← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 100

Sashe 24

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan an kwana biyu kuma ranar asabar tayi tuwon shinkafa da miyar gyada da rana shima ga mamakinsa yanda waccan miyar tayi wannan ma haka tayi.

Dandanon babu dadi ga shi kuma har wani bashi miyar takeyi, dole ta tashi tayi sauri ta kada musu miyar kuka suka ci tuwon.

Sanda ta ajiye abincin dare tana kula da Abban Sadik sai da ya dandana kadan sannan ya saki jiki yaci.

Daga baya kuma suna zaune a falo suna hira da daddare yake tambayarta

‘Wai kuwa kin gane abinda yake bata miki miya, ko kayan kamshi da kike sakawa ne?’

Cikin damuwa tace

‘Wallahi ban gane ba, bana jin kuma kayan kamshin ne amma dai zan cigaba da dubawa.’

‘Ya kamata dai ki kula sosai, idan ma wani abune yake shiga abincin sai ki mayar da hankali ki gyara.’

‘In Sha Allah.’

Ta kula da yanda yake kokarin ya zargi ko tana saka masa wani abun a abinci wanda hakan ya sosa mata rai, sai dai itama ta rasa abinda yake faruwa da miyar tata.

Haka ta cigaba da kula ko zata gane.

A ‘yan kwanakin nan saida abincinta yayi irin haka wajen sau biyar, domin har dafa duka tayi wadda ta dinga yi musu kanshi da kumfa kamar sabulu.

Gaba daya ta shiga damuwa, amma ta kasa gane inda matsalar take. Gashi Abban Sadik ya fara hakura da abincinta sai yaje waken Zahra yaci. Don haka ta mayar da hankali take ta rokon Allah ya yaye mata kuma ya nuna mata abinda yake faruwa kada taje ta cutar da su ita da Abban Sadik din.
……

Ranar Alhamis ce, kamar yanda suka saba a kwanakin nan Yusra ce da Nana a zaune a falon Aisha bayan sallar la’asar. Kallon TV sukeyi ta tashi ta shiga kicin ta dora abincin dare; tuwon miyar kuka ta dora wanda bayan ta sa komai a wuta ta fito daga kicin din ta shige daki.
Tana shigewa Yusra ta dubi Nana tace

‘Ki zauna a nan kada ki taso bari na samo ruwa na sha.’

Tayi sauri ta fada kichin din.

Da gaggawa ta karasa kusa da cooker, ta kai hannu ta dauki murfin tukunyar miya ta ajiye a gefe. Ta zaro 'yar farar ledar da ta ke daure a jikin siket dinta ta bude, da sauri ta debi abinda yake cikin ledar ta barbada a miyar ta juya ta kulle ledar ta rike a daya hannunta. Ta dauki murfin tukunyar wanda murfin glass ne tana kokarin rufe tukunyar, bata san yanda aka yi ba murfin ya subuce ya tarwatse a kasa. Karar faduwar murfin ya sa Aisha ta karaso kichin din da gudu wadda dama tana hanyar dawowa kicin din, itama Nana da sauri ta karasa kicin din.
Yanda Yusran take kallonta tana rawar jiki ya sa ta san bata da gaskiya, ta karasa a hankali tace

‘A’a, Yusra me kikeyi kuma a nan zakije ki kona kanki?’

Tana karasawa ta kula da ledar da take hannun Yusra, ita kuma tana ganin hankalinta ya kai kan ledar tayi sauri ta fara kokarin boyewa.

Da sauri Aishan ta cafke hannunta ta dauki ledar tana budewa da mamaki tana fadin

‘Yusra! Me kuma kike saka min a miyar?’

Tayi tsuru-tsuru tana kallonta tas tana wani murguda mata baki tace

‘ba komai.’

Ta fara kokarin juyawa ta fita daga kicin din Aishan ta daka mata tsawa, take ta tsaya.

Ta kwance ledar ta duba sosai tana yi tana shanshanawa; idan dai ba kuskure tayi ba to sabulu ne sai dai an gurza shi kamar da abun gurza kubewa. Ta gyada kai; tabbas sabulu ake saka mata a abinci ‘yan kwanakin nan da abincinta yake baci. Ta dubi Yusra tace

‘Sabulu Yusra? Kike zuba min a miya saboda mugunta ko me?’

Ta sunkuyar da kai tana gunguni.

Aisha tayi murmushi tace

‘Hhhh! Ba ni kike cuta ba Yusra, ubanki kike cuta saboda dai sabulu ba abinci ba kuma tabbas zai iya illata lafiyar mutum musamman mutum mai shekaru kamar Abbanki. Ni ubana ya mutu na san menene maraici, ba abune mai dadi ba amma ke naki uban kike so ki dinga bawa sabulu saboda ki illata shi. Na san Mommy ce ta turoki, don haka idan kin je ki gaya mata nace tsohonki kike zubawa sabulun yana ci, idan kuwa ya mutu ku ya macewa ku da ita domin kune kaf danginku babu wanda ya kaishi kudi balle ku sa rai wani zai kula daku kamar yanda yake yi. Garin zalunci zaku cutar da kanku a banza.’

Ta kama hannunta ta saka mata ledar ta danke mata tace

‘Gashi nan idan kin je kice mata nace abinda tayi min Allah yayi mata kuma kema haka.’

Ta murguda baki ta ja tsaki sannan ta fizge hannunta ta fice daga gidan tana huci, Nana tana biye da ita.

UWAR SADDIKU

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

15

A fusace suka shiga gidan, Anti Rahma ce a zaune a falo da Baby a hannunta. Ta bisu da kallo bayan da suka nufi hawa sama tace

‘Ke Yusra meye zaku shigo gida babu sallama ko baki ga mutum a falon bane?’

