← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 100

Sashe 50

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

‘Amin.’

Ba tare da ya kalli fuskarta ba ya fice daga dakin ya ja mata kofa, yana saukowa kasa ya ajiye Sumayya ya cewa Sadiku wanda yake zaune a falon ya tashi ya fita ya koma dakinsa Rahma ta rufe cikin gidan.

Duk gajiyar da ta kwaso bata samu tayi baccin kirki ba saboda yanda take takaicin kasancewar Abban a wajen Aisha; kusan sati uku basu ga juna ba amma shi ko dokin ganinta baya yi, ya tafi wajen amaryarsa saboda ya nuna mata bata isa ba.
------

Ko da gari ya waye ranar asabar ce babu aiki don haka sai wajen karfe goma suka tashi daga bacci. Nan da nan ta hada musu abincin safe suka ci suka shirya.

Wajen sha daya da rabi yace mata zai je gidan Zahra, take ta dauki mayafin abayar da take jikinta tana fadin

‘Bari na zo muje sai nayiwa Mommy sannu da zuwa na dawo kada tsaraba ta kare gara na karbo tawa da wuri.’

Yayi dariya yace

‘Ko kuma na karbe taki da tawa ba.’
Suka fice suna dariya.

Babu yabo babu fallasa ta tarbesu don har ruwa da lemo ta sa aka kawowa Aishan; sai dai hakan bai hana Aishan ta gane yanda Zahra take kare mata kallo ba kamar mayunwacin karen da ya ga abinci. Suka gaisa tayi mata Allah ya sanya alkhairi, jimawa kadan tayi musu sallama; Mommy ta mike da kanta ta debo mata dabino da bagaruwa ta bata sukayi sallama ta tafi ta bar Abban a nan.

Kafin Abban ya shigo sunyi waya da Amina ta gaya mata idan Abban ya shigo kada ta wani tada hankali, ta gaya mata ta lallaba shi domin akwai wani malami ta da zata kaita wajenshi domin shi aikinsa kamar yankan wuka ne. Idan suka je sai yanda taga dama zata yi da Abban don haka ta bata shawara kada ta daga masa hankali; ta huta na sati daya in ya so sai ta zo suje. Kawai dai ta sanar da ita ta tanadi kudi domin su hada aikin biyu; da na yaron Malam da na wannan sabon Malamin domin ayita ta kare kawai a gama labarin Aisha.

Don haka duk wata fitna da ta tanada zata yi bata yi ba, musamman da ta ga alamar har yanzu yana shakkarta kamar yanda ta tafi ta barshi.
_

Tunda ta dawo take tunanin inda zata sami kudi, amma duk wata dabara ta kare mata. Business din ma ya dan durkushe tunda harda kudaden business din ta hada ta tafi Saudiyya da niyyar zata saro abaya; sai dai bata saro abayar ba kuma ta kashe kudin.

Tana dan samun a wajen Abban amma da dabara take yaga da dubu ashirin da goma, zata dauki lokaci bata tara yawan abinda take so ba. Gashi ita ba ma’aikaciya ba balle ta tara albashinta. Tayi tunanin ko zata sayar da babban saitin gwal dinta amma gaskiya bata jin zata iya saboda tana sonshi kuma idan ta siyar shine kadararta ta karshe; don haka wannan ma ba zai yiwu ba. Ta san Suwaiba zata iya bata kudin rance to amma idan ta bata sai ta gayawa Yaya Murja, don haka ta hakura.

Kusan kwananta biyar da dawowa kafin dabara ta fado mata.

Bayan yayi mata sallama ya tafi wajen Aisha tunda a can zai kwana; Saida ta tabbatar kowa yayi bacci a gidan sannan ta shiga dakin Abban ta turo kofa. Ta riga ta san inda yake duk wata ajiya, duk wata takarda da yake ajiye da ita ta san inda take.

Wani karamin bakin akwati ta dauko daga wardrobe din can saman, ta koma kan gado ta zauna. Akwatin yana da password amma ta dade da sanin password din ba tare da Abban ya sani ba.

Nan da nan ta bude akwatin ta fara duba envelope din ciki tana neman takardar, sai da ta bude kusan guda biyar sannan ta sami takardun da take nema.

Tayi murmushi ta zare takardun daga cikin envelope din ta ajiye a kan gadon da take zaune. Ta mayar da akwatin ta rufe ta tashi ta taka wardrobe din ta mayar da akwatin.

Ta kwashi takardun ta fice ta nufi dakinta cikin tsananin farin ciki.

Tana shiga dakinta ta zauna a gefen gado tana duba takardun tana yiwa kanta murmushi; takardun fili ne wanda Abban ya saya da sunan Saddiku. Ya sanar da ita lokacin da ya saya kuma ya gaya mata filin ba kato bane amma dai ya sayawa Sadikun ne saboda nan gaba. Sun gama magana da Amina an samo mata wanda zasu sayi filin a kan kudi sama da miliyan hudu, a hakan ma sunce don ba a kewaye filin bane. Ta gama lissafin idan ta siyar ta biya malamanta suka yi mata aiki canjin sai ta zuba abusiness dinta da ya durkushe.

Ta yiwa kanta dariya ta tashi ta adana takardun nan a kasan katifar dakinta, sannan ta koma ta kwanta.
__
Tunda ta dawo daga Saudiya Saddiku ya hanata motarta, shi yake hawa motar nan kullum musamman da yake baya wani karatu yana zaman jiran sake jarrabawa; sai dai kawai ya zo ya tambayeta kudin mai ko kuma idan ya ballo gyara ya zo ta bashi kudin.

