← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 100

Sashe 25

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rahma ta katse mata tunanin tana gaisheta, babu izgilanci ko alamar fushi a maganar Rahman don haka itama ta dan saki jiki suka gaisa ba yabo ba fallasa.

Rahman tace

‘Yar taki ce tace ta fasa murfin tukunya kuma sai tazo da maganganu marasa dadi, shine nazo na ji wai me ya faru ne?’

Kamar ba zata yi magana ba, ta dan kauda kai tana murmushi sannan tace

‘Haba dai murfin tukunyar me? Abinda kaima a hannunka yana fashewa.’

Nan ta mayar mata da abinda ya faru da kuma sabulun da ta kama Yusran da shi, tace

‘Murfin tukunyar bai dameni ba kwata-kwata amma ace yarinya kamar Yusra ta san yanda zata bi ta cutar dani saboda ina auren babanta ai kinga dole na zata aikota aka yi.’

Mamaki ya cika Rahma, ta juya ta kalli Yusra. Yanda yarinyar tayi tsamo-tsamo ya tabbatar mata lallai ta aikata. Ta mayar da dubanta ga Aisha tace

‘Ikon Allah! To don Allah kiyi hakuri, wallahi abune na yarinta don na tabbatar babu yanda za ayi Mommy ta turota tayi wannan aika-aika. Kuma na tabbatar da taje bata gaya wa Mommy din abinda tayi ba, ta dai ce ta fasa miki murfin tukunya kinata fada. Zan yiwa Mommy din bayani in naje, yara ne sai hakuri in Sha Allah na san haka bazata sake faruwa ba.’

‘Hmmm! Babu komai ai ya wuce.’

Rahma ta mike tana fadin

‘Bari mu koma.’

Sukayi mata sallama suka fice.

Gaba daya yaran haushin Rahma suke ji saboda su zuwa sukayi ayiwa Aisha rashin mutunci amma ta zauna tana bada hakuri.
Koda suka koma wajen Mommy din haka Rahma ta zauna tayi mata bayanin abinda Yusran ta aikata; sai dai daga yanda Mommy din take bata amsa ta san bata gamsu ba. Domin daga karshe ma cewa Rahman tayi sharri ne Aishan takewa Yusra, itama bata san sharrin Aishan bane shi yasa ta kama zancen.

Haka ta taso jiki babu kwari ta sauko daga falon saman tana jiyo hayaniyarsu. Tabbas daga wannan dan bayani da suka mayar ta gamsu ko da ba Mommy ce ta sa Yusra wannan aika-aika ba to da saninta aka aikata; haka ta zauna tana mamakin yaushe Zahra ta zama haka, ta watsar da tarbiyyar yaranta saboda kishi.
………

Ko da ma su Rahma basu zo ba dama Aisha bata yi niyyar gayawa Abban Sadik abinda ya faru ba, ba ayi abun a gabansa ba kuma zuwa yanzu ta fahimci Zahra mace ce da ta iya juya zance don haka ta barwa ranta abun. Amma idan suka gaya masa wani abu to tabbas da shi da su bazasu ji dadinta ba.

Sai dai itama Mommy din ta gane idan ta kai masa wannan maganar abun zai zama kamar ta kai karar kanta ne, don haka itama sai tayi shiru. Suma yaran ta gargadesu kada su gayawa Abbansu kuma kada su gayawa Rukayya wadda lokacin da akayi abun tana daki tana hadda.
……….

Wajen fiye da sati biyu kenan rabon da ya sha zobo a wajen Mommy, musamman da daddare. Don haka yanzu normal yake harkarsa, duk yanda yake so yana samu a wajen Aisha tunda ita Zahra tana jego. Baya son ya zargeta da zuba masa abun da zai taba lafiyarsa amma dai yana so ya tabbatar ko don ya gane abunda ya haifar masa da wannan matsalar.

Tun kafin ya karaso unguwar ya yiwo mata waya yace ta ajiye masa shayi in ya zo zai sha kafin ya wuce tunda kwanan Aisha ne.

Da murna ta tashi da kanta ta shiga kicin don dama tunda ta haihu ko zobon zata hada masa bata bari Rahma tayi kuma ko ya sha ko bai sha ba da kanta take zubar da sauran ba tare da mutan gidan sun sani ba.

Nan da nan ta dafa shayin ta juye a flask ta hada da kofuna biyu ta kai dakinta tunda yanzu mafi yawancin lokuta idan ya dawo tana dakinta.

A dakin kuwa ya sameta, tun kafin ma yace ina shayin ta zuba masa. Ya zauna a kan dadduma ya jingina da gadonta yayinda ita kuma take kan gadon. Yana shan shayin suna hira; a zuciyarsa yana fatan abinda yake zargi kada ya tabbata. Yana ji a jikinsa cewa Zahra ba zata iya cutar dashi ba ko da kuwa don kishi ne.

Sai wajen tara da rabi sannan yayi mata sallama ya tafi; yana ta mamakin yanda yau din take ta walwala fiye da ‘yan kwanakin baya, tana ta faman kakalo hira har ya shanye shayin.

A wannan daren duk yanda yake bukatar Aisha kasa yin komai yayi, sai jagwalgwala ta kawai da yayi. Sosai ta firgita saboda da ta fara murna cewa matsalarsu ta kare, don haka saida ya dauki lokaci yana kwantar mata da hankali yana bata tabbacin ya riga ya sami magani don haka daga wannan daren ba za a sake samun irin wannan matsalar ba.

Haka suka kwana tana fatan Allah ya sa da gaske yake ya sami maganin yayinda shi kuma yake matsanancin mamaki na yanda za ayi ace Zahra tana zuba masa wani abu a shayin don ya kasa kusantar Aisha.

