← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 100

Sashe 59

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mommy bata dukansu, ba karamin laifi mutum zai yi a gidan nan ba Mommy ta dokeshi amma ita gashi yau Mommy ta mareta kawai saboda ta je gidan Anti Aishan. Ta san Mommy din ta hanata zuwa amma ai Abba ne yace ta dinga zuwa; ko kuwa Mommy kawai ya kamata ta dinga yiwa biyayya? Ta san Yusra ce zata zauna ta tsarawa Mommy karya da gaskiya kuma ita ta zuga akayi mata wannan marin; duk da haka kuma ta san Mommy din ta fi son Yusra a kanta. Tunda da bakinta mommy din tana fada Rukayyan ‘yar Abba ce, kuma duk wata mu’amalar da take yi da su yana nuna tana son duka yaran fiye da yanda take sonta. Don ita ko doguwar hira bata fiya hadasu da Mommy ba saboda da zarar ta fadi ra’ayinta sai Mommy din su hadu da Yusra suce bata da hankali bata san ciwon kanta ba, ko kuma idan tayi wani abun Mommy tace wai bata da wayo kamar Anti Murja ko tace halin Abbanta ta gado.

Ta sa hijabinta ta goge hawayenta, bata jin dadin yanda Mommy take mata; ta kasa fahimtar abinda ya sa Mommy take ganin kamar Anti Aisha cutar dasu zatayi don ita abubuwa da yawa na ‘yan mata a wajen Anti Aishan take koya saboda tana sauraronta tayi surutu son ranta. Ba zata iya kinta ba ko don Abbanta, sai dai kawai tana son Mommy ta so ta ko Yaya ne don a yanzu zata iya cewa Mommy bata sonta; duk da abu ne da ta sani tun kafin Abba ya auro Aisha.

Ta mike tsaye ta fara wanke fuska tana fatan Allah yasa kada Yusra ta kulata don yau idan ta kulata duk wani haushi da take ji sai ta huce a kanta.

Haka ta wuni cikin damuwa har dare yayi Abban ya rakata gidan Aisha, ita kanta Aishan tana ta faman tamabayarta ko bata da lafiya saboda yanda ta ganta; sai kawai tace mata cikinta ne yake ciwo amma ta sha magani. Haka ta kwana babu walwala.
___

Tunda suka dawo daga wajen boka take tunanin yanda zatayi ta sa Abban Sadiku ya kwana da janaba. A iya zaman aurensu da shi zata iya cewa idan banda satin amarcinsu na farko bai taba kwana da janaba ba, duk yanda ya kai ga shagala sai yayi wanka yayi alwala. Ko da zai sake dawowa to sai dai idan yayi wanka kuma yana gamawa zai sake yin wanka. Gaba daya tunaninta ya kare, gashi yau Juma’a ta rasa ta ina zata kama abun.

Tana zaune a dakinta a kan dadduma ta idar da sallar Magriba dabara ta fado mata, gara ta kirawo Amina don ta san ba zata rasa dabara ba.

Tana bugawa tayi sa’a, bugu daya Aminan ta dauka, bayan sun gaisa ta sanar da ita halin da ake ciki. Tace

‘Ai da kin gaya min tuntuni, kin manta ne da Hajja. Akwai wani yaji da zata baki da kuma turare, wallahi in kikayi amfani da shi to sai dai kawai nace kema ki shirya don zai yi ta aiki ne daga ya juye zai sake laluboki. Ba zai ma sami sukunin wanka ba. Bari nayi mata waya, ko da yake kema ki kirawota na san gobe da safe zata iya kawo miki.’

Nan take tayi mata sallama suka ajiye waya ta kirawo Hajja, tayi mata bayanin duk abinda take so ita kuma tayi mata alkawarin gobe kafin azahar zata kawo mata kayan aiki.

Ta ajiye wayar tana murmushi.

Sai yanzu ne ta sami natsuwa, fatanta kawai kada a sami wata matsala musamman idan Abban yaki bata hadin kai. Amma dole ne tayi iya yinta saboda ba zata yarda Aisha ta rabata da mijinta ba, gashi yanzu kiri-kiri ta fara janye mata hankalin yara. Tana mamakin abinda ya sa Rukayya take son matar nan duk da dai ta san karshenta a wajen kwanan da take zuwa tayawa za a bata abubuwan da zasu saka a mallaketa.
Tabbas dole ta mike tsaye ta raba Rukayya da matar nan.

Tana matukar son Rukayya tun lokacin da ta haifeta kuma har kawo yanzu, duk cikin yaranta babu wanda yake kama da mahaifiyrta kamar Rukayya, domin da ta haifi Rukayyan ma sunan mahaifiyar ta taso sakawa. Sai dai lokacin da aka haifi Rukayyan Abbanta ya tafi aikin Hajii don haka Yaya Bello ne a kan komai, shi kuma bai yi shawara da kowa ba ya saka mata Rukayya. Wanda Abban yace hakan yayi, don haka suna ya bita. Shine saida aka haifi Ummi aka sa sunan mahaifiyar tata.

Duk da haka Rukayyan tana fara girma dabi’unta suka koma kamar na babanta. Ga saukin kai da hakuri, komai zata ce ba komai bane, ga rashin wayo. Sai kuma ya zama ta fi shakuwa da Abban saboda ya fi sauraronta fiye da Mommy din.

