← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 100

Sashe 54

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranar haka Aisha ta kwana cikin tsananin murna; babban abinda yake kara sakata farin ciki shine zata je ta yiwa Abbanta da Mustafa addu’a. Sannan kuma zata kara rokawa kanta tsari domin ta kula idan dai zata cigaba da zama da Uwar Saddiku to tabbas tana bukatar tsari daga Allah.
………

Washegari suna zaune a falo suna cin abincin safe suna ‘yan hirarrakinsu ya dubeta yace

‘Idan muka gama aikin Hajji sai na sako ki a jirgi ki dawo gida, ni kuma na wuce Dubai. Akwai Abdurrahman zamu hadu da shi a can sai mu sayo kayan nan da nake gaya miki.’

‘Ma sha Allah, Allah ya nuna mana.’

Suka dan cigaba da cin abincinsu.

Jimawa kadan ta kurbi shayinta tayi gyaran murya tace

‘Alhaji.’

Ya kalleta da mamaki saboda ba haka ta saba kiransa ba, tayi murmushi tace

‘To ka tafi dani Dubai din mana, ai ko jaka ma na rike maka ko?’

Ya ajiye cokalin da yake hannunsa yana kallonta yana murmushi, ta cigaba

‘Kuma ma ya za ayi ace kamar kai ka tafi Dubai ba tare da ni ba, haba mana. Ai ko jaka ma sai na rike maka kuma in ka gaji ma ko tausa ai nayi maka.’

Ya jijjiga kai yana murmushi yace

‘Small girl. Wai ni zaki tsara ko?’

Ta dauko kwanon dankali ta ta dawo kujerar kusa da shi tana zumbura baki

‘To ba sai ka tsaru ba. Don Allah mu tafi tare kawai, ya za ayi ka tafi Dubai kai kadai wai sai kace baka da gata.’

Ta karasa tana kwantar da kanta a kafadarsa.
Ya shafa kumatunta yace

‘Nima ina son naje da ke amma dai ba yanzu ba, yanzu gaba daya kudin zan tattare nayi sayayya. Idan abun ya kankama wata rana zamu je dake.’

Ta langabe kai

‘Bari dai nayi Sallah nayi addu’a, watakila ka taka kulli kafin lokacin sai kaga mun tafi tare.’

Shima yana son tafiya da ita don ya san zai huta sosai, to amma tashin hankalin da Zahra zata yi masa kadai ya isheshi sannan kuma kamar yanda ya fada kudaden hannunsa bazasu kai ya tafi da Aisha ya kashe mata kudi yanda yake so ba; kwata-kwata ma kwana biyu yake son yi a Dubai din ya wuto Nigeria.

Haka suka karasa cin abinsu suka tashi.

Ita kuwa Aisha tana nan ta dana tarko don gaskiya tana son zuwa Dubai don haka ba zata bari damar nan ta wuce ta ba.
__

A zaune yake a falon yana hutawa da yake ranar Lahadi ce, tana zaune a gefensa yayinda Sumayya take wasanninta a gefe guda.

Ta dan yi gyaran murya tace

‘Um dama ina so na gaya maka, mijin yayar Amina ya rasu zamu je mata gaisuwa a gidanta da yake garin Doguwa.’

Da mamaki ya kalleta

‘Kin san nisan kauyen nan kuwa? To ke da wa zaku je?’
‘Ni da Aminan ne, a motar ta ma driver dinta zai kaimu.’

‘Ohk. To babu damuwa amma dai da kin bari sai next weekend, dama ina son gaya miki nextweek zan tafi aikin Hajji tare da kanwarki.’

Bata san yana shirin tafiya Hajjin ba don haka ta dan yi mamaki. Ta gatsina baki ta dan yi murmushi

‘Kuma da gaggawa haka? Allah ya kai ku lafiya Allah ya amsa ibada. Kace mu kadai zamuyi Sallah a gidan kenan.’

