← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 100

Sashe 22

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A cikin tattaunawarsu da Aisha ya sanar da ita idan yaje wajen Zahra baya samun wannan matsalar. A tunaninta asiri ne Zahran tayi amma ta kasa gaya masa, sai dai ta dage da neman maganin karya sihiri.
Musamman ta sami ruwan zamzam take yi addu’ar karya sihiri tana sha tana wanka, shi kuma duk wani ruwa da zai sha a gidan nan sai ta yi masa addua’ar a ciki amma babu wani cigaba. Yanzu ma an kai matsayin da ta daina bari ya jagwalgwala ta, shima kuma ya daina rawar kai a kanta. Sai dai kullum cikin bata hakuri yake yana yi mata alkawarin zai je asibiti a duba shi amma dai ya kasa zuwa, ita kuma bata bashi kwarin gwiwar yaje asibitin ba saboda ta riga ta yarda sihiri ne, don haka dai ta dage da addu’a.
__

Ranar Alhamis Zahra ta tashi da ciwon nakuda sai dai da yake ciwon bai zo mata gaba daya ba ta cigaba da aiyukanta tana yi tana hutawa. Ba kwananta bane amma dai ta riga ta sanar da shi tana nakuda don haka ranar gaba daya a cikin sauraron kiranta yake.

Tun wajen karfe biyar na yamma ya dawo daga aiki, wajen Zahran ya fara shiga bayan ya dubota sai ya koma wajen Aishan tunda yana nan da ta ji wani ciwo sai tayi masa waya.

Sai bayan sallar magriba sannan ta kirawosa, a gurguje ya shirya yayi sallama da Aisha bayan ya sanar da ita idan akwai abinda yaran suke bukata zai ce su karba a wajenta.

Tun wajen karfe bakwai suka shiga asibitin aka shigar da ita labour room, sai wajen karfe taran dare sannan ta haihu.

Dakin da ta haihu ita kadai ce a ciki sai ma’aikatan lafiya da likita, likitan yana tsaye a daidai kanta yayinda matron da kuma nurses uku suke daidai kafafunta suna dubawa suna taimaka mata. Tara da minti biyar tayi yunkuri ta haifi yarinyarta santaleliya, a take matron ta yanke cibiya ta dauki yarinyar ta mikowa likita. Ya karba ya dubi Zahra da take kwance yace

‘Sannu Hajiya.’

Ta amsa tana murmushi.

Ya juyo al’aurar yarinyar ya nuna mata yace

‘Kinga abinda kika haifa, me kika samu?’

Sosai mamaki ya bayyana a fuskarta tace

‘Mace?’

Likita yace

‘Yauwa, gata nan kuma lafiyayyiya Alhamdulillah.’

Nan da nan ma’aikatan lafiya suka shiga kokarin wanke mai jego da abinda ta haifa, daga baya aka fito aka sanarwa Abban.

Bayan likitan ya fito yayi masa duk wani bayani kuma ya sanar da shi zasu riketa ta kwana in ya so zuwa gobe da yamma za a sallameta.

A hanyarsa ta komawa gidan ya dauko kanwarta wadda zata tayata kwana a asibitin suka wuce gidan. Nan da nan ta zabo mata kaya ta hado mata dan abinda zata ci. Babu yanda bai yi da su Yusra su tafi gidan Aisha su kwana ba suka ki, kananunma sun riga sun fara bacci don haka tace zasu iya kwana. Haka ya hakura ya sa Sadik ya rufe musu gidan suka koma asibiti.

Ko da suka koma asibitin saida ya siyo musu duk abubuwan bukata ya kawo kudi ya bata sannan ya kamo hanyar gidan.

Wajen Aisha ya fara shiga inda dama a nan ya kamata ya kwana, yana shiga yayi mata sallama ya sanar da ita zai kawo mata Rukayya sai ya kwana da sauran yara.

Tace

‘Dare yayi wallahi, don Allah ka barta tayi baccinta sai da safe kawai. Idan kuna bukata wani abu kawai ka sanar da ni.’

Sukayi sallama ya fita ta rufe kofa.
……..

Tunda aka canza mata daki aka gyara Baby aka kwantar da ita a kusa da ita take mamaki, tayi scanning an gaya mata namiji zata haifa yanzu kuma ta haifi mace.

Ta dubi Rahma; wadda kanwace a wajenta wato ‘yar kanwar babarsu, mijinta ne ya rasu tun yaronta yana karamin kuma bata sake aure ba shi yasa duk irin wadannan abubuwan ita ake kira.

Tace

‘Rahama kin san kuwa nayi scanning an ce min namiji zan haifa, amma kinga ikon Allah mace na haifa.’

Tayi ‘yar dariya tace

‘Um, ai wallahi Anti abun fa na Allah ne dama likitocin ma lalube suke a duhu abinda Allah ya boye ai mutum ba zai iya gani ba.’

‘Hhhh! Kin san da ace ba ni kadai ce a dakin haihuwar nan ba Allah cewa zanyi canza min suka yi.’

Ta kyalkyale da dariya

‘Lallai Anti, kuma kinga gata nan kamar ‘yayanki don wannan sak yanda kika san Sadiku yana jariri.’

‘Hmmm!’

Ta yarda mace ta haifa kuma tana kaunar yarinyar amma dai tabbas ta saka ran haihuwar namiji, don haka ne ma ya saka komai kayan yara maza ta siya.
Haka dai ta yi ta wasi-wasi har bacci ya kwasheta.
……..

Da wuri Aisha ta tashi tunda ta san Zahra bata nan, ta soya doya da kwai yanda zai ishesu gaba daya sannan ta dafa ruwan zafi ta zuba a babban flask, ta dafa shinkafa da miya. Bayan ta gama wajen karfe bakwai saura ta kirawoshi a waya tace ya turo yara su dauki abinci.

