← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 100

Sashe 52

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba karamin tashin hankali Mommy ta shiga ba da ta ga Saddiku, musamman da yake lokacin da taje ya farka yana kukan hannunsa yana ciwo. Da kyar nurse ta taimaka mata ya Sha shayi Rabin kofi sannan aka sake yi masa allura ya koma bacci.

Bayan yayi bacci ta barshi da Rahama ta fito daga dakin ta sami waje kan wata baranda ta zauna; ta rasa me yake mata dadi. Matse hawaye kawai take tana ajiyar zuciya.

Tana na zaune tana kirga motocin da suke shigowa wajen ta hango motar Amina, da sauri ta fito daga motar ta karaso wajen Zahran. Tana zama ta fada jikinta ta fashe da kuka, Saida tayi mai isarta sannan ta dago ta kalli Amina tana share kwalla

‘Amina kinga Sadiku kuwa yanda ya zama?’

‘Hmm! Na dai ga motar da ina tahowa Zahra, wallahi wannan motar ma idan aka ce na ciki duka sun mutu ba zan yi mamaki ba. Kuma kamar ita kadai ce motar ba tare da sun bige kowa ba sukayi hatsarin. Gaskiya abun da mamaki.’

Ta mike tana fadin

‘Tashi muje ki gan shi.’

Suka mike suka koma dakin gaba daya.

Suka tsaya a gefen gadon nasa bayan sun gaisa da Rahma, har yanzu bacci yakeyi sai dai kana kallon fuskarsa ka san a cikin wahala yake baccin.

‘Kin ganshi ko Amina, duk jikinsa ciwo ne kuma an ce karaya ce a wannan hannun sai gobe za a yi masa aiki.’

‘Allah ya baka lafiya Saddiku.’

Amina ta fada cike da tausayawa.

Ta jata suka fito suka koma inda suka tashi suka suka zauna, suna zama ta share kwalla tace

‘Kin ganshi ko Amina? Kuma fa Abban yace daya yaron da suke tare a motar shi buguwa kadan yayi, amma dubi Saddiku. Ya za ayi na yarda ba hannu aka sa masa ba, wannan ma ina jin kasheshi aka so yi Allah ya ja kwanansa.’

‘Gaskiya ne kawata, sai ma kin ga motar yanda ta lalace gaba daya zaki san nisan kwana ne ya hanashi mutuwa. Gaskiya wannan abun kam sai kin mike tsaye.’

Sukayi shiru na dan lokaci, jimawa kadan Zahran tace

‘Wallahi ba zan yarda ba, babu wanda nake zargi sai matar ubansu don motar ma ai tunda tana hawa ba zata so na hau ba. Na samo takardun filin nan ma amma bari a kwana biyu mu ga jikin Saddikun sai muje a gama komai; in sha Allahu matsalar kudi ta kare komai tsadar aiki sai inda karfina ya kare.’

‘Gaskiyarki kawata, kin san hatta faduwar Saddiku jarrabawa ma kawai shiru nayi miki amma ina zargin matar nan. Tunda kin ga Saddiku yana da kokarinsa amma ace jarrabawa ta gagareshi.’

Haka suka cigaba da tattaunawa Amina tana kara zuga ta a kan su dauki mataki.

Kafin yamma dangi duk sun zo anata duba Saddiku, don saida likita ya hanasu shiga dakin yace su daina damunsa.
Har dare yayi Zahra tana nan a asibitin, sauran yaran kuma suna gidan ta barsu da Jummai. A yanda ta tsara Rahma ta tafi ta kular mata da gidan ita zata zauna da Saddiku zuwa a yi masa aiki don an ce da safe karfe bakwai za a shiga.

Bayan sallar Isha’i Aisha ta dafa macaroni da sauce din kaza, ta sami flask ta zuba na asibiti. Ta zuba madarar waken suya mai dumi a flask ta hada Abban ya dauketa suka nufi asibitin.

