← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 100

Sashe 51

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

‘To ai da wayar Saddikun aka kirawo ni kinga ko ma wane yana tare da Saddikun kenan, gara kawai naje dare yana kara yi.’
‘To Amma ka kirawo Mommy ka tambayeta ta duba maka dakin Saddikun ta tabbatar, ka ga idan yana nan zai iya yiwuwa sace wayar aka yi. Tunda ka ga ka hanashi yawon dare kuma yanzu fa duba ka gani wajen sha biyu saura, yaushe ya taba kaiwa haka a waje?’

Ya dan yi tunani kadan, ya koma ya zauna a bayan kujera ya zaro wayarsa daga aljihu yana fadin

‘Bari na kirawota na tabbatar din kam.’

Ya lalubo lambar Zahra ya danna mata kira, cikin yanayi na bacci ta amsa wayar

‘Yallabai.’

‘Zahra. Ina Saddiku? Ya dawo gidan kuwa?’

Ta dan dauke wayar daga kunnenta ta duba lokaci sannan ta bashi amsa

‘Ya dawo mana, yana dakinsa yana bacci fa.’

‘To don Allah ki je ki duba kiyi min confirming zan kira ki nan da minti biyar.’

Ya ajiye wayar ya zauna yana jiranta.

Ita kuma tana ajiye wayar tana mamaki; har zuwa lokacin da ta kwanta wajen sha daya dai ta san Saddiku bai dawo ba amma tayi masa waya yace mata yana hanya. To wani munafukin ne kenan ya gaya masa bai dawo ba zai tashe ta daga bacci da wannan tsohon daren. Ta saka hijabinta ta sauko ta fito daga cikin gidan, tana fitowa farfajiyar gidan taga babu motarta don haka ta tabbar bai dawo ba. Ta haska fitila ta kirawo Malam Sado, nan da nan ya karaso inda take.
Tace

‘Malam Sado Saddiku bai dawo ba?’

Cikin girmamawa ya bata amsa

‘Bai dawo ba Hajiya ai yana tafe dai ko da wanne lokaci zaki iya ganinsa.’

‘Don Allah da ya shigo kace nace ya kirawo ni a waya, bana son na kirawoshi yanzu ya dauka yana tuki ga dare.’

Ta sallameshi ta koma ciki ta rufe gidan.

Tana shiga falon wayar Abba ta shigo, tana dauka yace

‘Ina Sadikun?’

‘Yana dakinsa, bacci ma yake don ta taga na leka ban zagaya ba saboda dare.’

Ya ajiye wayar ya dubi Aisha dake tsaye a gabansa

‘Kin ji kuma wai yana gidan.’

‘To ai shi nake gaya maka, kada kaje trap ne kai ake nema ba Saddiku ba.’

Ya dan yi shiru yana tunani, jimawa kadan yace

‘Bari dai naje gidan na gani, ko babu komai na ji wanda ya bawa wayar tasa.’

Ta sake shan gabansa ta langabe, ya dafa kafadarta yace

‘Gara naje na gani don zai iya yiwuwa boye min takeyi don kada nayi masa fada da safe. Idan na sameshi a gidan yanzu zan dawo, ko ma menene zan kirawo ki a waya in Sha Allah.’

Ya fice tana yi masa a dawo lafiya.
……..

Yana taba gate din gidan Malam Sado ya taso yana haskawa, yana gane wanda yake bude gate din ya ja baya ya kwashi gaisuwa. Ya karewa tsakar gidan kallo a takaice, motar Zahra bata wajen da aka saba ajiyeta. Yace

‘Sado ina motar matar gidan?’

Ya sosa keya sanna cikin in ina yace

‘Yallabai Sadiku ya fita da ita ai tun kafin magriba, sai dai ma yau yayi dare sosai amma na san yana tafe da izinin Allah.’

Ko sauraronsa bai yi ba ya nufi kofar shiga gidan a fusace, iya karfinsa ya buga kofar saida ya buga sannan ya tuna akwai mukullin kofar a hannunsa. Ya saka mukullin ya bude kofar ya shiga, kai tsaye ya haye saman.

Tana zaune a kan gado tana muttsike ido tana shirin saukowa don ta zata Saddiku ne ya dawo. Ta ja tsaki ta mika hannu ta janyo hijabinta a daidai lokacin da ya bude kofar ya shiga dakin.

Ta san fada zaiyi a kan fitar Sadiku don haka ta kara tsuke fuska tayi shirin kora masa jawabi.

Cikin dacin rai yace

‘Zahra, kika ce min Saddiku yana nan yanzu kuma naga baya nan, ina ya tafi? Don me zakiyi min karya?’

Ta mike tsaye ta fuskanceshi

‘Karya kuma? Wai kai don Allah me ya sa kake….’

Ba zai iya sauraronta ba don haka ya katseta da murya mai cike da damuwa

‘Zahra garin ki cutar da ni kina cutar da kanki, kin bashi mota duk da na hanaki baki ji ba, na saka masa doka kina taimaka masa yana karyawa. Waya aka bugo min da wayarsa cewa yana asibiti yayi hatsari a motar, yana can rai a hannun Allah. Nayi tunanin ya kamata a ce yana gida shi yasa na zata ko wani wasa ne ko karya don na san ya kamata ace yanzu yana gida, ashe baya nan. Allah ya sauwake, kin cutar da kanki kin cutar da mu baki daya.’
Tuni ta daskare jiri ya fara dibanta, kwakwalwarta ta daskare don tun bayan rasuwar mahaifiyarsu bata kara shiga tashin hankali irin wanda ta shiga yanzu ba da yake gaya mata Sadiku yayi hatsari. Ya juya zai fice daga dakin, cikin zafin nama ta dafa kafadarsa tana fadin

‘Sadiku fa kace min, la ilaha illallah! To yanzu yana ina? bari na taho muje.’

