← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 100

Sashe 66

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

‘In Sha Allah idan naje sai nayi dawafi sannan nayi miki addu’a Yaya; yanda kuke so na Allah ya soku fiye da haka kuma Allah ya karramaku fiye da yanda kuke karramin.’

Ta fara share kwalla, Zahida ta dafa bayanta yayinda Hajiya tace

‘To ga ‘yarki nan baure sarkin kuka zata tayaki muna murna zaku saka mu kuka.’

Suka sa dariya gaba daya.

Ana idar da sallar Magriba duk suka watse suka bar Aisha da Amira wadanda sai bayan sallar isha’i zasu tafi.

A nan falon Hajiya suka ci abinci suna ta hirarsu, sai da aka idar da sallar isha’i suka tashi tafiya. Lokacin Farha tayi bacci don haka Abdallah da Anti Uwani suka rakosu farfajiyar gidan.
UWAR SADDIKU

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

34

Babu yanda Zahra ta iya, tana ji tana gani aka fasa kai yaran Dubai karatu. Ta dai samu ta karfin tsiya ta takura Abban ya amince zai saka su a Maryam Abacha University. Yayi magana da Yaya Bello shima ya amince da haka, tunda dama abinda yake gaya masa shine ya kasance yaronka yana kwana a gida har sai ka ga yanayin fahimtarsa a rayuwa tukunna. Don haka nan da nan aka fara shirin shiga MAUN.

Sai dai kawai ta yiwa kanta alkawarin sai ta kai Yaya Bello wajen boka don ta fuskanci tunda yanzu dan uwansa ya kara kusanci da shi to lallai hukuncinta zai ci gaba da cin karo da nasa. Yanda take jin yanzu ta sami Abba a hannunta bata jin zata sake bari ya subuce mata, duk wata hanya da zata bi sai ta bi don ta tabbatar babu wanda ya sha gabanta a wajen Abba. Domin a yanzu ma gani takeyi kamar Abban yana bawa Yaya Bello wasu kudade ne.
__

Tun lokacin da ta gane aikin boka yayi tasiri take kula da motsin Aisha, musamman ta sami mai aikin gidan commissioner wadda dattijuwa ce take sa mata ido tana kular mata da motsin Aishan. Tana so ta san lokacin da Aishan zata bar gidan. Zuwa yanzu kusan watanni goma an sanar da ita Aishan tana na; ta kasa gane wanne irin naci ne wannan. Miji baya kula ki amma ace ba zaki bar masa gida ba? Ta dai bata daga nan zuwa babbar Sallah ta san in Sha Allahu zuwa lokacin ko bata gaji ba to tabbas kudin hayar gidan zai kare.

Maganar boka ta tuno da ya ja layi guda biyu yace mata tafiyar Aisha da Yusuf mai tsawo ce; yanzu haka tsawon kenan kuma in Sha Allahu sai ta ga karshen wannan tafiyar.
__

Kwanci tashi har azumi ya karaso; duk wani abu da Aisha take bukata na azumi haka ta dauki Amira suka je suka siya, kuma da yake Yaya Abubakar ya san halin da take ciki ranar da aka ga watan azumi sai ga sako ya aiko mata. Buhun shinkafa, dankalin bature, doya, kifi da suga haka aka kawo mata.

Ranar goma sha takwas ga watan azumi jirgin su Hajiya zai tashi tare da Aisha. Ranar sha biyar ga wata ta shirya suka tafi gidan Hajiya ita da Amira; bayan ta kwashe duk wani abu mai amfani nata saboda bata barwa kowa ajiyar gidan ba. Sai da ta kulle ko ina tayi addu’a sannan suka fito, har zata saka kwado a gate din ta tuna duk wanda ya zo yaga kwado daga waje ya san babu kowa a gidan don haka sai ta fasa saka kwadon kawai ta kulle da mukullin. Babu wanda take harka da su a kan layin don haka bata bukatar yiwa kowa sallama, ta ja motarta suka bar unguwar.