‘Eh daga ke sai yara ba, amma da an sallace zata dawo ni kuma na wuce Dubai na gaya miki zan je Dubai.’

‘Ok, tafiyar ta zo kenan? To Allah ya sa a je a sa’a.’

‘Amin ya Allah. Kinga idan muka tafi sai ki sami damar zuwa gaisuwar ko? Amma fa sai kin dinga hakura da fita tunda kin ga Saddiku bai gama warkewa ba.’

‘Eh kusan daga wannan din ma babu wata fita da zan sakeyi in Sha Allah sai dai ko gaisuwar Sallah in Sha Allah.’

Suka karasa hirarrakinsu.

Bata ji dadin yanda bai sanar da ita shirinsa ba, saboda ya za ayi tana nan yana shirin tafiya Saudiyya amma ba zai sanar da ita ba.

Ta dai kyale zancen ne saboda tana da nata shirin, kuma da bata ji yace zai wuce da Aishan Dubai ba bata da damuwa.

Ita din ma zata so ace baya gari zasuyi wannan tafiyar ita da Amina tunda zai zama babu wani sauri da takeyi ta dawo gida sai lokacin da ta ga dama kawai. Don haka a take ta yiwa Amina waya suka daga ranar tafiya, domin a lokacin dama Asiya bata dade da haihuwa ba.
__

Ranar asabar ce wadda gobe Lahadi jirgin Abban Sadik da Aisha zai tashi.

Duk wani shiri da take bukata ta gama shi; abu dayane a ranta yanda zata tsara Abban Sadik ya yarda ta biyawa kanta kudin zuwa Dubai ta bishi. Tunda yayi maganar ta sa aka bincika mata aka gama yi mata lisaffi; kudin jirgi, hotel har zuwa kudin da take so ta kashe ta lissafa kuma taga cewa tana da su zata iya biyawa kanta.

Jirgin safe zasu tafi don haka zuwa goman dare sun gama komai sun kwanta. Yana kwance rigingine tana kwance a gefensa sai dai basu kashe fitila ba tukunna don basuyi bacci ba.

Mirginawa tayi ta koma jikinsa, ta dora kanta a kan hannunsa sannan ta dora tafin hannunta a tsakiyar kirjinsa, tace

‘Yallabai za a wuce da ni Dubai din?’

Ya dan dago kansa ya kalli fuskarta

‘A’a. Ai na gaya miki babu kudi amma kada ki damu kiyi ta addu’a business din ya kankama zamu je Dubai in Sha Allah.’

Sukayi shiru na dan lokaci, jimawa kadan ta muskuta tace

‘Don Allah to ni zan biyawa kaina, kaga dama adashin da nace maka na dauka last month 250k suna nan kuma inada wasu savings sai na kara.’

‘Um, kiyi abinda kika tsara zakiyi da kudinki in Sha Allah next time sai muje Dubai din.’

‘To kayi tunani dai kafin muje, kudin suna dollar account dina Kuma kaga visa din Dubai bata wahala. Kafin mu gama aikin Hajji kayi shawara. Kaga kafin ma mu dawo gida mun huta, ko kwana biyun ne ina laifi.’

‘Saboda muje kiyi min addu’a, ki tsara ni kiyi min wayo ko?’

Ta kyalkyale da dariya.

Suka karasa hirarrakinsu suka yi bacci.

Gari yana wayewa karfe tara na safe jirginsu ya daga sai Saudiyya.
___

Ranar litinin karfe shida na safe Uwar Sadiku suka kama hanyar garin Doguwa; a motar Amina suka tafi sai dai akwai Alele yaronta shine yake tukasu.

Nisan garin ya bawa Zahra mamaki matuka, don gani tayi kamar za a fita daga garin Kano.
Ko da suka Isa Doguwa ma wucewa sukayi sai da suka kusa fita Kano sannan suka sauka daga kwalta suka fada wani daji, da ba don taga alamar motoci suna bi ba da zata ce babu wanda yake shiga wajen.

