← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 100

Sashe 42

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A labarai Network News Abban ya gani cewa WAEC sun fitar da sakamakon don haka a take ya ce a kirawo Sadik ya zo a duba masa nasa a computer din Abban.

Yusra aka tura taje dakinsa wanda yanzu ya koma boys quarters ta kirawoshi, an yi sa a yana nan don haka kafin Yusran ta gama gyara zamanta ya shigo falon.

Da mamaki Abban ya kalleshi, har ya karaso kusa da shi ya zauna sannan yace

‘Kai meye haka ne zaka taho kamar zaka fada kan mutane.’

Ya sunkuyar da kai yana fadin

‘Wallahi bacci nakeyi Abba ta taso ni.’

Nan ya umarceshu ya dauko katin inda yace masa yana wajen Mommy. Ba tare da bata lokaci ba ta tashi ta dauko katin tare da computer din Abban ya karba ya duba masa sakamakon.

Yaci komai da sakamakon mai kyau sai dai bai ci English ba, wanda kuma dole sai da shi ake admission a halin yanzu.

Abban ya dubeshi yace

‘Baka ci English ba, ya akayi haka?’

Ya shafa kai

‘Wallahi Abba ina jin matsala muka samu don duk ‘yan makarantar tamu da muka yi exam tare har yanzu bamu ga wanda yaci English din ba.’
‘Babu wata matsala, kun dai fadi kawai. Ai da matsala kuka samu rike sakamakon za ayi a saka muku pending ko awaiting result. Kun dai fadi English kawai, amma zanje makarantar naji.’

Mommy tace

‘To yanzu ya za ayi da admission din nashi?’

‘Ai babu wannan zancen kuma har sai ya sake jarrabawa ya sami English wannan ai ko a nan Nigeria ba zai sami admission din ba. Kasashen waje kuma ko sun bashi admission rashin wanna English din sai yayi affecting dinsa a nan gida. Next year sai ya gyara mu gani, amma dai gobe zanje makarantar naji yanda za a yi.’

…………

Kamar yanda yayi alkawari haka yayi, yana fita ya tsaya a makarantar su Sadik. A nan principal yayi masa bayanin cewa su Sadik su biyar ne suka sami F a English, saboda sun yiwa malamin da ya zo da jarabawar rashin kunya; su dai a makarantar suna tunanin abinda ya sa ya kada su English din kenan.

Har ya tashi zai tafi principal ya tsayar da shi, yace

‘Yallabai kuma a dan duba yaron nan don ka ga da yaron babu ruwanshi amma zuwa lokacin da suka gama jarrabawa gaskiya yaran da yake bi gaskiya duk suna shaye-shaye. Gara dai a bincika kafin abun yayi nisa.’

Yayi masa sallama ya tafi yana mamaki; Bai taba zargin Sadik ba amma yanzu kam dole ya dau mataki.

Bayan ya dawo daga aiki ko abinci bai ci ba ya sa Mommy ta kirawo masa Sadik, har zata fita ta barsu yace ta dawo ta zauna.

Ya dubi Sadik din yace

‘Su waye abokanka? Kuma meye gaskiyar magana da aka ce min kuna shaye-shaye?’

Ya zare ido

‘Wallahi Abba babu abinda muke sha, gaba dayan abokan nawa ma Mommy ta san su.’

Ya kalli Mommy.

Tace

‘Gaskiya na san abokansa dukansu babu wanda yake shaye-shaye, yaran da har nan din ma suna zuwa.’

Duk yanda ya so yayiwa Sadik fada Mommy bata bari ba, tun yana kokarin fadan har ya gaji yayi musu shiru.

Kuma da yake gaba daya yaran sun riga sun gane duk yanda Mommy ta fada haka akeyi don haka duk abinda basa so yayi magana a kai sai su tsara Mommy, don haka haka Sadik ya sa ta gaba a kan karya akeyi masa. Shikenan a haka zancen ya wuce.

Haka ya cigaba da tara abokansa suna shaye-shayensu da sakarcinsu.

Jummai tana kallon abubuwan da suke faruwa amma babu yanda zata yi don haka ta sawa abun ido.
--------

Tun ranar da suka dawo daga asibiti bai sake shiga gidan Aisha ba, wayar ma yanzu ba sosai sukeyi ba.

Ga shi idan yayiwo cefane a gidan Zahra zai ajiye ya raba sannan yace Balele ya kwashi na Aisha ya kai mata; don haka a nan Zahra zata samu ta zare duk abinda take ganin bata so a kaiwa Aishan. Ta kwashe kaji da kifi wani lokacin harda kayan shayi duk kwashewa takeyi, don haka duk wata sai Aisha tayi ciko a cefanenta. Ta riga ta san me yake faruwa don haka abun baya wani damunta.
…………

Tunda aka siyo motar nan kuwa Zahra ta sami kafar yawo, gashi yanzu baya iya yi mata fada. Wasu abubuwan suna damunsa amma sai ya rasa yanda zai yi da ita.

Ya raina hankalin Sadik don haka ma ya hana a bashi mota, amma yana ji yana gani Zahra ta barshi yana hawa motarta. Gashi bazai sami admission ba sai shekara ta zagayo idan ya gyara jarrabawarsa.

Haka dai ya zubawa gidan ido ita da yaranta suna yin yanda suka ga dama.
………..

Tunda suka bar gidan Aisha Hajiya da Anti Uwani suka kasa nutsuwa, ta san Allah ne yake bada haihuwa amma tana ganin gara a nemi taimako a kan yawan barin nan. Don haka suna komawa gida ta sa Anti Uwani ta kai abun sadaka makarantar allo ayi mata addu’a.
Bayan ta yiwa malamin bayani kuma yace ta sami ruwan zamzam ta dinga tofa fatiha kafa bakwai tana sha kullum safe da yamma, ko menene zai warware da izinin Allah.