Babu kowa a wajenshi daga Mommy sai Rahma, ya dan sami sauki don idonsa biyu kuma ba kuka yake ba. Da kyar ta bude baki ta amsa gaisuwar Aisha, itama Aishan sai taja jikinta. Ta yiwa Sadikun sannu ta koma kan dadduma kusa da Rahma ta zauna, suka gaisa da Rahman suka dan taba hira.

Basu fi minti goma Sha biyar ba Abban yace ta tashi su tafi, ya dubi Zahra yace
‘Kema ki tashi mu tafi, Rahma ta kwana da shi in ya so da safe kya dawo.’

Aisha ce ta yiwa Rahma sallama ta fice sai Abban ya bi bayanta.

Saida ta jira Abban ya fice ta ja Rahma gefe ta rada mata

‘Kada ki bashi abincin da matar ubanshi ta kawo, akwai ragowar burodi da ruwan zafi a flask din da na zo da shi ki hada masa kawai tunda da kyar yake cin abinci. Wanda ta kawo ki bada shi kawai.’

‘To.’

Sukayi sallama ta fice; Rahma ta bi bayanta da kallo tana jijjiga kai tana mamakin wannan kiyayya da zargi da ake wa Aisha don ita bata ga alamar cutarwa a tare da Aishan ba.
……..

A hankali ta biyo bayansu domin ta shirya tijarar da zatayiwa Abban idan Aisha ta shiga gaban mota; a nan zata nuna musu iyakarsu don babu yarinyar da ta isa ta shigar mata gaban motar miji.

Shida Aishan suka fara isa wajen motar, yana budewa ta shige bayan motar. Bayan ya zauna ya juyo ya dubeta

‘Kika shige baya?’

Tayi ‘yar dariya tace

‘To mai guri ya zo ai dole mai tabarma ya nade ko, naji kace da Mommy zamu tafi kaga kuwa ita ya kamata ta zauna a nan.’

Kafin ya bata amsa Zahra ta karaso, babu haske sosai a wajen don haka bata hango Aisha ba. Cikin isa ta fizgi murfin kofar motar, sai dai ga mamakinta babu kowa a wajen; ta hango Aishan a bayan motar. Ta shiga ta zauna cike da isa tana ta wani cin magani ta rufe kofar motar.

Ba tare da kowa yayi magana ba Abban yaja motar suka nufi gida.
Kwanan Zahra ne don haka Aisha ya fara ajiyewa sannan suka wuce.

Ta tanadi tsiya kala kala da magnaganu masu zafi da zata gaya masa idan har ya kuskura yayi mata maganar bawa Sadiku mota, sai dai ga mamakinta suna shiga gidan ya rufe gidan; bayan yara sun sanar da shi Jummai ta tafi; ya shige dakinsa ya barta da yara suna tamabayarta labarin Saddiku.

Iya haushi ta shaki haushin Abba sai dai ko sauraronta bai yi ba sannan kuma ita kanta damuwar halin da ta baro Saddiku ya isheta. Haka ta kwana cikin matsananciyar damuwa.
-------

Karfe bakwai aka ce za a shiga da Saddiku tiyata don haka tun karfe shida da rabi Abban ya gama shiryawa. Ya riga ya sanarwa Aisha ta hada masa abincin safe da nashi da na ‘yan asibiti don haka ko abinci bai nema ba a shirye ya sauko.

Yara sunata shirin makaranta duka suka gaisheshi. Ya wuce kichin inda ya jiyo motsinta; bayan ta gaishe shi tace

‘Ba zaka ci abinci ba? Kafin ka gama Jummai ta karaso sai mu tafi tare.’

‘Yanzu zan tafi na karya a can, ki jira Malam Ali idan ya kaisu makaranta sai ya dawo ya kaiki, don akwai takardun da sai na saka hannu sannan zasu shiga da shi tiyata. Ni na tafi.’

Bai saurari amsarta ba ya fice.