Ranar da aka dauki azumi na sha takwas da safe Aisha da kanta ta dauki Abdallah da Farha ta kaisu gidan Umma, kakarsu ta wajen Uba. Ba karamin dadi Umma taji ba don dama sun dade basu je mata kwana ba. Sukayi sallama a kan sai bayan Sallah idan ta dawo zata zo ta daukesu. Da yamma jirginsu ya tashi sai kasa mai tsarki, tana tsakiyar Hajiyanta da Anti Uwani.
____

Ranar da aka kai azumi na ashirin da biyar Baba Salamatu wato mai aikin gidan commissioner ta shigo gidan Zahra. Lokacin yara duk sun tafi masallaci sallar asham sai Jummai wadda take aiyukanta a kichin yayinda Mommy din take hutawa a falon sama. Bayan sun gaisa da Jummai ta hau saman ta kirawo Mommy.

Nan da nan ta sauko saboda ta san akwai labari tunda Sala ta zo. Bayan sun gaisa tace

‘Hajiya ina ga kanwarki dai ta bar gidan na fa.’

Ta ji dadi sosai a ranta, amma sai ta waske tace

‘Allah Sala, ko dai unguwa ta tafi.’

‘Kai gaskiya ba unguwa ta tafi ba Hajiya. Don Kinga fa tun azumi na kusan goma na daina ganin motsinta, almajiran ma da suke zama kofar gidan jiya sun tabbatar min bata nan don farkon azumi kullum da magriba sai ta basu sadaka amma yanzu an kwana biyu basu ga motsi a gidan ba.’

Ta dan yatsina fuska

‘Allah sarki, to na gode Salamatu. Dan jirani ina zuwa.’

Ta karasa tana mikewa tsaye, ta haye sama ta barta a nan.
Jimawa kadan ta sauko ta zauna a inda ta tashi, ta mikawa Salamatu naira dubu tana fadin

‘Ga abun sadaka kya sayi ko dan sabulu.’

Nan da nan ta washe baki da addu’a tana ta faman godiya, tayi mata sallama ta fice.
……….

Cikin walwala suka tashi ranar idi, nan da nan aka shirya yara kowa ya sha kwallaiya. Karfe takwas saura Abba ya fito ya zuba su a mota suka wuce masallacin idi.

Kafin su dawo an sauke tuwon Sallah.

Sai da kowa yaci ya koshi sannan Mommy ta ware na makota, Jummai ta dauka suka tafi tare da Nana da Ummi. Gidaje uku suka kai, gidan commissioner ne na karshe kuma shine cikon na hudun. Bayan sun gaisa da matarsa wato Dr. Maimuna wadda ake kira Mama suka bayar da tuwon, aka juye aka basu kwanukan da kuma tukwici.

Salamatu ta dauko kwanukan ta biyosu suna ‘yar hira da Jummai kamar zata yi mata rakiya. Kasa-kasa suke yin maganar don haka Ummi da Nana da suka wuce gaba basa jinsu. Salamatu tace

‘Wai ni Jummalo amaryar gidanku auren ya mutu ne?’

Jummai tace

‘Babu mamaki fa, don na manta rabon da maigidan ma yayi rabon kwana da ita; ko ba ayi shekara ba an kusa. Ina ga sakinta yayi ko kuma dai wata matsala aka samu.’

‘Gaakiya da alama, tunda kin ga ta bar gidan fa tun farkon azumi. Yanzu haka dai auren ya kare. To ko Uwar dakinki ce ta kar auren ne?’

Ta dan zaro ido

‘Ke salamatu! To ni ban sani ba in kin shiga gidan kya tambayeta.’

Ta tabe baki

‘Au na manta ke fa ba a sukan uwar Saddiku a gabanki ko. To ku gaida gida.’

Tayi musu sallama suka wuce.