Don haka yanzu bata rabuwa da ruwan zamzam kullum cikin tofi take tana sha. Ga sallar dare da adduointa da bata fasa ba.
Sai dai duk yanda ta so abun kar ya dameta ta kasa jurewa. Ta rame ta dan yi duhu, idan dai mutum ya santa ya san tana cikin damuwa. Da tana tsammanin ramar da takeyi ciki ne amma yanzu da babu cikin ta gane lallai tana cikin damuwa.
Duk da motsin Amira a gidan yana debe mata kewa amma dai gaskiya yanzu abun ya fara damunta sosai, tana kewar mijinta kuma zaman a haka yana damunta.

Ta sami islamiyya a kusa da unguwar tasu ta shiga duk don ta debewa kanta kewa amma dai ita kanta ta san lallabawa takeyi.

Lokuta da dama idan ta kwanta da daddare sai dai tayi ta juyi a gadon, idan kuma abun ya ciyota sai ta kwana tana kuka.

Tun tana lissafi yanzu har ta bata a lissafi, ta san dai an fi wata hudu.
__

Tunda aka fara lissafi azumi saura sati biyu tayiwa Abba tunin Umrarta, a take ya sanar da ita cewa duk wasu shirye-shirye ma ya gama su tunda tace a goman karshe take so.

Saura kwana biyu azumi yana zaune a falonsa yana karatun jarida ta shigo falon, ta mika masa takardar da take hannunta tace

‘Ga shopping list din azumin na rubuta yallabai.’

Ya karba ya dan duba, ya mayar ya ajiye a kusa da shi yace

‘Gobe za a kawo in Sha Allahu.’

Dama ita yake jira don itama Aisha tun jiya yayi mata waya ta turo masa kuma ta turo.

Jimawa kadan ta dubeshi tace

‘Yallabi ka shirya mana mu tafi Umra tare, ai zai fi dadi ko?’

Ya ajiye jaridar ya gyara zama sannan yace

‘A’a ai na gaya miki ni bazani Umra ba, Hajji nake son komawa kuma akwai wani business da nake son yi a Dubai don haka sai na hada kudin gaba daya da na aikin Hajji da kuma na business din in ya so ko shekara mai zuwa ko ta sama idan na gama aikin Hajji sai na wuce Dubai din.’

‘To bari naje na dage da addu’a wata kila da ni za a je Dubai din. Amma dai ka san gaskiya Umrar azumi akwai sa nutsuwa ko? Wallahi shi yasa na so mu tafi tare.’

Duk yanda ta so ya shirya su tafi Umrar nan tare yaki domin ya tabbatar mata shi Hajj zai je kuma ba zai yiwu da shi da ita su tafi su bar yara ba, don haka dai ta hakura.

Fargabarta daya kada ta tafi kafin ta dawo ya koma wajen matarsa; duk da cewa ko a daren jiya saida sukayi magana ta Whatsapp da yaron Malam ya tabbatar mata ko shekara nawa zatayi bata dawo ba ba zai iya kusantar Aisha ba, ya ma tabbatar mata ba Aisha ba ko wata mace ce ma babu abinda zai shiga tsakaninsa da ita.

Don haka ba tare da damuwa ba ta cigaba da shirinta na tafiya Umra.
………….

Ana i gobe azumi ya yiwo duk wata sayayya, kowacce list din da ta bayar shi yayi amfani da shi ya siyo mata. A nan kan barandar gidan Zahra ya sauke kayan ya kirawo Balele ya ware na Aisha yace ya kai mata yanzu shi kuma ya shige gida.

Yana shigewa Zahra ta dakatar da Balele ta caje ledodin kusan duk wani abu da yake kwalba ko roba saida ta kwashe shi irinsu mayonnaise da salad cream, butter. Ta dauke kayan shayi ma sannan ta kwashe kwai da kaji. A karshe idomie kawai ta bari rabin carton da macaroni da semovita sai sabulun wanka da Omo aka kaiwa Aishan.
Haka ta karba tana mamaki; to ya san wannan zai siyo menene zai sa yace ta rubuto list. Haka ta adana kayan ta dauki Amira suka je suka karasa nasu shopping din na kayan bukata saboda azumi.
-------

Tun saura kwana uku jurgin su Zahra ya tashi Rahma; ‘yar uwarta wadda ta zauna mata da ta haifi Sumayya ta dawo gidan, domin itace zata kula mata da yara da gidan kafin ta dawo.

Sallah saura kwana goma sha uku jirginsu ya tashi sai kasa mai tsarki.
-------

Ranar da Mommy ta tafi da yamma ana dab da shan ruwa Rukayya ta sami Abban a falo, yana kwance a kan doguwar kujera ta shiga da sallama. Bayan ya amsa sallamarta ta karasa ta zauna a gabansa, yace

‘Ya akayi ne Rukayya? Ko har an fara missing Mommy ne?’

Tace

‘A’a Abba, abinda ma sati biyu kawai zatayi.’

‘Hakane.’

Sukayi shiru na dan lokaci, jim kadan Rukayya tace

‘Abba naje gidan Anti Aisha na dinga tayata kwana kafin Mommy ta dawo?’

Da fara’a ya sa mata

‘Eh, ki je Rukayya.’

Zumbur ta daka tsalle ta mike, kafin yace wani abu tayi kasa da gudu.
Chapter 42 · 0% Book details