Ta san watakila zasu dau lokaci kafin su karaso kuma ta san idan da shi suka taho yana da mukulli don haka tayi sauri ta shiga wanka tunda itama zata je aiki.

Ta fito daga wankan daure da karamin tawul dinta ta ji shigowarsu falon yana mata sallama. Nan da nan ta dauki jilbab dinta ta zura ta fito falon tana amsa sallamar; shi da Nana ne da Rukayya.

Bayan sun gaisheta ta amsa ta nuna musu kwanukan suka fara dauka, ya dubeta yace

‘Kin ajiye min nawa ko, a nan zan yi breakfast.’

Ta bashi amsa da

‘Eh.’

Har sun kusa zuwa bakin kofa yace

‘Rukayya tunda kowa ya shirya sai ku ci abinci kawai kowa Yaya ta zuba masa na makaranta na san yanzu Malam Sule zaizo sai ku tafi. Kafin ku dawo Mommy ta dawo mana da babinmu.’

Suka amsa sannan suka fice.

Aisha ta tambayeshi kwanan masu jego ya sanar da ita basuyi waya ba sai daga baya idan gari ya kara wayewa.

Har zata shige daki sai kuma ta dawo tana fadin

‘Bari nayi serving abincin kawai da na sako kaya sai mu ci kada yara su zo suna jirana.’

Ta juyo ta kama hanyar kichin yayinda shi kuma ya juyo da kujerar dining table daya ya zauna don ya jira ta. Har ta shiga kicin din kuma sai ta dawo ta tube jilbab din jikinta ta jefa kan kujerar zaman mutum uku, ta cigaba da kaiwa da kawowa tana kwaso abinci daga kicin tana ajiyewa.

Idonsa yana kanta har ta gama, sauri takeyi don haka bata ma kula da yanda yake kallonta ba.

Bayan ta gama ajiye abincin ta bi ta gabansa ta wuce da niyyar shigewa daki. Bata kula da lokacin da ya mike tsaye ba sai ji kawai tayi ya kama hannunta ya dawo da ita ta fada jikinsa. Duk yanda ta so ta kwace kasawa tayi, don ya riketa sosai kuma dama ya gama sanin lagonta.

Wajen wata uku kenan rabonsa da ita, yau din kuma ji yake kamar zai iya biya mata bukata. Ko ma dai menene ba zai iya hana kansa ita din ba a yanzu, ya san abinda take tsoro kuma ya ji a jikinsa babu wannan matsalar don ko daga yanda ya riketa itama ta ji alamun hakan. Da kyar ta lalubo muryarta tace

‘Zamu makara fa ni da yara.’

Ba tare da ya saketa ba ya fara kokarin lalubo wayarsa a aljihunsa, ta sami damar kara dagewa don ta kwaci kanta bayan ya dauko wayar ya rada mata magana a kunnenta ta kyalkyale da dariya. Tana jinsa ya kirawo Malam Sule yace

‘Malam Sule yau Antinsu ba zata aiki ba ku wuce ka kai yara kawai sai ka wuce office ka jira ni.’

Nan da nan ya kife wayar ya jefata kan kujerar zaman mutum uku.

Ko ba a gaya mata ba ta tabbatar yau lafiyarsa ta dawo, sai wajen takwas saura sannan ya kyaleta.

Ta dubi agogon bangon dake dakin tace

‘La ilaha illallahu, yau ka makarar dani zaka sa principal tayi ta yi min mita.’

Yana dariya ya bata amsa

‘Shikenan sai kiyi zamanki a gida gobe kya je aiki.’

Haka tayi sauri ta shiga wanka, Koda ta fito ya riga ya saka kayansa yana falo yana jiranta.

Haka suka gama breakfast tana mitar ya makarar da ita.

Da taga dai karfe tara ta kusan yi haka ta hakura tayi waya makarantar ta sanar da su ba zata sami zuwa ba.

Daga baya ya shirya ya wuce asibiti ya barta a gidan yana mata dariya.
UWAR SADDIKU

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

14

Har Abban Sadik yaje asibiti yana mamakin yanda akayi yau lafiyarsa ta dawo a wajen Aisha, duk wani lissafi yayi shi amma ya kasa samo amsar. Abu daya ya iya yankewa duk da ya kasa tuna tabbas din abinda ya faru kuma baya son ya zargi Zahra. Yana zargin kamar duk ranar da ya sha zobo ko shayi a wajenta to idan kwanan Aisha ne baya iya komai, domin a iya lissafinsa wannan zobon ne kawai bai sha ba tunda a asibiti ta kwana, shi yasa bai sami matsala ba. Ya yanke shawarar zai sa ido ya gani kuma ba zai sake yarda ya sha zobon nan ba sai dai idan ranar kwananta ne ita Zahran.

Yana isa asibitin aka sallamosu, don haka ba tare da bata lokaci ba ya dauko su ya dawo da su gida. Nan da nan aka shiga hidima da mai jego.

A ranar ya kamata ya dawo kwananta amma ta san a bisa al’ada kamata yayi ta barwa Aisha kwanan sai tayi arba’in.

Bata da matsala da hakan don tuni ta kirawo Hajja don ta karo mata maganin da ta bata don ta cigaba da dafa masa zobo; tayiwa kanta alkawarin yanda tayi jegon nan shima haka zai yi.

Tunda yamma ta sanar da shi ta barwa Aisha kwanata har sai tayi arba’in, yaji dadi sosai kuma ta kara daraja a idonsa.
Chapter 22 · 0% Book details