← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 100

Sashe 3

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

‘Wannan babu wata damuwa, ni dinma ba sauri nake ba. Tunda dai kin san da zamana babu wata damuwa Allah ya sa dai ni din ne mai rabo, kuma Allah ya ji kan babansu Abdul din.’

Ta ji mamaki da ya san sunan yaranta ko da yake ta san dan sa ido ne na gaske.

‘Amin.’

Ta amsa a gajarce. Ta mike tsaye ta koma ta tsaya a bayan kujerar da ta tashi tana wasa da kujerar tana fadin

‘Bari na shiga gida don dama kokarin dora abinci nake aka kirawoni.’

Shima ya mike.

‘Allah sarki, to ai babu damuwa. Akwai ‘yar tsaraba da na zowa da su Abdul ita a mota bari na dauko sai ki shigar musu da ita.’

Kafin ta bashi amsa ya juya ya nufi gate. Tana nan tsaye ya shigo da leda a hannunsa ya mika mata.

‘Yar alewa ce ta yara, kya shafa min kansu tunda naga kamar kina sauri balle nace ki kirawosu mu gaisa.’

Ta karba tana murmushi

‘Ai da yake ma basa nan, suna gidan kanwata amma in sha Allah da sun dawo zan basu. An gode Allah ya saka da alkhairi.’

Sukayi sallama ya fice ita kuma ta nufi cikin gida tana mamaki da takaici a lokaci guda. Gaba daya ma dariya abun yake bata; duk da dai principal mutumin kirkine amma gaskiya ko zata yi aure ba zata aureshi ba balle ma da yake gaba daya auren ma yanzu baya gabanta. Bayan Mustafa ba taga wani namiji a duniya da zata iya sallamawa zuciyarta da jikinta gaba daya ba, ba zata iya ba gara tayi zamanta ta kula da yaranta.

Tana shiga gidan ta wuce daki ta sami Hajiya a zaune a gefen gado, ta karasa ta zauna tare da ajiye ledar a gabanta tana dariya.
Hajiya ta dubeta tana murmushi

‘Ikon Allah! Har kun daidaita kenan da bazawarin kenan?’

Ta kara tsananta dariyarta tana fadin

‘Hajiya, wai bazawari!’

Ta bita da harara

‘Bana son shakiyanci fa.’

‘Hajiya principal dinmu ne fa na makarantar da nake koyarwa, wai ni zai zo yace yana so.’

Hajiya ta dan bata rai

‘Ikon Allah! To bai kai ba kenan ko me?’

‘A’a Hajiya, nifa ban ce komai ba. Kawai dai ba zan aureshi ba kuma na gaya masa don bana son ma na bata masa lokaci. Makarantar tasa ma na san zuwa sati mai zuwa transfer dina zata fito don tun da na koma na nema a dawo dani nan Sabontiti don tafi kusa. Yaje dai yaji da ‘yar matarsa nima naji da kaina.’

Ta karasa tana dariya.

Hajiya tace

‘Amma dai kin san ba zamu zuba miki ido haka babu aure ba ko? Idan ma so kike kice ba zaki sake aure ba to ki bari, ba ki kai shekarun da za a zuba miki ido babu aure ba sai dai idan Allah bai fito da mijin ba.’

Ta sunkuyar da kai tana wasa da ledar da ta shigo da ita. Hajiya ta gyara zama ta dafa hannunta

‘Hakuri zakiyi kinji Aisha, ki fawwalawa Allah lamarinki shi ya hadaki da Mustafa kuma shi zai hadaki da wanda ya fi shi cikin bayinsa nagari. Ki cire komai daga ranki ki sawa ranki idan Allah ya kawo miji zakiyi aure kin ji ko?’

‘Um.’

‘Yauwa. Allah ya kara miki hakuri.’