Dole ta hakura da motar Malam Ali Direba da da ta kwace tunda tatan Sadiku ya hana; sai dai shi Sadikun ya kaita duk inda zata ko Malam Ali ya kaita.

Duk lokacin da Abban yayi magana sai tace wai duk abokan Sadikun wadanda ma iyayensu basu kai Abban kudi ba an basu mota amma shi ya hana Sadiku; idan kuma ya bi abokan yace zai bi ‘yan shaye-shaye. Don haka ya hakura ya sa musu ido.
--------

Abokinsu ne Tijjani Tukur wanda suke kira TT yake birthday, don haka ya shirya party a gidansu da yake unguwar Lodge Road; da yake iyayensa ba sa gari.

Sai wajen karfe tara na dare aka fara fatin, suka hadu maza da mata sukayi ta sakarci, wadanda suke shaye-shaye a cikinsu ranar kowa kyauta TT ya basu kwaya irin wadda suke so.

Saddiku ya san Abbansa yana gari don haka yake ta kokarin dawowa gida da wuri, shi da abokinsa Munir wanda dama a wajen Saddikun zai kwana. Sai wajen goma da rabi na dare suka samu suka fito daga wajen kuma duk su biyun a buge suke.

Take Sadiku ya fada kujerar direba ya fizgi motar da gudu; babu mutane sosai don haka suka sami sararin gudun.

Mutum suka hango a tsaye a gefen titi yana haska karamar tochila, Munir ya dubi Saddiku yace

‘Ga mutanenka can 'yan KAROTA har an fara tsayar da mu.’

Ya kyalkyale da dariya yace

‘Kuma ba zan tsayaba ba, bari ka ga tsiyar da zan masa dan iska kawai.’

Ya kara taka motar yayi kan mutumin wanda ya zura da gudu, sunata dariya shi da Munir din yayinda yayi wuf ya fara kokarin mayar da motar kan titi. Babu wanda ya san yanda akayi sai gani akayi motar ta kwace ta daki fitilar titi ta dawo tsakiyar titi tayi tsalle sannan ta kife. Gilasan motar suka tawarwatse sannan injin ya mutu.

Tsirarun mutanen da suke wajen suka karaso da hanzari harda mutumin da suka kusa kwashewa; nan da nan aka fara kokarin zaro su.

Ihun Munir kawai ake ji domin shi Sadiku tuni ya sume, sai jini da yake fita daga wasu bangarori na jikinsu.

Kafin wani lokaci Jamai’an road safety sun bayyana, don haka aka kwashesu sai asibitin Murtala.

Ba a sami wayar Munir ba amma jami’an road safety din sun sami waya guda daya wadda ta Saddiku ce. Sai da aka shigar da yaran dakin bada taimakon gaggawa wato Accident and Emergency na asibitin Murtala sannan jami’in da wayar ke hannunsa ya samu ya bude wayar. Duba jerin sunayen dake cikin jerin lambobi yake har yazo kan lambar da aka saka Daddy; ba tare da bata lokaci ba ya danna mata kira.
…………

A kwance yake a falo Aisha tana yi masa tausa, wayarsa da take chaji a gefe tayi kara. Ta mike ta dauko wayar tana fadin

‘Waye wannan da tsakar dare?’

Tana kallon wayar tace

‘Kaga kuwa Saddiku ne.’
Cikin hanzari ta mika masa wayar ya karba, tana dab da tsinkewa ya amsa yana mamakin abinda yasa Sadiku zai kirawoshi a wannan daren; don ko haka kawai ma basu fiya waya da Saddiku ba don duk abinda yake so uwarsa yake gayawa ta sa ayi masa ko ana so ko ba a so.

Yana dauka kafin yace wani abu aka yi masa sallama daga daya bangaren da muryar da ba ta Saddiku ba. Cike da tsananin mamaki ya amsa sallamar inda kai tsaye mai sallamar yace

‘Sunana M. K. Takai, jami’i ne na hukumar road safety, zamu so muji alakar ka da mai wannan wayar da nake kiranka da ita.’

Yayi gyaran murya cikin sanyin jiki yace

‘Ni mahaifinshine.’

‘To Alhaji yaronka yayi hatsarin mota a nan kan tin gidan gwamna, a halin yanzu muna dakin bayar da taimakon gaggawa na asibitin Murtala da yake cikin birni. Zamu so ka zo domin kaga halin da yaranka suke ciki domin su biyu ne a motar.’

‘Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun! Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun. Officer gani nan zuwa yanzu-yanzu in Sha Allah.’

Ya ajiye wayar ya mike da gaggawa ya nufi daki, ta bishi da sauri ta sameshi a gaban durowar mudubi ya dauko mukullin mota ya juyo.

‘Me ya faru da Saddikun ne? Fita zaka yi?’

Ya dan tsaya yana fuskantar ta sannan yace

‘Accident yayi, ina jin a motar Mommynshi ne. An dai ce yana Murtala yanzu zan je na gani.’

Ya wuceta ya nufo falon da sauri, ta sha gabansa a falon yana dab da fita.

Ta kama hannunsa tace

‘Tsaya kaji mana. Ka san fa yanzu babu security kada kaje fa trap ne aka yi maka don ka fito, ka san yanzu babu wuya an yi kidnapping mutum.’
Chapter 50 · 0% Book details