Hannu ya saka ya tureta daga jikinsa ta koma kamar zata fada kan gadon, ya fice ba tare da ya sake kallonta ba.

UWAR SADDIKU

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

28

Nan ta zube tana fitar da hawaye masu zafi; Sadiku yayi accident? A wannan daren? Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun.

Ta dafe kirjinta wanda yake kara kuntata zuciyarta ta ja jiki daga inda ta zube ta koma kan gadon. Ta kifa kanta a kan filo ta fashe da kuka.

Bata san tsawon lokacin da ta dauka a haka ba amma lokacin da ta daga ta duba agogon wayarta karfe uku na dare saura kwata. Nan da nan ta dauki waya ta bugawa Abban don bai gaya mata koda asibitin da aka kai Saddikun ba. Ta kirawo shi ya kai sau goma amma bai dauka ba, don haka hankalinta ya kara tashi.

Bata yi niyyar saukowa ta shirya yara su tafi makaranta ba amma sai ta tuna idan basu tafi makarantar ba damunta zasuyi tayi; musamman da yake Rahma ta tafi, don haka ta sauko bayan ta idar da sallar asuba ta fara shirinsu.

Har karfe goma na safe bai dauki wayarta ba, so take kawai ya gaya mata inda Sadik din yake amma ya ki daga wayar. Haka ta hakura ta zauna tana ta abu kamar zautacciya.
--------

Yana fita ya kirawo Aisha ya sanar da ita halin da ake ciki, ya wuce asibitin.

A emergency ya samesu; kusan a sume Saddikun yake duk da dai likitocin sun sanar da shi allura akayi masa ta sashi barchi. Ya sami karaya a hannun hagu, sannan kuma ya yanke a cinyarsa wanda sun riga sun yi masa dressing sannan kuma akwai sauran ciwuka kanana a waje daban-daban a jikinsa. A take likitan ya bawa Abban shawara a mayar da shi asibitin kashi saboda a duba hannunsa sosai.

An nuna masa Munir sai dai Abban bai san yaron ba, kuma ba a sami lambar iyayen yaron ba don tun a wajen da akayi accident din aka sami wani ya dauke wayar tasa. Bai sami wani babban ciwo ba sai kurjewa nan da can sannan kuma da firgita da yayi, don haka aka yi masa allura yake ta barci bayan an wanke masa ciwukan.

Kafin asuba an gama duk wasu shirye-shirye aka saka Saddiku a ambulance Abba ya bi su a baya bayan ya sami wanda zai tsaya masa a kan Munir. Suna zuwa aka kwantar da shi; wajen karfe takwas da rabi likitocin suka shigo.

Nan da nan aka duba Saddiku aka yi masa hotuna, aka tabbatarwa Abban karayar hannunce kawai matsala. Kafin a gama hotunan nan ya faraka, babu abinda yakeyi sai kuka da kiran Mommy. Don kamar ma baya gane mutanen da suke kansa balle ya gane Abban.

Nan da nan aka sake yi masa allura ya koma bacci, aka gyara shi aka kwantar da shi. Lokacin wajen karfe tara da rabi.

A take Abban ya dauki waya ya kirawo Rahama ya sanar da ita halin da ake ciki ya roki alfarma tazo ta zauna da Saddiku a asibiti; ta jajanta masa hatsarin sannan ta fara shiri. Tana shiryawa tana mita don tayi alkawarin ba zata sake zuwa gidan ta zauna da yara ba ko yanzun ma da Zahra ce ta kirawota ba zata je ba.
Amma tana jin nauyin Abba, ba zata iya ki ba. Tayiwa Ummansu sallama ta nufi asibitin.

Rahama tana fita Ummanta ta fara waya tana gayawa dangi Saddiku yayi accident; bayan ta kirawo su Murja ta kirawo Zahra ta jajanta mata. Sai a lokacin ta sanar da ita ai Rahama ta tafi asibitin kashi wajen Saddiku.

Taji haushin Abban da yaki daga wayarta har ya gayawa danginta inda Saddikun yake amma ita bai sanar da ita ba. Su Yaya Murja duk sun mata waya a kan kafin azahar zasu sameta a asibitin. Nan da nan ta tashi ta soya kwai da dankali ta zuba ruwan zafi a flask sannan ta shiga wanka.
Saida ta gama shiryawa ta kirawo Abban taci sa’a ya dauka, kafin ta gaisheshi tace

‘Ya Saddikun? Sai kiranka nake baka dauka ba, don Allah kuna ina?’

‘Mtsewww. Ki zo nan asibitin Murtala, akwai yaron da sukayi accident din tare da Saddikun ko zaki gane shi don ni ban sanshi ba . Har yanzu bamu sami iyayensa ba, ki zo ki gani ko kin san iyayensa in ya so daga nan kya wuce asibitin kashi.’

‘Ina jin Munir ne yaron kuma wallahi nima ban san iyayenshi ba, sai dai ko idan ya farfado a tambayeshi.’
Sukayi sallama ta ajiye wayar, ta karasa shiryawa ta shiga mota Malam Ali ya ja suka wuce asibitin kashi.

Haka Abban Sadiku ya zauna a asibitin Murtala wajen Munir har saida Munir din ya farfado, aka samu aka tambayeshi. Nan ya bayar da lambar babansa aka kirawoshi, ba a gari yake ba don haka kaninsa ya turo. Kafin ya iso Abba ya gama biyan duk wani abu da ake bukata an canzawa Munir daki, an sayo magungunan da yake bukata; duk da ma likitan yace zasu iya sallamarsa zuwa gobe.
………..
Chapter 51 · 0% Book details