Ta share kwalla; itama tana so ta ga Sadikun kafin a shiga da shi tiyata shi yasa ma taso tafiya yanzun, tayi kwafa ta cigaba da aikinta.

Ko da Malam Ali yazo daukan yara da kanta ta fito tace masa da ya ajiye yaran a makarantar ya zo ya kaita asibiti. Ya amsa suka fice shi da yara.

Yana ajiye yara a makarantar kiran Abban ya shigo wayarsa, bayan sun gaisa Abban ya tambayeshi inda yake ya sanar dashi. Abban yace

‘Idan ka ajiyesu ka wuce office ka jira ni.’

‘To ranka ya dade Hajiya dai tace idan na saukesu naje na kaita asibiti, idan na kaita asibiti sai na zarto office din kenan Ranka ya dade.’

‘Ali, ni kake wa aiki ko ita?’

A take ya shiga taitayinsa, yace

‘Ah Ranka ya dade!’

‘Daga nan inda kake ka kai min mota office ka zauna ka jirani.’

Ya tsinke wayar ba tare da ya saurari amsarshi ba.

A take shi kuwa ya karkata kan motar ya tafi office. Ya san Mommy tana da lambarsa kuma bai san me zai gaya mata ba idan ta kirawoshi don haka yana shiga office din ya kashe wayarsa tunda ya san idan Abba yana nemansa zai kirawo wani a office din yace a bashi.

Haka tayi ta jiran Ali bai dawo ba, shi kuwa Abba tunda ta kirawoshi ya ki dauka ta sa a ranta ba zata sake kiranshi ba a kan maganar Saddiku.
Sai can wajen sha daya Suwaiba ta kirawota zata tafi asibitin don haka sai tace ta biyo mata su tafi.
………..

An yi aiki kuma komai ya tafi daidai sai dai likitan ya bada umarnin ‘yan dubiya su dan saurara zuwa awa ashirin da hudu kafin nan zugin hannun yayi sauki. Don haka mommy da Abban ne kawai suke zuwa.

Musamman Amina ta dauko mata hoton motar yanda ta kwankwatse kafin daga baya road safety suka janye motar.
--------

Tunda Hajiya ta sami labarin hatsarin hankalinta yake kan ta zo taga Saddiku, sai dai Abba ya hanasu zuwa. Saida ya kwana biyar a asibiti lokacin ciwon yayi masa sauki tunda har ana hira da shi, kuma duk ciwukan jikinsa sun fara nuna alamar warkewa tunda tun a asibitin Murtala aka yi masa dressing dinsu.

Malam Ali ya tura ya dauko Hajiya tare da Yaya Saratu da kuma Innani, Yaya Bello shima duk da kusan kullum sai ya zo haka ya biyosu suka taho.

A nan dakin aka shimfida musu tabarma suka zauna ana ta jajantawa ana ‘yan hirarraki har Abban.

Wajen karfe sha daya sai ga mutanen gidan su Aisha; Hajiya, Anti Uwani da kuma Yaya Zuwaira wanda Yaya Abubakar da kanshi ya kawosu.

Cikin mutunci da girmamawa suka gaisa da su Hajiya, itama Zahra da yake a gaban Hajiya ne da Abba cikin mutunci aka gaisa. Suka jajanta musu sosai suka duba Saddiku. Suka dan taba hira, jimawa kadan suka ajiye musu leda cike da kayan marmari ga kuma wata ledar da kajin gidan gona guda shida gyararru. Yaya Abubakar ya zaro kudi naira dubu goma ya ajiye a gaban Hajiya yace a saya masa abun tabawa. Suka fito ana son barka, Abba ya biyosu yana rike da hannun Yaya Abubakar yana yi musu godiya.

Bayan sun fita Yaya Saratu ta dubi Zahra tace

‘Ikon Allah, albasa batayi halin ruwa ba. Mutanen gidansu masu mutunci da karamci amma kanwar taki kam babu hali.’
Chapter 52 · 0% Book details