← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 100

Sashe 11

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya riga ya gayawa ‘yan uwansa ba za ayi taro ba don haka mata basu zo gidan ba sai wadanda suke zuwa gidan Hajiyarsu Allah ya sanya alkhairi. Kannen Hajiya mutum biyu da kuma kanwar mahaifinsa tare da matar Yayansa Bello sune zasu je daukan amarya kuma ya riga ya sanar dasu idan sun daukota kai tsaye su wuce da ita gidanta, idan ya zo da kansa zai kaita wajen Zahran.

Sai da ya gama duk wani shiri nasa na tarbar bakinsa 'yan daurin aure sannan ya kama hanyar gida, lokacin dare yayi don har yara sunyi bacci.

Haka Zahra ta tare shi babu yabo babu fallasa don kawo yanzu ta kasa danne kishinta wanda bakin ciki ne yake kara mata shi; musamman idan taga yanda yake ta rawar kai a kan auren. Bayan ta ajiye masa abincin dare ta dubeshi tace

‘Bari naje na kwanta don gobe mu da hidima saboda baki duk da dai ba taro za ayi ba.’

Tambayar ta bashi mamaki ya amsa yana kallonta

‘Hidimar me kuma? Ai ba wani taro don su Hajiya ma na gaya musu ba sai mata sun zo ba daga baya sa zo.’

Ta dan faki idonsa ta gatsina baki wanda tayi saurin biyewa da murmushin yake

‘Eh ai nima ka gaya min, amma ai naga idan aka dauko amarya wajen uwargida ake fara kaita ayi nasiha kafin a kaita dakin miji, shi yasa zamu gyara gidan kuma na tanaji abun tukuici.’

‘Oh, wanna ai nace ba sai sun kawota ba daga baya na kawota kawai.’

Ta kalleshi yayinda ya cika baki da lomar abinci yana kallon wayar hannunsa.

Tanada nata tanadin da tayiwa wannan zuwan na amarya amma zai rusa mata aiki, gaskiya ba zata yarda ba. Idan shi ya kawota ba lallai tayi abunta a sirri ba sannan kuma ba lallai ya kawota a daren ba; ita kuwa a wannan juma’ar take so ayi ta ta kare. Ta danyi gyaran murya tare da bata rai

‘Uhm! Ashe fa naku tsarin da ban ne. Naga dai abun karramawa ce da girmama uwargida tunda iyayenta ne da iyayenka zasu kawota, idan basu kawota sun nuna mata mu zauna lafiya ba ai dole tazo ta kalleni banza banza…'

Ya ajiye cokalin hannunsa ya hadiye abincin bakinsa da sauri ya tari numfashinta

‘A’a ai ba zata yi haka ba, nima ba zan barta ba ai kuma fa…'

Ta tabe baki itama ta katseshi a daidai lokacin da kwalla take fadowa daga idonta

‘Um um ai ba sai kace komai ba wanne bari kuma? Tun yanzu ka fara raba kan gidanka! Ka ce ba zata shigo cikinmu ba ni da ‘yayanka, yanzu kuma kace ba za ma a kawota a nuna mata girmana ba, ai shikenan ku yi zamanki ku biyu nima na koma cikin ‘yan kallo.’

Ta juya da hanzari ta nufi hawa sama, ya mike tsaye yana kallonta da mamaki da damuwa

‘Haba Zarah…'

Kafin ya karasa ta haye sama tana share hawaye, ya koma ya zauna a kan kujerar kamar wanda aka tunkuda, ya bi hanyar da ta bi da kallo yana mamaki.

Tabbas Aisha ce ta nuna ta fi son gidanta ita kadai kuma da ya gayawa Zahra bata nuna damuwa ba, amma yanzu shi da kansa yace ba sai an kawota ba saboda gudun ayi wani abu da zai tada rigima. Ya ma riga ya gayawa Aishan da Yaya Zuwaira cewa idan an daukota a kaita gidanta kai tasye.
Ya dafe kai yana mamakin Zahra, wai shi da kansa ya tarwatsa gidansa kuma anki a girmamata. Ya ma za ayi tace haka bayan duk wannan kaffa-kaffan da yake yi dominta ne?
Ya ture kwanon abincin ya mike ya bi bayanta.

