← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 100

Sashe 81

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun Hajiya tana da lafiyarta ta bar wasiyyaa cewa idan ta rasu kada ayi mata zaman makoki, amma saboda ‘yan uwanta wadanda suka taho daga Sumaila da kuma Ummulkhairi da yaranta su biyar wadanda sai sunyi sati biyu sannan zasu koma Lagos haka aka hakura aka yi zaman na kwana uku. Duk wanda ya tambayi Saddiku haka Yaya Bello yake cewa yana makaranta suna jarrabawa shi yasa ba a gaya masa rasuwa ba.

Ranar da aka kwana uku da safe Yaya Bello da kansa ya shiga har cikin gidan ya sanar da mata cewa bayan azahar zai sa a kawo mota za a mayar da su Sumaila. Duk yanda Yaya Saratu ta so ya bari a kai bakwai bai ma saurareta ba. Itama Ummulkhairi da taji wannan sanarwar take ta sanar da shi tana so ita da yaranta su wuce gidan Yusuf su karasa kwanakin nasu a can. Don haka ta karfin tsiya Yaya Bello ya sallami kowa aka share makoki.
Azahar nayi shima Yaya Bello ya tattara iyalansa a gaba suka koma gida tare da Najma ‘yar wajen Ummulkhairi. Iyalan Abba suka shiga mota Malam Ali ya ja suka tafi, shi kuma Abban ya dauko Ummulkhairi da yaranta wadanda zasu karasa hutunsu a gidansa. Yaya Saratu kawai suka bari a kan ita sai da yamma zata tafi sai a bar mai aikin Hajiya da kuma Innani kanwar Hajiya tare da Anisa wadanda sai daga baya zasu tafi.

……….

Lokacin da su Zahra suka bar gidan makokin Ummulkhairi ta sanar da ita suna nan zuwa ita da yara, don haka suna shiga gidan ta sa aka fara gyara musu dakin baki na falon kasa. Sai dai suna shiga unguwar Abba ya ajiyesu a gidan Aisha yace su sauka a nan tunda kusa ne sa dinga shiga wajen Zahra da yaran.

Nan da nan Aisha ta shiga hidima da su.

Yana shiga gidan Zahra tana zaune a falon kasa yayinda Jummai take goge dakin. Bayan ya amsa sannu da zuwanta ta ce

'Ina Anti Ummun? Tace min tare zaku taho.’

'Eh tare muka taho suna gidan Aisha na san nan din ma da anjima zaki gansu.’

Bai saurari abinda zata ce ba ya haye saman; ba zai iya sauraron komai ba saboda yanda ya gaji kuma ga damuwa.

Ta kawar dakai tana mamaki; yanzu kenan ba zai ma bari ta sauki bakinsa ba! Ta tashi itama ta haye saman.

Haka aka gama jimamin rabuwa da Hajiya kowa ya koma harkokinsa, mutanen Lagos ma suka gama hutunsu suka koma gida.

—-----

Dole ta saka Zahra tana yin amfani da shawarwarin Yaya Murja tunda ko babu komai ta san sai ta kwantar da kai a wajen Abba sannan zata sami kudin zuwa wajen Malami. Tunda dama da business dinta take samun kudi kuma a halin yanzu babu zancen wani business domin duk ta cinye kudin.

Yanda take ganin walwalar Abban ta san cewa Saddiku yana lafiya tunda ya gaya mata yana zuwa duboshi kuma yana yi masa waya. Shima Abban ya sami natsuwa ne saboda yanda yake ganin cigaba a wajen Saddiku; rehabilitation center din sun bashi rahota a yanzu da Saddiku ya kai wata biyu a hannunsu an samu an raba shi da miyagun kwayoyin; yanzu aikin gyaran dabi'unsa ake yi da kuma karatun islamiyya da ake biya musu. Wannan ya sa Abban ya kara sakewa da Zahran duk da bai sanar da ita inda Saddikun yake ba.

……

Mahaifiyar Amina ta fara samun lafiya sannan kuma a halin yanzu akwai kanwar Aminan wadda take karatu a Sudan ta zo hutu, don haka tana gidan Aminan kuma tana kula da Umman nasu. Don haka suke cigaba da shirye-shiryen zuwa wajen boka; domin Amina ta samo musu sabon boka.

Yau ranar asabar ce kuma da yake ana cikin hutun makaranta kullum yara suna gida, don haka ta gaji da hayaniyarsu tana so ta dan fita. Gidan Amina take son zuwa don ta san a nan ne zata samu a saurareta kuma a bata irin shawarwarin da take so. Ba a gidanta Abban Sadik ya kwana ba don haka sai wajen karfe goma na safe ya shigo gidan. Bayan ya gama abinda zai yi da zai fita ta tambayeshi izinin fita wanda ba tare da wani bata lokaci ba ya bata dama.

Nan da nan ta shirya, ta sallami yaran sannan ta barwa Jummai abincin rana da abincin dare don batayi niyyar dawowa da wuri ba. Ta fito Malam Ali ya ajiyeta, ta sallameshi domin Aminan zata mayar da ita gida idan sun gama.

Sai da ta fara gaisawa da Umman su Aminan ta yi mata ya jiki sannan suka zauna a falo suna gaisawa da Aminan. Basu jima a falon ba suka koma dakin Aminan. Nan suka baje a kan kafet din da yake tsakar daki, Raihana kanwar Aminan ta zo ta kawowa Zahra ruwa da lemon roba suka gaisa sannan ta fice ta ja musu kofa.

Bayan sun dan taba hirarsu ta duniya Zahra tace

'Aminoni ina cikin damuwa wallahi ba zaki gane ba, yanda kika ganni nan daurewa kawai nakeyi amma komai ya tsaya min.’