Amma yanzu duk abinda ta gani a tattare da Rukayya gani take Aisha ce take sakata don haka ta yi shirin dole sai ta rabasu ko ta wane hali.
---------

Ranar asabar tun kafin azahar Hajja ta kawo mata abin da ta bukata; wani gari ne dan kadan wanda tace mata gaba daya zata juye masa a miya sannan kuma da wani turare wanda zata shafa a jikinta dai-dai inda zai dinga shakar kamshin saboda kamshin turaren zai dinga kara kunnashi koda ya gama biyan bukatarsa. Sannan kuma ita kanta aka bata kayan da zata yi amfani da su saboda kada ta gaji.

Yana matukar son couscous da miyar alaiyahu wanda ita kuma bata son couscous din, don haka ma bata yawan yin couscous. Amma yau da yake da akwai abinda ta shirya sai ta dafa masa couscous din da miyar alaiyahu wadda ta sha kifi da nama duk don ta badda kama.

Wajen karfe takwas da rabi na dare bayan ya dawo daga sallar isha’i ya raka Rukayya gidan Aisha don ta tayata kwana kamar yanda ya saba. Kafin ya dawo ta riga ta jera abincin a kan dining table. Bayan ya zauna ta zuba masa abincin ta ajiye sannan ta wuce kitchen ta zubo indomie din da ta dafa domin ta ci, ta zauna a kujerar da take gefen tasa. Ya dubeta yana dariya

‘Yanzu fa sai kice indomie ta fi couscous din nan dadi ko?’

Tayi dariya

‘Ai ko ban fada ba ma haka ne, wallahi ni ban san me kike ci na dadi ba a cikin couscous gara nayi ta cin indomie.’

‘Allah sarki, kin bar dadi fa.’

Haka ya cinye couscous din nan yana ta faman yi mata surutu har sai da ya kara.

Bayan ya rufe gidan ya dawo ya zauna a falon sama tare da ita suna hira yayinda Sumayya da Ummi suke wasanninsu.

A al’adarsa sai wajen sha daya na dare yake kwanciya amma yau tun wajen karfe tara ya fara neman dalili, sai dai Sumayya ta ki yin bacci. Don haka ya dubi Mommy yace

‘Bari naje idan kin shirya kya sameni a dakin, naga mutuniyar taki yau hira take ji.’

Yana shigewa ta bi bayansa da dariya domin ita ta fuskanci abinda ya tasheshi da wuri don tana kula da yanda yake ta wasu muzurai da wasu mutsu-mutsu.

Sai da ta gama yangarta ta gama nata yi lokacin wajen karfe sha daya, ya gama zakuwa ta yanda shi kansa mamakin abinda ya janyo masa hakan yakeyi sanna ta shigo dakin. Tana shiga dakin kuma ta yarda zaninta a gefen gadon da yake kwance ta tsiri wata kaiwa da kawowa. Ta shiga bandakinsa tayi brush, ta fito ta kama zarya kamar mai neman wani abu a daki. Sai da ta tabbatar ya gama zakuwa sannan ta kashe fitila ta kwanta a kusa da shi. Tana kwanciya ya fada mata kamar wani mayunwacin zaki.

Tun sha biyun dare suke abu daya amma ya kasa gamsuwa, ko da ya gamsu kafin ya tashi sai kuma yaji yana bukatar kari. Tun yana jin dadi har ya fara mamaki saboda bai saba samun irin haka ba. Watakila dai zai iya tunawa ya sami shigen hakan lokacin da ya dinga kasa yin komai a kwanan Aisha, sai dai a wancan lokacin ba kasa gamsuwa yake ba sai bayan ya gamsu sai ita Zahran ta kara laluboshi. To ko dai yanzun ma wani abun Zahra ta bashi yaci a abincin dare. Haka ya cigaba da hidimar nan yana yi yana tunanin da safe tabbas sai ya binciki Zahra.
Sai can gefin asuba wani bacci mai nauyi ya dauke shi, tunda ta duba taga yayi bacci kuma ta tabbatar baccin nasa yayi nauyi sosai sai ta zare jikinta ta fice daga dakin; domin itama ta gaji duk jikinta ciwo yakeyi.

Sai da aka idar da sallar asuba a masallaci gari ya fara wayewa sannan ya farka daga bacci.

Firgigit ya tashi zaune, ya janyo wayarsa ya duba lokaci yaga shida saura kwata. Yace

‘Subhanallah.’

Ba zai iya tuna lokacin da ya makara sallar asuba ba koda kuwa bashi da lafiya, nan yayi addu’a ya sauko daga kan gadon ya fada bandaki.

Har ya idar da sallah yana mamaki, sai dai ya kasa tuna mamakin me yakeyi, ya kasa tuna abubuwan da suka faru a daren jiya. Yana nan zaune a kan daddumar har kwakwalwarsa ta fara gajiya da kokarin da yakeyi ya tuno me ya makarar da shi sallar asuba amma ya kasa. Bacci kawai yake ji don haka ya tashi lokacin ya fara jiyo hayaniyar yara suna shirin tafiya tahafiz, ya koma kan gadon ya kwanta bacci ya kwasheshi.

Sai wajen karfe goma sannan ya fito, zuwa lokacin ta riga ta jera abincin safe a tebur. Nan ya zauna ya gama cin abincin, bayan ya gama ya fice ya tafi gidan Hajiya.
--------

Tunda suka dawo daga Dubai sai yanzu ne ta huta ta dawo dai dai duk wata gajiya ta rabu da ita, don haka tun asuba da ta tashi ta sa Rukayya ta tayata suka gyara gidan tsaf, har inda ma bata gyara ba tunda ta dawo. Karfe tara saura kwata Rukayya tayi wanka ta shirya ta fice don tafiya tahfiz, tayi mata sallama a kan sai an kwana biyu tunda ta san yau Abba a nan zai kwana.
Chapter 59 · 0% Book details