Ta amsa sannan ta yiwa Hajiya bayanin alewar ta tashi ta fice ta nufi dakinta.
Tana shiga ta turo kofar ta fada kan gado, hawayen da ta tare ya kwace; ba zata iya auren wani mutum ba bayan Mustafa, ita din tashi ce shi kadai in sha Allah. Duk ma rigimar da za ayi sai dai ayi amma babu wanda zata aura a duniya, sai dai su gaji su barta.
……..

Tunda aka canza mata makaranta ta toshe duk wata hanyar da ta san principal zai sameta, haka ya gaji da zuwa gidansu bata fita ya hakura.

Ta kula da yanda Hajiya take matukar so tayi aure, don haka duk wani wanda ya nuna yana so ta da wuri take dakatar da shi kafin ma Hajiya ta ji zancen. A haka har aka shekara uku da rasuwar Mustafa, lokacin Abdallah yana da shekaru bakwai Farha tana da shekaru biyar.
UWAR SADDIKU

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

3

Ranar asabar ce yau, don haka gidan Yaya Zainab suka wuni ita da su Abdallah, sai da sukayi sallar la’asar suka fito suka kamo hanya. Suna karyo kwanar gida ta hango motar Yaya Abubakar, ta san yana gidan.

A dakin Hajiya suka sameshi yana zaune a kan dadduma Hajiya tana zaune a gefen gado suna hira. Bayan sun gaisheshi su Abdallah suka fito falo da gudu suka barsu, itama Aisha ta mike zata fita ta koma dakinta, Hajiya ta dakatar da ita

‘Dawo ki zauna ai maganarkice dama ta kawo Yayan naki, duk da na san babu wata matsala.’

Ta koma ta zauna a gefen gado kusa da Hajiya cikin sanyin jiki don ko ba a gaya mata ba ta san ba zai wuce maganar aure wadda kwana biyu da taga babu wanda yayi zancen ta zata an hakura.

Yaya Abubakar yayi gyaran murya yace

‘Ai kin san Musbahu abokina ko?’

Ta daga kai alamar ‘e’.

‘Yauwa to shine yayi min magana a kan yana so ya zo neman aurenki, idan kin amince.’

Hajiya tace

‘Ai ba za a sami matsala ba ma, mutumin da ba bako bane a gidan nan.’

Ta sunkuyar da kai don bata san me zata ce musu ba, kamar ma dai sun gama yin na’am da maganar Musbahun.

Yaya Abubakar yace

‘Baki ce komai ba.’

Ta danne damuwar da take ciki tayi murmushi tace

‘To Yaya sai ya zo din, Allah ya tabbatar mana da alkhairi.’

‘Amin ya Allah. Ai in sha Allah ba zaku sami matsala ba.’

Ta fice daga dakin ta barsu suna tattaunawa.

Tana shiga daki ta jefa jakarta da hijabinta kan gado, ta dora hannu a ka; so take ta rusa ihu amma ta san dole sai an jiyo ta. Ta karasa gaban mudubi ta tsaya tana kallon fuskarta tana fitar da kwalla; kamar dai kowa ya manta da Mustafa ita kadai ce bata manta da shi ba. Tana aikinta tana kula da kanta kuma yara iyayensu suna yi musu komai amma an dameta da wani aure.

‘Musbahu.’

Ta fada a fili tana jijjiga kai, ta juyo daga mudubin ta zauna a gefen gado ta dafe goshinta da hannuta.

Ya za ayi ta auri wani Musbahu, ta san shi sosai tunda abokin Yayan ne tun suna yara kuma dama can ita Allah bai hada jininta da shi ba tana dai girmamashi saboda abokin Yaya ne. Ta san matarsa daya da ‘yayansa, kuma ta san shi din dan kasuwa ne don haka take ganin idan ta aureshi zata rasa damammaki da yawa kamar aiki da takeyi da sauransu.

Ta share kwallar ta mike ta shige bandaki.

