata gayawa yaran musamman Saddiku wanda yake ta faman murna yana gayawa abokansa wadanda yanzu yawanci suna level 2 cewa shi Dubai zai tafi kuma ba zasu rigashi gama degree ba.

Sai dai shi Abban yaji dadin wannan hukuncin kawai dai yana mamakin yanda tafi shakkar Yaya Bello fiye da shi.

Bayan Sallar isha’i ne suna zaune a falon sama har yaran suna hirarsu, Yusra ce ta shigo da sallama daga falon kasa. Kujerar da take kusa da ta Abban ta zauna, bata jima da zama ba tace

‘Abba wai yaushe zamu yi jarrabawar ne? Wadda kace zamuyi don samun admission a Dubai din.’

Ya kalleta

‘Oh, Mommy bata gaya muku ba ko? Ai an fasa zuwa Dubai din, na yanke hukunci da ke da Yayan naki kuyi first degree a nan BUK in ya so idan kun gama sai ku tafi duka kasar da kuke so don yin second degree. So yanzu idan result ya fito BUK za a nema, daman kin ga ita kuka cike a JAMB form ko?’

Nan take idonta ya ciko da kwalla, Mommy wadda take zaune a kusa da shi ta tashi ta shige dakinta. Yusran ta zumburo baki

‘Abba! Haba Abba, don Allah Abba ka bari mu tafi.’

‘An gama magana Yusra, nan din ma degree zakuyi irin na can so babu wannan zancen. Amma nayi miki alkawarin idan dai kika fita da first class to in Sha Allahu ko ban biya miki ba zan nemar miki scholarahip ki je UK ma kiyi masters kinga na can ya fi daraja.’

Ta share zafafan hawayen da suka gangaro kan fuskarta, ta tashi ta shige dakinsu na sama ba tare da tace masa komai ba. Ya bi bayanta da kallo yana jijjiga kai, ya san abun da haushi amma bai ji dadin yanda tayi masa hakan ba sai dai ya san wannan din dabi’ar uwarsu ce. Ya cigaba da hirarsa da suaran yaran, sai daga baya suka tashi kowa ya tafi makwancinsa.

Tun kafin gari ya waye Yusra ta sanar da Saddiku abinda Abba yace, nan da nan ya rikice. Ya sami Mommy a dakinta ya sa mata kuka; yana tsugune a gabanta Yusra ta shigo ta zauna a gefen gado kusa da Mommy din. Ta kalli Saddikun ta kawar da kai, tace

‘Mommy don Allah ki yiwa Abban magana mana, wai me ma yasa zai canza magana bayan an gama maganar nan?’

Taja tsaki ta kawar da kai

‘Wai ubanku ne Bello yace ba zaku je Dubai din ba sai dai BUK, nima babu yanda banyi dasu ba don jiya ma da safe da na fita gidan Bellon naje. Yace wai a barku saboda tarbiyya, ko kuma tsabar bakin ciki ne oho! Tunda yaransa BUK sukeyi to dan kowa ma yayi BUK.’

Saddiku ya dubi Mommy yace

‘Wallahi Mommy na dade da sanin mutumin nan dan bakin ciki ne, ina ruwansa tunda ba da kudinsa za a je ba?’

Yusra tace

‘Uhm! Yanzu ai sai ya zuba ruwa a kasa ya sha tunda zamu zauna muyi BUK kamar yaransa. Mtsewww! Na tsani dan sa ido wallahi.’

Saddiku ya dora hannuwansa a kan gwiwar Mommy yace

‘To yanzu Mommy babu abinda zaki iya yi a kai?’
‘Da zan iya da tuni nayi, ka san shi da bakin taurin kai.’

Ya dafa kansa da hannuwansa biyu

‘Amma gaskiya ya cuceni Mommy, duk friends dina na gama gaya musu zan tafi Dubai amma gayen nan ya sa aka fasa. Allah ya isa wallahi.’

Tace

‘Ka barni da shi, zan yi maganinsa kwanannan.’