Ta yi dan gajeren murmushi mai ciwo, tace

'Baki kai ni damuwa ba Uwar Saddiku! Idan banda Daddy ya raina ni ya za ayi ace ina zaune nan a Kano yana Abuja yana bin matan banza; harda wadda aka ce shi ya ajiyeta kamar matarsa yake mata komai. Kuma duk abun nan ya hana ni zuwa Abujan kuma sai yayi wata biyu bai zo ba, da ya zo kuma dama kwana biyu ne zai ce yana da aiki don haka nan da nan zai koma. Ni zai yiwa tozarci!’

Ta dan zaro ido

'Ikon Allah! Kai Jama'ah wallahi maza basu da mutunci.’
'Ki bari kawai kawata. Akwai wani malami da aka hadani da shi kuma shima an ce aikinsa yana yi sosai, gashi bashi da nisa don an ce nan cikin unguwa uku yake. Kawai dai aikinsa da tsada.’

'To ai haka zamu je don kin ga ni ma na kusa hada 300k, ina ga ko bata isa an gama aikin ba zata isa a fara. In ya so idan ana bukatar ciko sai na bada dakunnen Rukayya a sayar.’

'Nima kusan na hada kudin, kin san akwai aikin da za a yiwa Ummanmu a asibitin koyarwa na A B U. To Raihana ce zata zauna da ita, so nake sai sun tafi asibitin kafin a sallameta sai muje mu gama duk abinda zamu yi. Saura sati shida, kada ki damu kawata kafin azumin bana komai ya dawo dai-dai.’

'Ina ga ma mu dan kara don ni so nake sai ya dawo min da Saddiku tukunna, ina jin shi kuma saura sati biyu ya dawo. In ya dawo na ganshi sai na fi samu nutsuwa, kai da danka saboda zalunci a hanaka ganinsa!’

Suka cigaba da tattauna yanda zasu fitowa matsalolinsu.

Sai da akayi sallar la'asar sannan Zahra ta shirya Aminan ta mayar da ita gida.

__

Kwanci tashi Saddiku yayi wata shida a rehabilitation center, kuma yau Alhamis yau ce ranar da za a daukoshi a dawo da shi gida. Cikin walwala Abba ya shirya tunda ya riga ya dauki hutu ba zai je office ba a ranar, bai gayawa kowa cewa yau zai dawo da Saddiku ba ya fice ya nufi gidan Yaya Bello.

Sai da suka kama hanya sannan Yaya Bello ya sanar da shi cewa idan sun dauko Saddikun shi ya saukeshi a kasuwa, suka kama hanya cikin walwala.

Suna isa suka sami Saddikun a shirye da kayansa tsaf a reception yana jiransu, suna shiga aka yi musu iso wajen shugaban center din wanda shine zai basu takardar sallama.

Bayan sun gama gaisawa ya mikawa Abba takardu ya sa hannu ya tura masa; yayi gyaran murya yace

'To Alhamdulillah, Sadik Yusuf ya fita daga harkar shaye-shaye da izinin Allah. Sai dai akwai bukatar a tabbatar bai koma harka da abokansa na baya ba domin ‘yan shaye-shaye suna da zumunci. Zasu iya sake janshi cikin harkar ba tare da bata lokaci ba. Ba wai hanashi harka da abokai za ayi ba, no, kawai a canza masa environment ko makaranta yanda da kanshi zai sake zabar abokai. Alhamdulillah ma yaron yana da saukin kai domin ya koyi abubuwa da yawa kuma ya haddace wajen izu sha biyar a nan din.’

Cikin jin dadi Abba yace

'Alhamdulillahi. In sha Allah za a kiyaye.’

Sukayi sallama suka dauko Sadiku suka kamo hanyar gida; sai da suka sauke Yaya Bello a kasuwa sannan suka wuce gidan.

Babu kowa a farfajiyar gidan, duka suna cikin falon kasa suna kallon TV saboda ranar children day ce don haka babu makaranta. Ita kuma Mommy tana falon sama.

Da sallama Saddiku ya shiga falon yana dauke da karamar jakarsa wadda kayansa suke ciki, gaba daya daskarewa suka yi na dan lokaci suka kasa magana. Rukayya ce ta fara mikewa ta sa ihu

'Yaya Sadik!’

Kafin ayi wani abu ta mike ta daka tsalle ta fada jikinsa ta rungumeshi tana dariya. Gaba daya su suka taso suka fada jikinsa da gudu banda Yusra wadda ta fito daga dakinsu ta tsaya tana kallonsu tana dariya.

A nan Abban ya shigo dauke da sauran kayan Saddikun yana dariya yace

'An tareka a nan kenan?’

Suka karasa ciki gaba daya bayan Abba ya amsa sannu da zuwan da suke masa. Yusra wadda ta zauna a hannun kujera tace

'Yaya Sadik bamu san fa zaka dawo ba don ko dakinka ba a gyara ba, gashi yau Jummai bata nan.’

Kafin ta sami amsa ta kalli Rukayya tace

'Ke Rukayya sai kije ki share masa dakin in ya so idan Jummai tazo gobe sai ta kara gyarawa.’

Rukayya ta dan bata fuska saboda haka suka saba duk lokacin da ake bukatar wanda zai yi wani aiki to nan da nan Yusra zata ce Rukayyan tayi don ita kusan bata moruwa.

Nan da nan kuma ta dan yi murmushi ta mike tana fadin

‘Bari ka gani Yaya Sadik in ba haka ba Ya Yusra bata ki ka kwana a kan kurar ba.’

Da sauri ta shiga kicin ta kwaso tsintsiyoyi ta fito ta nufi kofar waje da niyyar ta gyara masa dakinsa na boys quarters. Abba ya mike yana fadin
Chapter 81 · 0% Book details