Ta share kwalla tana zumbura baki, ba tare da ta juyo ba tace

‘Mommy nake nema.’

Suka karasa hayewa saman ba tare da sun ce mata komai ba.

Tana zaune a falon Abban tana kallon TV tana shan romon kaza, suna shiga suka zube a gabanta Yusra ta kifa kai a cinyarta ta fashe da kuka. Ta dafa kanta da mamaki ta dubi Nana tace

‘Meye haka kuma? Nana me aka yi mata?’

Ta zumbura baki sannan tace

‘Mommy Anti ce fa, ta zageta ta zagi Abba harda ke ma ta zaga kuma tace Yaya Yusran ta gaya miki.’

Da mamaki ta tambaya

‘Anti Rahma?’

‘Matar Abba mana.’

‘Aisha? Lallai matar nan rainin nata ya isa! Me tace miki?’

Yusra ta dago kanta, kafin tayi magana Nana tace

‘Tace zamu kashe ubanmu kuma kowa a danginmu ba masu kudi bane sai shi, harda cewa ita babanta ya mutu.’

Yusra ta bude tafin hannunta ta turawa Mommy ledar garin sabulun wadda dama ita ta bata ita, nan da nan ta dauke ta zura a bayanta. Yusra tace

‘Mommy garin na rufe tukunyar ne to dama non stick ce mai murfin glass shine murfin ya fadi ya fashe tazo tana ta maganganu.’

Ta mayar wa da Mommy duk maganganun da Aishan ta fada.

Suna cikin wannan maganar Anti Rahma ta hawo sama ta zauna a kan kujera tace

‘Me aka yiwa Yayan ne?’

Cikin fushi Mommy tace

‘Ita da matar ubanta ne, kawai saboda ta fasa murfin tukunya shine za a zageta a gaya mata maganganun banza har ana cewa ta zo ta gaya min saboda raini.’

Rahma ta taya su jimami da mamakin yanda murfin tukunyar zai sa ayi haka, tace

‘To ai murfin tukunyar bai fi karfin uban Yusra ba da za a zageta a kai kwanukan nan da kai da kanka ma kake fasawa shine harda zagi. Kai wasu matan dai sun kwashe kayansu daga gaban ma’aiki.’

Sukayi shiru na dan lokacin, jim kadan Mommy ta zabura ta mike ta tsallake su ta wuce daki, jimawa kadan ta fito da mayafi ta dubi su Yusra tace

‘Ku tashi muje, sai na ji uban da ya tsaya mata.’

Sadik ne ya shigo yana rike da hannun Ummi yana karasa shigowa yace

‘Mommy kowa yana cikin gida wannan yarinyar tana baya tana ta faman wasan kasa, kalli jikinta fa.’

Rahma ta sha gaban Mommy tana mika mata Sumayya tana fadin

‘Haba Yaya, ai bata isa kije ba saboda wannan maganar. Riketa muje sai na ji uzirinta, ai idan kika je raini sai ya shiga tsakani.’

Ta karbi Sumayya ranta a bace; bata so Rahma ta hanata ba don da sai ta tafi da yaran ta sa Sadik ya mammari Aishan.

Tunda Abbansu ya daina shan zobonta a kan kullum sai yace cikinsa yana bashi matsala ta shiga damuwa saboda ta san yana samun biyan bukatarsa a can. Don haka ta fito da wannan dabarar domin ta san idan ranshi ya baci wajen abincin dare to daren ba zai yi dadi ba. Da farko gishiri tayi tunanin a dinga karawa sai kuma taga ai idan gishiri ne da an ci za a gane ta fi son abinda idan ya ci zai zargi ko wani abun ne na asiri aka zuba masa; don haka ta sami sabulu.

Ta dubi Rahma tace

‘Da kin bari naje in ga idon mara kunya.’

‘Ai bata isa ba wallahi, wutsiyar rakumi ai tayi nesa da kasa.’

Mayafin Mommy din ta karba ta yafa ta dubi Yusra tace

‘Muje Yaya.’

Mommy ta dubi Sadik wanda Nana ta gama yiwa bayanin abinda ya faru tace

‘Ka bisu kaima saboda naga matar nan saitin ta yana gocewa.’

Rahma tace

‘Yayi zamansa ma na isheta.’

‘Gara dai ya biku, kuje Sadik.’

Haka Rahma ta wuce Yusra, Nana da Sadik suka bita a baya suka nufi gidan Aishan.
……..

Su Yusra suna fita Aisha ta zubar da miyar, ta gyara wajen. Har zata dora sabuwar miya sai kuma taji hankalinta bai kwanta da tuwon ba ma don haka sai ta sauke ta sheka masa ruwa tunda daman rude kawai tayi.

Ta fito daga kicin din ta zauna a falo da niyyar idan tayi sallar magriba ta dafa musu jollof kawai.

TV a kunne take amma bata gane me ake fada a TV din tunani kawai take tana mamakin me ta tsarewa Zahra.

Tana nan zaune aka buga kofa don haka ta tashi ta bude, batayi mamaki ba da ta gansu don ta san sai wani abun ya biyo baya.

Babu yabo babu fallasa Rahma tayi mata sallama don haka ta wuce ciki bayan ta cewa Rahman Bismillah. Suka karasa falo suka zauna, ita Yusra sai faman muzurai takeyi tana murgude baki shi kuwa Sadik ko zaman ma bai samu yayi ba, tsayawa yayi a kansu yana muzurai kamar wani soja. Ta bi su da kallo, har zata cewa Sadik din ya zauna sai kuma ta fasa don ba ita ta hanashi zaman ba. Bata son kallon da yake mata; tunda take a rayuwarta bata taba kallon idon mutum taga zallar kiyayya ba kamar yanda take gani a idon Sadiku.
Chapter 24 · 0% Book details