Tun daga wannan lokacin gulma ta fara yawo a unguwar cewa Abba ya saki Aisha.

Bayan da su Nana suka dawo ne kuma Malam Ali ya kwashesu da tuwon gidan Hajiya suka tafi kai mata. Mommy ta riga ta gayawa Yusra cewa idan Hajiya ta tambaya Ina abincin gidan Aisha tace tare suka yi don haka suna ajiye tuwon ma kafin a tambaya Yusra ta cewa Hajiyan

‘Tare sukayi tuwon da Mommy da Anti Aishan.’

Ta yashe baki

‘Ai gara hakan ya fi.’

Bata jin dadi sosai saboda ciwon diabetes wanda tun goman karshe ya tasar mata saboda an hanata azumi tace sai tayi, don haka ta san ba cin tuwon zata yi ba. Nan ta bawa Yusra umarni ta kaiwa Anisa ta ajiye a kicin. Ta gyara kwanciyarta ta kara muryar rediyonta yayinda su kuma yaran suka fito tsakar gida suka cigaba da hidimominsu.
_

Bayan Sallah da sati daya su Aisha suka dawo Nigeria; tayi sallah kuma tayi addu’a a kan Allah ya karya wannan kulli da aka yi tsakaninta da mijinta, sannan kuma ta roki Allah ya saka mata ko ma waye yake mata wannan zaluncin kuma Allah ya toni asirin me yi mata hakan.

Tabbas ta sami natsuwa kuma ta dawo da wani sabon karsashi na zaman jiran lokacin da wannan asirin zai karye, in Sha Allahu ko zata rabu da Yusuf to ba yanzu ba sai dai idan ya dawo hayyacinsa yace ta tafi to tabbas a lokacin zata tafi.

Kwanansu biyar da dawowa Aisha tana hutawa a gidan Hajiya; an dauko su Abdallah duka ta basu tsarabarsu har sun je gidan ‘yanuwanta yawon zumunci.

Suna zaune a rumfar da take farfajiyar gidan suna hirarrakinsu, Hajiya ce a kashingide a kan tabarma yayinda Anti Uwani ke zaune a kusa da ita. Ranar laraba ce don haka Farha da Abdallah suna islamiyya. Aisha ta fito daga cikin gidan bayan tayi musu sannu da hutawa ta zauna a kusa da Anti Uwani. Bata dade da zama ba ta dubi Hajiya tace

‘Hajiya gobe ni da su Abdallah zamu je gidan Yaya Zainab, daga nan zan dauko ‘yata ranar Juma’a sai mu koma gida.’

Sai da Hajiyan ta tashi zaune sannan ta bata amsa

‘To Allah ya kaimu goben. Baku yi magana da Yayanki bane?’

‘Tun last week dai da yazo, ranar da muka je gidansa har muka taho bai dawo ba kuma da ya zo nan shekaranjiya bana nan, amma idan bai zo ba zan kirawoshi kafin mu tafi.’

Tayi gyaran murya tace

‘Uhm! To ai munyi magana ba zaki koma gidan Yusufa ba tunda ko kin koma dake da wadda bata da miji duk daya kuke. Ki zauna a nan, ba zamu kashe miki aure ba, duk lokacin da ya dawo hayyacinsa sai ya zo ya daukeki ku koma.’
Tuni idonta ya cicciko da kwalla tace

‘Hajiya don….’

‘Ba shawara na zauna yi dake ba, idan ke baki san ciwon kanki ba mu muna kishinki. Na gama magana babu inda zaki koma har sai Yusufa ya zo nan da kanshi sai ku tafi.’

Da kyar ta bude bakinta tace

‘To.’

Ta tashi jikihta babu kwari ta koma cikin gidan, kai tsaye dakin Anti Uwani ta wuce ta fada kan gado ta sa kuka.

Tana shigewa Anti Uwani ta dubi Hajiya tace
Chapter 66 · 0% Book details