Wayewar garin ranar ya kama kwananta ne ita Zahran, har dare yayi ya shiga wajen nata. Yayi niyyar ya tunkareta da maganar abinda take zuba masa a zobo amma kuma har suka kwanta bacci yana wasi-wasi.

Duk saukin kanta da halayenta masu kyau da yake so amma fa bata taba karbar laifinta; haka zata saka shi a gaba suyi ta musu a kan lallai sai ya fahimci ba itace mai laifi ba sai dai idan wani ne mai laifin. Don irin wannan ma ya san ba zata taba yarda tace ta saka masa abu a zobo ba, idan taga dama ma haka zata sa kuka ta juya zancen a kan cewa shine zai zargeta tayi ta rigima har sai ya bata hakuri.

Haka har gari ya waye sai dai kawai kallonta da yake yana mamaki; sau biyu tana tambayarta me yasa yake kallonta shi kuma sai yace mata babu komai.

Haka ya kare wannan kwana biyun ba tare da yace mata komai ba.
Kuma duk cikin kwana biyun nan batayi zobo ko lemon tsamiya ba, shayi ma kuma da bai nema ba bata bashi ba. Sai na safe kawai wanda yace a daina saka komai a ciki a dinga bashi ruwa kawai zai hada shayinsa da kansa.

Ranar da zai koma kwanan Aisha ranar ne tayi zobo, lafiyayye sai kamshi ne yake tashi ga sanyi har gumi jug din yakeyi. Duk yanda yake son zobon nan haka ya hakura, har ta cika masa kofi ya dubeta yace

‘Kai ba zan sha zobon nan ba, bana jin dadin cikina sai dai ko wani lokacin.’

Suka cigaba da hirarsu a dining table, shi yana cin abinci ita kuma tana taya shi hira da yake lokacin wajen karfe biyar ne don haka ita ta riga taci abincinta na rana. Ya dubeta ya tura mata kofin zobon yace

‘To ai sai ki shanye wannan da kika zuba.’

Tayi ‘yar dariya tace

‘Ni kam na sha nawa, wannan ai naka ne. Sai dai idan baka sha ba na ajiye da daddare na sha.’

Ya cigaba da cin abincinsa; dama bai yi zaton zata sha ba tunda ta san ta saka wani abun a ciki don tabbas ya san da babu wani abun a ciki da tuni ta shanye zobon nan.

Ya kusa gama cin abincin Sadik ya shigo daga makaranta, ya riga ya shiga SS 2 don haka idan aka tashi daga makarantar yana tsayawa lesson sai biyar suke tashi. Bayan yayi musu sannu da gida ya dubi jug din zobon nan yana gumi yace

‘Abba in dauko kofi in sha zobonka, wallahi zafi nake ji yau an yi rana.’

‘Ai ba ma sai ka dauko kofi ba dauki wannan ka sha.’

Abban ya bashi amsa yana nuna wanda Mommy ta riga ta zuba masa a kofi.

Da sauri Sadik ya karaso da niyyar daukan kofin, kafin ya karasa ta balla masa harara tana kokarin buge masa hannu

‘Naka zobon ai yana kicin da abincinka ka shige ka dauka.’

‘Mommy wai na sha wannan din kafin na cire uniform.’

‘To ki barshi mana tunda ba sha zanyi ba.’

Abba ya fada yana kokarin daukar kofin ya mika masa, tayi wuf ta rigashi daukewa tana fadin

‘Allah ba zai sha ba sarkin rashin kunya, yaje ya sha nasa.’

Sadik ya jefa jakarsa kan kujerar falon ya shige kichin yana gunguni, ta mayar da kofin ta ajiye tana ta wani kumbura.

Sai da ya gama cin abincin tsaf ya dubeta yace

‘Zahra.’

‘Na’am.’

Ta amsa da alamun jikinta ya dan yi sanyi.

Ya kalleta suka hada ido, ta kau da nata idon saboda yanda yake kallonta kamar yana kokarin karanto wani abu a zuciyarta.

Yace

‘Ko dai akwai wani abu a zobo nan ne wanda ba Sadiku aka zubawa ba ni aka zubawa.’

Ta dan dirirce sai kuma tayi kokari ta waske

‘Ban gane ba? Kamar me kenan? Bayan ga irin zobon nan Sadiku ya debo daga kicin kuma ya sha.’

‘To me yasa ba zai sha wannan ba kema kuma ba zaki sha ba?’

Ta dan bata rai sannan tace

‘Gani nayi ai ba tarbiyya bace na zubawa ubansa abinci shi kuma ya dauka ya sha, a kofin ma da na zuba maka. Amma idan kana so lallai ya sha zaka iya kiransa ka bashi, ni dai ba zan sha ba tunda na gaya maka bana bukata. Me zan zuba maka a zobon? Shekaru goma sha kana shan zobona ban taba zuba maka komai ba sai yanzu? Saboda dai ni babu abinda zanyi na burgeka. Ai shikenan!’

Ta tura kujerar ta mike ta bar masa waje ta nufi dakinta, ya bi bayanta da kallo yana mamaki.

Dama ya san haka zatayi domin hakan ne dabi’arta a duk lokacin da bata da gaskiya, ya karasa cin abincinsa ya tashi ya shige dakinsa.

Ya saba bata hakuri idan sukayi irin haka sai dai yau ya ci alwashin ba zai bata hakuri ba don shima ta bashi haushi da mamaki. Bayan sallar isha’i ya gama shirinsa ya sameta a daki yayi mata sallama ya nufi wajen Aisha.

UWAR SADDIKU

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

16
Chapter 25 · 0% Book details