Kamar yanda ya zata a dakinta ya sameta, tana zaune a gefen gado tana tunani tare da fitar da hawaye; ta riga ta karbo layar da Malam ya bata ta sa a wajen da amarya zata tsallaka kuma a ranar Malam yace tayi don da gari ya waye amarya ta bar mata gidanta, idan ba a kawo mata amaryar ba ya za ayi ta samu wannan damar?
Da yake bata hade kofar dakin ba har ya shiga bata sani ba saboda nisan da tunaninta yayi, sai da yayi gyaran murya sannan ta dawo hayyacinta.

Ta yi sauri ta share hawayenta ta mike tsaye tana kokarin shigewa bandakinta, yayi sauri ya kara taku biyu ya riketa.

Ta juyo ta gefe tana kallonsa tana kokarin saita fuskarta.

‘Mm! Bandaki zan shiga.’

Bai bata amsa ba ya riketa ya zaunar da ita a gefen gadon ya zauna a kusa da ita sannan yace

‘Kiyi hakuri ki fahimceni, da kai a nace kada a kawota saboda kin san halin mata ban sa da su wa za a taho ba daga can gidan nasu. Amma idan dai wannan ne ya bata miki rai to ki daina damuwa za a kawo miki ita nan, tunda dama su Goggo Habiba ne zasu daukota. Shikenan?’.

Ta kawar da kai tare da gyara zama

‘Ni bani da wata damuwa kuje kuyi yanda kuka tsara kawai.’

Ya tsattsareta da ido, har sai da ta sunkuyar da kai sannan yace

‘Ku cigaba da shirin tarbar amarya, za a kawo miki ita idan kuka gama sai su kaita nata gidan. Shine tsarina.’

Ta amsa murya kasa-kasa

‘Uhhm!’

‘In akwai wani abu da kike bukata sai kiyi min magana.’

Tayi shiru na dan lokaci, har zai tashi tayi gyaran murya tace

‘Dama akwai kudi da zan bawa amaryar kyauta kuma sababbi ake bayarwa, to na bada naira dubu goma a samo min sabbinsu har yanzu ba a kawo ba, ban sani ba ko zan samu a wajenka.’

‘To babu damuwa, idan kika shigo sai na baki akwai wasu da na canza.’

‘To na gode, Allah ya sanya alkhairi.’

Ya mike ya fice ya ja mata kofa. Ta bi kofar da harara da murguda baki kamar yana wajen tace

‘Asabar i yanzu ka dawo hayyacinka.’

Ta mike ta shige bandaki don ta wanko fuska.
____
Tun da aka ce an tafi kafi Aisha ta sake shiga damuwa, kana kallonta zaka ga ta wani firgice. Hajiya tana kula da ita sosai don haka ta cewa Zahida kada ta bari su rabu, ta dinga bata hakuri tana tauson zuciyarta. Ko da su Yaya Zainab suka dawo daga kafin ma kin zama tayi a inda suke, da yake sun ganeta sai kawai kowa ya fita harkarta.

Duk a gidan suka kwana ana ta hira da kuma shirin biki. Gari yana wayewa Aisha ta kara firgicewa, hawayen da take makalewa ma yau kyaleshu tayi. Tana hawaye tana yake duk a lokaci guda saboda yanda zuciyarta ta jagule.

A falo suke zaune kusan duk dangi ne a kewaye da ita anata raha da kokarin kwantar mata da hankali.