Nan suka gama hirarrakinsu suna ta zagin Yaya Bello. Daga baya suka sanar da Mommy cewa idan hakane ta yiwa Abban magana su in ba za a kai su Dubai din ba to sun fi son Maryam Abacha University. Duk da bata san yanda zai dauki wannan zabin nasu ba amma tayi musu alkawarin zata yi iya yinta taga a kalla sun sami nan domin ko babu komai dai kada suyi Jami'ar da ‘yayan Bellon suke yi wato BUK.
__

Kwanci tashi har an fara yiwa azumi lissafin abinda bai fi wata daya ba. Zuwa yanzu duk wanda ya ga Aisha ya san tana da damuwa, sai dai duk yanda ‘yan uwanta suke so su rabata da gidan Yusuf ta ki yarda. Suna nan dai ita da Amira, duk da bata rasa komai ba amma rashin ganin Abban yana damunta. Ko a hanya bata ganinsa, kusan kamar ma dai suna rayuwa a mabanbanta duniyoyi.
Bata taba fasa addu’a da sadaka ba, ga addu’ar karya sihiri wadda kullum sai tayi kuma Hajiya ma sai ta yi ta aiko mata da ruwan. Tun tana lissafin kwanaki har ta gaji ta daina; abinda ta rike kawai shine Allah ya amsa addu’arta lokaci kawai ake jira.
………..

Ranar Juma’a ce kuma da yake ta kama ranar hutun aiki Zuwaira, Zainab da Aisha da Zahida gaba daya su da yaransu sun hallara a gidan Hajiya. Don haka sai kaiwa da kawowa akeyi, Farha da Abdallah wanda yake shirin zana common entrance suma suna nan a cikin dangi. Mijin Zahida ne ya bawa Hajiya kujerar Umra wadda zasu tafi cikin azumi don haka kowa murna yakeyi.

Can wajen karfe biyar na yamma lokacin kowa ya fara shirin tafiya Yaya Abubakar shima ya shigo tare da babban yaronsa Abulkhairi. Bayan sun gaisa ya dubi Anti Uwani yace

‘Anti Uwani family meeting kuke yi ne aka wareni?’

Tayi dariya tace

‘A’a wa ya isa ya wareka? Nan da ka gansu duk dadin baki suka zo su yiwa ‘yar uwata zata tafi Umra su samu ta tafi dasu ni kuwa ina kallonsu da ni zata duk a Nigeria zamu barsu.’

Yayi dariya yace

‘Ai kuwa a Nigeria zaku barsu Anti Uwani don kema da taki kujerar nazo.’

Zahida tayi caraf tace

‘Allah Yaya da gaske.’

Ya daga kai

‘In Sha Allah na ma gama biyan kudin sai su tafi tare, nima don dai ban dade da komawa sabon office bane da dani za a.’

Nan take Zahida ta zabga guda, kafin ta dire Yaya Zainab ta harareta tace

‘To sarkin bidi’a, da an yi motsi sai ki kama wani nanannen hanciki.’

Suka kyalkyale da dariya.

Nan suka hau sabuwar murna gaba daya. Hajiya ma sai tafi Anti Uwanin murna domin sai da ta matse kwalla saboda jin dadi. Haka ta dinga sakawa Abubakar albarka tana addu’a Allah ya kara masa arziki.

Haka Anti Uwani ma sai ta rasa inda zata saka ranta don murna, tayi ta sa musu albarka tana musu addu’a. Ta matsa kusa da Hajiya ta dafa ta tace

‘Yaya, Yaya Kinga dana ko? Na rasa bakin godiya Yaya. Tunda kika haihu ban taba kukan rashin haihuwa ba, kullum godewa Allah nake da bai bari na sha wahalar goyon ciki ba kika sha mana wahalar ke kadai kika haifo min ‘yaya. Gashi nan kinyi shuka sai girbar alkhairi nakeyi hankalina kwance.’

Hajiya tayi dariya tace

‘Naga alama kam to ina binki bashi kenan na wahalar nakuda.’

Suka sa dariya gaba daya
Chapter 65 · 0% Book details