Haka ta karasa wunin nan a daki ita kadai, Hajiya tana kula da yanda yanayinta ya canza saboda anyi maganar aure amma tayi burus da ita, don babu yanda za ayi a kyaleta babu aure.
……..

Suna zaune a falo bayan sallar isha’i ta jiyo karar wayarta daga daki, kafin ta motsa Farha ta zura da gudu ta dauko wayar. Bakuwar lambar ce don haka babu suna, tayi sauri ta amsa kiran ta kara wayar a kunnenta kafin ta tsinke.

Tunda yayi sallama ta gane muryarsa, ta mike ta koma dakinta. Kafin yace wani abu saida ya gabatar mata da kansa

‘Sunana Musbahu Ahmad Tudunwada.’

Ta dan yi yake ta juya kwayar idonta tace

‘Hm, ai na gane.’

Suka gaisa suka dan taba hira yana tambayarta yaranta. Daga baya ya sanar da ita gobe zai zo bayan sallar isha’i, sukayi sallama suka ajiye wayar.

Ta janyo kujerar gaban mudubi ta zauna tare da ajiya wayar a kan mudubin, ta zuba tagumi; gaskiya bata son mutumin nan, ba zata iya aurensa ba don kwata-kwata baya cikin irin mazan da take jin zata iya rayuwa da su. Gashi taga Yaya da Hajiya duk sunyi na’am da shi, ta san yanzu tana yin magana Hajiya zata ce bata son aure.

Ta daga hannu tana addu’a

‘Allah ka kawo min mafita.’

Ana yin sallar isha’i kuwa sai ga Musbahu, ba yaro ya turo ba da kansa ya shiga bayan ya buga kofa an bude. Har falo ya shiga ya gaida Hajiya, tayi ta sa masa albarka tana fatan Allah ya tabbatar da alkhairi. Bayan sun gama gaisawa ya koma gareji don jiran Aisha wadda Hajiya tace masa yanzu za a turo ta.

Yana ficewa itama ta fito daga daki ta kama hanyar fita daga falon, sauri takeyi don kada Hajiya tace wani abu don a halin yanzu haushin yanda Hajiyan ta dinga wage masa baki take tana faman sa albarka kamar wadda yayiwa alfarma. Tana daf da isa bakin kofa Hajiya tace
‘Haba Aisha, ai ko ruwa kya dauka ki bawa bakon naki ko, tunda dai bakonka annabinka.’

Ba tare da ta juyo ba ta bata amsa

‘Hajiya zan dawo na dauka.’

Ta fice da sauri kafin Hajiyan tace wani abu.

Haka ta daure zuciyarta suka dan taba hira babu yabo babu fallasa, sai dai zuciyar Aisha a cunkushe take bata jin zata iya bashi waje a cikinta. Haka dai har ya gaji da surutu yayi mata sallama ya tafi.

Daga wannan lokacin ya zama duk juma’a sai Musbahu ya zo, duk da ya fuskanci bata saki jiki dashi ba sai dai yana ganin kamar idan ya bata lokaci zata dawo ta saki jiki.

Yanda Hajiya take kara sakankancewa da maganar Musbahu yasa ta kasa gaya mata bata sonshi. Tayi kokarin gayawa Yaya Abubakar shima ta ga kamar ba zai fahimceta ba, don haka ta hakura. Ta dai yiwa kanta alkawarin babu yanda za ayi ta aureshi.
___

Tunda mahaifinsu Aisha ya rasu duk ranar Juma’a sai Baffa Aminu ya zo gidan, shi ya zama kamar ubansu. Yau din ma ana saukowa daga masallaci ya wuto gidan danuwansa. Nan ya zauna a falon Hajiya, Aisha ta kawo masa abinci ya sa su Abdallah a gaba suka ci tare. Sai da aka kusa la’asar ya fara shirin tafiya. Ya dubi Hajiya wadda take zaune a kujerar zaman mutum uku yace
Chapter 3 · 0% Book details