Hanyar tsakiyar daji take, babu koda gona a kusa.

Ta kalli Amina wadda suke zaune a bayan mota tare zuciyarta fal tsoro, Amina tayi murmushi tace

‘Kada ki damu, kina hawowa nan layin kin zama bakuwar Malam Jani, babu abinda zai cutar dake har ki fito ki kama hanya sosai.’

Ta dan gyara zama ta mayar da hankali ga kallon hanya duk da ba wani gani takeyi sosai ba.

Sun kai kamar minti goma sha biyar suna zura gudu a lokon nan kawai sai taga sun fado wani sarari mai fadin gaske; kamar wata karamar unguwa.
A gaban wani babban gida sukayi parking wanda yake kewaye da wasu gidajen tsilli-tsilli sannan ga yara suna wucewa jefi-jefi. Yanayin wajen yanayi ne mai dadi, babu sanyi kuma babu zafi sannan ko ina a share yake tsaf.

A kofar babban gidan sukayi parking kusa da wasu motoci guda biyu wanda ga dukkan alamu masu kudine sosai kuma suma bakin wannan gidan ne.

Tun kafin su gama fitowa daga mota yaro ya fito daga cikin gidan yayi musu iso. Madadin su shiga ta kofar gidan sai yaron ya zagaya da su ta wata kofar da take bayan gidan.

Daki ne ya sha shimfidu na jajayen daddumai, har labulayen dakin duka jajaye ne. Ya nuna musu wata bakar dadduma yace su zauna, bayan sun zauna yace

‘Za ayi muku iso idan Malama ya gama, yana da wasu bakin.’

Kafin su amsa ya fice daga dakin.

Suna nan zaune tun wajen karfe tara na safe har sha biyu ta gota babu wanda ya sake lekosu, idan suka taba hira sai su koma suyi shiru.

Zahra ta dubi wayarta taga lokaci, ta dago ta dubi Amina tace

‘Amina anya ba a manta damu a gidan nan ba kuwa?’

‘Nace miki yana sane, tunda naga motocin nan na san yana da baki sai ya gama da su zai sauraremu.’

‘To ya ya za ayi muyi Sallah kin ga dai daya tayi.’

Ta dan zaro ido

‘Sallah! Ki rufa mana asiri, ai sai dai idan mukaje gida ma hade. Wa ya gaya miki ana kallon gabas a nan?’

Kallon da Amina take mata ya sa tayi shiru, suka cigaba da jira.

Jimawa kadan wajen daya da rabi yaron da ya rakosu dakin ya leko yace shu shigo. Ya wuce gaba suka bi bayansa. Kofar da suka shigo ba ita suka fito ba, wata kofar ce a dakin ya shiga suka bishi. Siririn corridor suka bi wanda ya sada su da wani daki mai kawanya.

Kusan komai na dakin ja ne sai fari tsilli-tsilli. Bangon da yake kallo kofar an bi shi kaf an rataye tarkace kala-kala, kayuwan dabbobin ita dai Zahra kamar har shekar tsuntsu ta hango.

Jar dadduma ce a shimfide a gaban bangon wadda kallo daya zaka yi mata ka san ta hadiye datti da yawa. Yana zaune ya tankwashe kafafu babu wata sutura a jikinsa sai gajeran wando da bai karasa gwiwarsa ba.

Tun da suka saka kafa a dakin Zahra ta damki hannun Amina ta rike gam saboda tsoro, ita kuwa Aminan da yake ta saba kai tsaye ta wuce gaban wannan bakin katon suka gurfana.

‘Ki gayawa bakuwarki ba a tsoro a nan Hajiya.’

Ya fadawa Amina da kakkausar muryarsa.

Nan da nan Zahra ta dan gyara zama tana kokarin ta dake.

‘Me kike so ayi da kishiyar taki da ta hanaki walwala?’

Sai da Amina ta zungureta sannan ta tuna ita akewa tambayar
Chapter 54 · 0% Book details