Ta sha kwalliya cikin wani shudin leshi mai ado da fulawowi ruwan gwal ta yafa karamin mayafin nan da ake kira Chantilly a kanta. Hannuwanta da kafufunta sun dauki kunshi ga fatarta sai sheki takeyi. Kunshin yayi matukar kyau a kan fatar tata duk da ita din ba fara bace, fuskarta babu yabo babu fallasa domin ta ki bari ayi mata kwalliya; sai dai hakan bai hanata yin kyau ba.

Tana zaune a tsakiyar danginta amma kamar ace kyat! ta ruga da gudu.

Farha ce ta shigo da gudu itama ta sha kwalliya, da murnarta ta tsallake mutane ta fada jikin Aishan tana fadin

‘Mama Baba Abba ya zo, da Anti Bushra da Anti Rakiya harda ma Sultan da Hajiya karama. Bari ma naje na shigo da su na manta.’

Kafin a bata amsa ta mike ta sake fita da gudu cikin murna da farin ciki tana ta tsalle-tsalle.

Take jikin Aisha ya kara sanyi, ta dubi Zahida wadda take gefenta suka hada ido Zahidan tana kokarin kara mata kwarin gwiwa da idonta; nan da nan hawaye ya kwace mata ta mike da gudu tayi dakinta. Kafin ayi magana Zahida ta mike ta bi bayanta Anti Uwani tana fadin

‘Ke ki dinga tashi a hankali saboda cikin jikinki.’

Ko saurarenta bata yi ba ta rufa mata baya suka turo kofar. Ta kusa kaiwa bandaki Zahida tace

‘Ya Aisha.’

Ta juyo ta tsaya, yayinda Zahidan ta kara matsowa. Ta fada jikin Zahida suka rungume juna; duka su biyun kowacce tana fitar da hawaye, sai da suka dauki lokaci a haka sannan Zahida tayi kokari ta banbare Zainab daga jikinta saboda yanda take ji yaron dake cikinta ya fara takura yana zullo. Suka rike hannun juna suna kallon juna suna hawaye, Zahida ta jasu suka karasa suka zauna a bakin gado. Aisha ta matse hannun Zahida ta bude baki cikin rawar murya tace
‘Hida zan iya kuwa? Hida Mustafa ya tafi da rabin zauciyata, ya za ayi na iya sallamawa wani mutumin ruhi na?’

Ta kifa kai a cinyar Zahida ta cigaba da kuka Zahida tana shafa kanta tana share nata hawayen. Da kyar ta lalubo bakinta tace

‘Ki yi hakuri Yaya Aisha, ki cigaba da yi masa addu’a. You will be fine in sha Allah kuma wannan auren da zakuyi shine zai tabbatar da cewa kin karbi hukuncin Allah a kanki, ki cigaba da addu’a.’

Motsin bude kofa ya sa Zahidan ta waigo yayinda Aishan ta dago kanta fuskarta duk hawaye. Bushra ce ta turo kofar a hankali ta shigo da sallama ta mayar ta rufe kofar.

Aisha ta kalleta tayi mata murmushi da fuskarta me hawaye a hankali ta kirawo sunanta

‘Anti Bushra.’

Ta karasa ta tsuguna a gaban gwiwoyin Aisha ta dafata tana dariya

‘Bari na tari hawayen amarya.’

Sukayi dariya gaba daya, su Aisha suna share hawayensu.

Zahida tace

‘Kiyi hakuri Anti Aisha kin ji, wannan shine hukuncin Allah. Allah ya sa miki albarka a rayuwarki. Hajiya tana gaisheki, kuma don karta sakaki kuka ne taki zuwa amma duk da haka sai da kikayi kukan.’

Tayi murmushi ta share sabon hawayen da ya zubo mata.

Bushra ta kalli Zahida tace

‘Anti Hida kin barta zata latse mana hancin yaro saboda kukan amarci.’

Sukayi dariya gaba daya, Aishan ta mike tana dariya ta shige bandaki tana fadin

‘Bari na wankon fuska.’
Chapter 11 · 0% Book details